_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 72*
Karfe biyu na rana jirgin Sanda yayi landing a birnin Katsina convert akayi mashi wajen daukoshi ba inda suke kai shi sai gidanshi da ke a cikin Katsina a unguwar G.R.A,sai da sukayi 5mn da isowa sannan aka buɗe mashi yana zuro dogayen kafafunshi a hankali yake fitowa cikin motar yana kare ma compound din gidan kallo yana mai shide ajiyar zuciya a hankali yana kallon wani dansanda da take tsaye gefenshi yana cewa."Abbas zai shigo idan yazo a barshi ya shigo ba daga shi ba ban buƙatar kowa ya shigo man dan ina buƙatar hutuwa." Ƙamaiwa yayi yana cewa."You Order is concern Sir." Gaba kawai Sanda yayi yana shigewa a cikin main parlon gidan direct upstairs ya hau dan samu ya watsa ruwa dan ba ƙaramin gajiya yayi ba, shigowarshi kasar kenan ko gidansu bai kai da zuwa ba ya sauka a guest house din shi dan sosai yake da buƙatar hutawa,wanka yayi da ruwan zafi mai zafi sosai sai da ya gasa jikinshi sosai ya gasu sannan ya fito ko cream bai tsaya shafawa ba Three quarter da single kawai ya saka ya kwanta take bacci yayi awon gaba da shi cike da zallar natsuwa yake baccin kallo ɗaya zaka yi mashi ka gane baccin wahala yake...Baccin one hour Sanda yayi dan bai tashi ba sai da Abbas yazo shine yama tadashi daga baccn bayan ya fito toilet ya ƙara watsa ruwa zama yayi saman stool ya fara shiryawa bayan ya gama shafe shafenshi ya murje jikinshi da turaruka masu dadin kamshi da saka natsuwa,yadi ya samu mai kyau da tsada brown calor ya saka sanan ya saka hula da cover shoe ba ƙaramin kyau Sanda yayi ba cike da izzarshi da gadara yake taka kasar har ya shigo parlo inda ya tadda Abbas yana cin cake, kallonshi Abbas yayi yana sakin murmushi yana cewa."Masha Allah na Jamila bada kanka a sare,Umar Sanda angon Jamila wannan kyaun duk Jamila za'a je a nuna ma shi.?" Murmushi kawai Sanda ya saki yana cewa."Kai dai ka sani dan rainin hankali kawai mutun na baccin shi azo a wani tadashi ko gudar mashi ciwon kai ba'a yi." Ɗage kafaɗa Abbas yayi yana cewa." Okay why not ka koma ka kwanta baccinka,kaga nima sai naje na cigaba da tawa sabgar ko.?" Time ya kalla yana cewa." Kai dai ake ji tashi muje ko.?" Tashi Abbas yayi yana cewa."Hope ka gaya mata zuwan namu ko.?" Gaba yayi yana cewa."A'a." Cike da mamaki Abbas yake cewa."Kamar ya A'a?daman haka ake zuwa wajen budurwa without notice.?" Tsaki yayi yana cewa."wallahi Abbas ka cika matsala notice din mai zan mata? yarinyar da taki natsuwa ma musan inda alaqarmu ta dosa baki ɗaya totally bamu waya fa bata Kirana.?" Numfasawa Abbas yayi bayan yayi ma motar key yana cewa."Dan bata kiranka shine kaima ba zaka kirata ba ko.?" Lumshe ido yayi yana buɗewa yana cewa."Abbas Please forget about this unnecessary issue haba mana ko wayar dole ne.?" Jinjina kai Abbas yayi yana cewa."A haka kake so yarinyar ta aure ka?karka manta bata baka ita akayi ba Sanda kawai a baka dama ka nemi so wajen yarinya ita tace tana so fine ayi da kai ita kuwa tace a'a kasan dai mahaifinta ba zai mata dole ba ko.?" Murmushin gefe baki Sanda yayi yana cewa." Ai duk duniya ba wanda ya dace ya zama mijin Jamila sai ni nan Umaru Farouk Sanda dan ni kaɗai aka hallaceta kaga mubar maganar Please." Taɓe baki kawai Abbas yayi yana cigaba da driving din shi ba tare da ya sake cewa komai ba.
