_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 52*
Cike da takaici Hajia Kubrah take kallon Umar Y tana cewa."Aikin banza aikin wofi wallahi Umar ya zama dole yarinyar nan tabar gidan nan akan wane dalili zata shigo falor alhalin His.Excellency na nan abin takaicin ma harda yimana amai muna break,wannan rubbish ne impossible." Numfasawa yayi yana cewa."Sorry Momy dan Allah kiyimani lamani kibar Jummala ta zauna wajen Ba'ba kinga dai yarinyar nan marainiya ce kuma yar amanace."nuna shi da yatsa tayi tana cewa."saika maidata inda ka daukota bazan iyaba nagaji."shiru yayi take yaji kanshi ya daure mashi yarasa abinda zaice mata da ido ya rakata harta isa wajen Jummala dake zaune gefe Rumaisa na taimaka mata ta wanke bakinta yan aikin gidan suka fara gyara wajen data bata."dan uban ki zo nan,uban wa yabaki damar shigowa part din nan without permission sannan saboda kin raina mutane zakiyi mani kazanta muna kalaci,maza tattaro kayan ki ki nemo gidan uban ki." Momy kiyi hakuri."yiman shiru Rumaisa zan saba maki."a hankali Jummala ta dago idanuwanta da sukayi jajir dasu tsabar wahalar data sha hawaye na zirarowa saman kuncinta tace."na tuba Momy bansan ya akai aman nan yazo mani ba,kiyiman aikin gafara idan kika koreni bansan ina zani ba."dacen daga gidan uban wa kike?kingane mani ja'irar yarinya."wallahi kuwa Momy nima nagaji da ganin wannan abar."Ke Hunaisa zan ballaki kika kuma magana."A husace Umar yayi maganar har saida ta tsorata da yanayin yayan nasu."Okay that's great akan wannan kenwar zakaima ya'ta ihu ko?akan wannan tsintacciyar magen zaka fasama ya'ta kunne ko? Ni dakune agidan nan nabaka nan da 2hrs ka kaɗa kanta ka maidata inda ka dauko ta."hannun Hunaisa taja suka haye sama sai bambami takeyi."Ya Umar kayi hakuri akan abinda Momy tayi maka,tashi Khadija kidaina kuka sannu Allah yabaki lafiya."ɗagota tayi ta tashi tsaye."Ya kaita wajen Baba insha Allah very soon Momy zata sako daga fushin ta."thank for your sopport."muje Jummala."gaba tayi har suka fita harabar gidan idanuwanta sunyi sumtum dasu."ya kika tsaya.?"sauke kanta tayi kasa cikin sanyin murya tace."kayi hakuri Yallabai kayi hakuri nina jamaka duk abinda yafaru,dan Allah kabarni na koma rugarmu kasan zamana a gidan nan bazai yuyuba kodan lalurar dake jikina!kayi hakuri nagaza tsaida aman dayazo mani shiyasa dan Allah ka maidani wajen Baffana."Girgiza kai yayi yana cewa."Aa Jummala zaki zauna BQ nasan Momy bata zuwa wajen ina son ki zauna tareda Baba komi kikeso zan baki ba sai kin shiga apartment din Momy ba,kuma ga Rumaisa zata taimaka maki."girgiza kanta tayi tace."akwai matsala zama a gidan nan kasani na dauki Momynmahaifiyata,ni nasan hakan yana cikin qaddarata da akwai yanda zanyi tabbas dana cire wannan lalurar a jikina,Allah kasakaman."wasu irin kwalla suka taho mashi ya samu ya maidasu ya dubeta cikeda tausayawa yace."Allah zai saka mani Khadija,ki daure insha Allah zaki haihu lafiya,ina so gobe ki shirya zan kaiki asibiti ayi maki awo."ance mutuwa akeyi."Aa ba zaki mutu ba kinji yar amana."kwallan idanuwanta ta share ta kuma kallan shi tace."nagode da kulawar ka 'yar labai."bakomai 'yar amana yanzun mi kike son ci."ina son fura da nono nayi kewarta."murmushi yayi yanajin dadi aranshi yace."Yau zakisha fura har sai kin koshi muje wajen Baba."tafiya sukayi suna isa ya iske Baba zaune saman kujera cikin makimancin falor tana ganin Umar ta mike ta gaishe shi cikin tarin girmamawa."yauwa Baba ya aiki.? "Alhamdulilahi."masha Allah,Baba ga yar amana na kawo maki bana son tana fitowa duk abinda zata bukata zanyi mata kuyiman magana sannan na hanata kowane kalan aiki,fatan kin fahimceni."nagane ranka shidade,duk abinda kake so zanyi mata."toh nagode maki ga wannan ki rike koda kuna bukatar wani abu."kudi ya bata wanda darajar su zasu kai akalla naira dubu ɗari."yauwa Baba tana son shan fura zanje inkawo mata dan Allah kitabbata tasha."shikenan mai gida baka da matsala saika dawo."juyowa yayi ya kalli Jummala ya fadada murmushin fuskar sa yace."bayan fura baki son komai.?"jinjina kanshi tayi tace."Ita kadai nike so."toh yar amana ko zakisha kankana."gyada kanta tayi alamar eh."saina dawo."Allah yatsareka da tsarewarsa ya kareka da kariyarka."Amin yar amanata."tafiya yayi suma suka shiga ciki Baba na janta a jikinta tana debe mata kewa.Yana isa parking space ya shige mota ya tafi akan hanya ya daga wayan shi ya kira Aliyu sukaci gaba dayin waya harya isa wajen siyen furar bai bata lokaci ba ya siyo mata sannan ya siyo mata kayan fruit ya jiyo gida yanayin parking ya fito."sannu da zuwa oga."yawwa Mudi ya aikin.?" "Alhamdulillah,yallabai ka kawo in daukar maka kayan."Aa Mudi nagode."sannu mai gida ka huta lafiya."Amin."tafiya yayi kai tsaye BQ din ya nufa."Ya Umar."ya tsinkayi muryar Hunaisa da kanwar Momy Anty Zakiyya."My Anti saukar yaushe.?"murmushi tayi tace."30 mnt ago,ya aikin oh ashe yau week end baka fita ko.? "Eh amman anjima zanje in gabatar da wani program."Alright ina zuwa naga ka nufi bayan gida.?"ɗan maida duban sa yayi kan Hunaisa ya wurga mata hararar da saida yan cikinta suka juya yace."zanje wajen Baba ne,ina zakuje haka.?"Hmm zamuje shopping kasan ɗana gobe yake dawowa."gaskia kam dole ki shiryama ɗan lele."Am Umar."Na'am Anti."miya hadaka da ledoji duk ina masu aikin gidan nan.?" Kallan ledojin hannun shi yayi yace."No nafison nayi aikina da kaina."well sai mundawo."okay kiyoman tsaraba."dariya tayi tace."yeah."juyawa sukayi da ido yabisu yanajin haushin Hunaisa matuka da suna tafiya saita juyo ta kalle shi har suka shige mota sannan ya shige BQ."Sannu da zuwa yallabai."yar amanata sannu da gida ina Baba.?"Taje gun Momy."okay gata kisha kinji."to nagode yallabai."ki tabbata gobe kin shirya da wuri kinji."insha Allahu."sai anjima ko.?"Allah yakaimu lafiya."Amin."yana fita daga BQ din ya nufi side dinshi.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.