_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 100*
Jama'a kowa yayi kokari yayi register mu Samu team ya cika zuwa karshen wata mu fara kwasar romon demoradiya,Kunga dai irin salary din da muke rabawa sunata yi mana Addu'a da sam barka suna fatan Alkairi akan wannan team work kowa yayi receiving alert Yana kwance cikin aminci, bugu da ka'ri kana a gefe da'ya account dinka Yana budewa ka ringa kwasar naira 100k a hakan ma Idan baka kawo kowa bane zaka Samu 100k Amma idan kayi kokari ka kawo jama'a zaka ringa samun Sama da haka duk da haka fa akwai arias na 600k bayan budewar account dinku da company ta baku Alhamdulillah 🙏💃💃💃 maraba da 52u,godiya ta tabbata ga Allah 52U Alkairi ne💸💸💸💸 🥰🥰🥰💃💃💃💃💃
Contact us via
07034464517
08160508316Bayan tafiyar yan Kawo kaya Diga sunfi karfin awa sama da uku suna zaune a cikin mota a kofar gidan Baba,basu sami ganin Baba sai da ya fito sallar la'asar tu kunnan sun ga Baba shima inda suke bai ishi Baba kallo ba ya wuce su dan tafiya yin Sallah dan ita ce ta fiddoshi daman,kallon Diga Ubaidu yayi yana cewa."Yaya wannan wani irin cin fuska ne ake mana kuma baka ce komai ba?idan da ace nine kai wallahi billahi da tsinin tsiya da bala'i zan auri yar tashi naga yanda zai yi,kuma shi zai ɗaura mana aure dan ba dauketa zanyi ba amman da kanshi zai ɗaura mana aure wallahi,amman dan yaga ana binshi sai wulaƙanta mutane yake fissabilillah Yaya,tun sha ɗaya safe muke zaune na kamar ya ajiye kayan wanki ko sallar azahur bai fito ba sai yanzun na kusa zuwa wuya fa Yaya."girgiza kai Diga yayi yana cewa."A'a Ƙanena karka kuskura kace haka,Baba mahaifinmu ne koda bai bani Jamila ba ka tuna kanwarmu Hannatu tana hannunshi duk da yana fushi damu bai maido mana ita ba,tana hannunshi ko dan haka mun ɗaga mashi ƙafa ban sake zuwa daga kai daga yau tunda kai kana da saurin zuciya,shiyasa nafi tafiya da Salisu shi bai kaika saurin fushi ba irin haka tashi muje muyi salla idan mun fito sai muyi maganar ba sai mu tafi gida ba.?"furzar da naunauyen numfashi kawai Ubaidu yayi bai ce komai ba,yana fitowa daga cikin mota ya buɗe ma Diga shima ya fito da yake suna da awallar sallar azahur shiyasa basu tsaya yin alwala ba suka wuce..koda suka shiga cikin masallaci zama sukayi gasu ga Baba suna jiran liman bayan liman ya shigo aka tashi aka fara sallah bayan an idar sukayi lazimi kusan a tare suka fito daga cikin masallacin,duƙawa har ƙasa Ubaidu yayi yana cewa."Babanmu ina wuni.?"kallon Ubaidu Baba yayi sak ya hango kamar shi da Hannatu yar kwanciyar hankali ya samu dan tunani yake anya ma ba kiddneping din Hannatu sukayi ba suka kawo mashi da sunan kanwarsu? amman ƙara ganin Ubaidu da yayi ya samu natsuwa,ansawa yayi yana wucewa tashi Ubaidu yayi suna bin bayan shi Diga na cewa."Baba dan Allah kayi hakuri ka saurareni kaji nawa uzurin idan kaji nawa uzurin na yarda ka yanke duk hukuncin da ya dace ka yanke a kaina Baba,amman karka yanke hukunci ba tare da kaji daga bakina ba."tak Baba bai ce mashi ba har sai da suka yazo kofar gida sannan ya dakata yana cewa."Umar har sau nawa zan gaya maka karka sake zoman kofar gida? maiyasa baka jin magana ne?to bari kaji daga yau karka kuma zoman gidan ba zan wani tsaya ɓata lokacina ba Umar ina sauraren wasu kalamanka ba zan tsaya ba dan ba amfanin da zasuyi man nidai Ƴata ce dai ko?ba zan baka aurenta ba na ba wanda naji zan iya ba ai shikenan dai ko?ku bar zuwan man kofar gida daga kai har yaranka har shi ƙanin naka Ubaidu kuma yarinya Hannatu ba zan baku ba dan ba tana hannuna zan dauki nauyin karatun ta ban buƙatar ko sisinku."daga haka Baba ya shige gidanshi bai jira ko ansar Diga ba,kallon Diga Ubaidu yayi yana cewa."wai mai wannan mutumin yake nufi damu ne?Yaya ba zan yarda ba fa ina kallo ana maka wulaƙanci wallahi yanzun ma ba dan nakai zuciya nesa ba da sai na sauke mashi maruka wallahi,an gaya mashi mu matsiyata ne ba zamu iya daukar nauyin karatun Hannatun ba?ko yana iko da ita da har zai mana tsakani da ita mu da kanwarmu."Dafa shi Diga yayi yana cewa."calmdawn ban hanaka irin wannan maganganun ba ga Baba ba Ubaidu.?"Maida kanshi ƙasa yayi yana cewa."Yi hakuri Yaya kawai banjin dadin irin abunda yake maka ne, Yaya kaine jigona a duniyar nan abun taƙamata da tunkaho bayan mahaifina banda kamarka dan'uwana rabin jiki,ba zan taɓa iya zuba ido yana kallon yana maka irin wannan abun ba zan iya ɗaukar mataki ne a take ba tare da nasan na dauka ba Yayanmu."Murmusawa Diga yayi yana cewa."Ina alfahari da kai ƙanena nima kaf duniya ban da kamarka dan inajinka har cikin zuciyata ina maku kallon ƙannen da muka kwanta ciki ɗaya daku kai da Hannatu shiyasa bani fatan abinda zai cutar daku kuma karka zucciya da Baba mu ƙara yi mashi uzuri mu tafi gida."gyaɗa kai kawai yayi suka wuce gida zuciyar Ubaidu ba dadi akan abinda Baba yayi ma Diga.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.