★★★
"Jigida." Dukar da kanshi Jigida yayi yana cewa."Hutawarka lafiya maigida." Jinjina kai Diga yayi can ya gyara zamanshi yana cewa."inason asa yara kamar guda biyar suna kula da duk wani motsinta dan ta kusa fara zuwa wajen aiki." Numfasawa Jigida yayi yana cewa."Angama Oga Alhaji Tahir yana ta kiran waya dazun." Wani kallo kawai yayi ma Jigida yana maida idanunshi a lumshe, Furzar da naunauyen numfashi Jigida yayi yana cewa."Maigida lokacin da yake kiran kana bacci ne shiyasa ban kawo maka ba dan bani son tadaka."A haɗa mota zamu tafi gidan shi a yanzun nan." Angama mai gida." Numfashi kawai Diga ya furzar yana jin zuciyarshi ta rage zafin kishin da take mashi dazun tabbas yasan kalamanta sun tafasa mashi zuciya wanda take yaji ina ma bai nemi alfarma wajen Baba na komawar nata wajen aiki ba,ashe ma missing din su take har take iya furtar mashi kalmar tana missing din wasu banzaye yan wajen aikinta numfasawa yayi yana tashi ya shiga ciki dan shiryawa zuwa gidan Alhaji Tahir,wayarshi ya dauka wanda yake waya da relatives din shi kawai ya duba miscall dinta har ukku ya gani sai kuma text massage bai duba ba har sai da ya gama shiryawa sanann ya zauna ya fara karantawa murmushi ya saki yana jin wani sanyin dadi yana ratsa zuciyar shi duk da ba wasu manyan kalaman soyayya ta rubuto mashi kalmomin hakuri ne kawai sai daga karshe da tace _ilove You myluv_ sosai ya nemi duk wani ɓacin ran da yake ciki ya ɓace...Koda ya fito duk angama shirya komai har Dila ya shiga mota shi kawai yake jira ya fito su wuce,kallon Jigida yayi yana cewa." Salisu ban buƙatar yin wannan tafiyar da kowa daga ni sai kai kawai." Kallon shi Jigida yayi yana cewa."Angama maigida." Matsawa yayi gaban motar yana kallon Dila yana cewa."Maigida yace bada kai zai yi tafiyar ba." Wani irin kallo Dila yayi mashi yana cewa."kamar ya bada ni za'ayi tafiya ba Jigida? Bayan kowa ya sani a gidan nan nike kai maigida duk inda zashi."Ai bani nace ba kai za'ayi tafiyar ba ko.?" Cikin zallar takaici Dila yake cewa."Jigida kana shigar man hanci da kudundune fa,kayi kokari kabar shigar man gona duk wata gulma da kake kitsaman a wajen Maigida ina sane da kai fa."idan naki fa.?" Cewar Jigida cikin fushi dan daman can ba wani jituwa ake ba tsakanin Jigida da Dila,gyaran murya Diga yayi yana cewa."Salisu ko anfasa tafiyar ne.?" Fitowa Dila yayi yana cewa."Allah ya tsare maigida." Jinjina mashi kai Diga yayi yana cewa." Dila nawa wayaunka da dubararka suna burgeni ka gaya masu gidan Alhaji Hadi zamu je." Dan zaro ido Dila yayi yana cewa."Maigida suwa kenan.!?" Dafa kafadar Dila yayi yana cewa." Su Jigau idan sun tambaye ka mana." Numfashi mai sauti Dila ya sauke yana cewa."Shikenna Oga a dawo lafiya." Da haka suka Diga suka bar gidan shi kuma Dila wayar shi ya fiddo a cikin aljihu yana dannan kira bayan an dauka ya ɗan duka kaɗan yana cewa."Oga ya fita." Numfasawa Dila yayi cike da takaici yana cewa." Naso ayi tafiyar nan dani kasan halin mai gida da ra'ayi ban san dalilin da yasa yace fa Jigida zai yi tafiyar ba ranka shi dade." Daga bangaren Buba ke cewa." Kuskuren da zaka ringa aikatawa ba tare da ka sani ba Dila shine Diga ya dunga fita ba tare da kai ba,balle fita irin wannan mai mahimmanci haka wai ma gidan wa ya tafi.?" Gidan Alhaji Hadi." Glass cup ne hannun Buba bai san sanda ya kubce daga hannunshi ba ya tarwatse tsabar firgitar da yayi tashi yayi yana cewa."What? Alhaji Hadi again?Dila kace gidan Alhaji Hadi fa.?" Jinjina kai Dila yayi cike da damuwa yana cewa."Kwarai kuwa Maigida can suka nufa ku....yi man shiru Dila ko na aiko yanzun a sare maka kai." Buba ka dakatar da Dila daga maganar da yake yana mai cigaba da cema Dila."inason ka jini da kyau Dila karka kuskura yau ta ƙare baka binciko man maganar da suka tautauna ba yau,idan har kayi kuskuren rashin kawo man maganar da Diga yayi da Hadi kayi kuka da kanka dan babban masifa ne yake neman tunkaromu mudin Diga ya dinke da Hadi karka manta Hadi makiyinmu ne kuma ɗan hayaima ne." Take zufa ta ketoma Dila taya zai iya jin maganar da Diga zaiyi da Hadi bayan da Jigida kawai ya fita?ya tabbata ko giyar wake yake sha ba zai taɓa iya tunkarar Jigida da magana irin wannan ba dan tsab Jigida zai ma sauke mashi kai yanda bai haɗa Diga da kowa ba maganar da Buba yayi ma Dila ce ta dawo dashi haiyacinshi yana cewa."A gaskiya Maigida ban san ta yanda zanyi ba wajen kawo maku maganar da suka zanta da Hadi duba da bai fita da kowa ba sai Salisu Jigida kuma kasan dai yanda Jigida yake da Maigida bai taɓa faɗin sirrinshi kuma nida Jigida ba wani jituwa muke ba balle ma." Dogon tsaki Buba yayi yana cewa." Na dai gama magana dole ne ka san yanda zakayi ka shiga jikin Jigida daga yau zuwa gobe dan jiyo mana maganar da suka tautauna." Bai jira ansar Jigida ba ya kashe wayarshi yana zagaye babban parlonshi zuciyarshi cike da tarin fargaba daga shi har Muhi kuwa da yana zaune akayi wayar sai dai shi Muhi bai nuna nashi tsoron a fili ba.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.