041

2 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 41*

"Khadija ki saki jikin ki,ko baki dauke mu kamar yan gidan ku ba."cewar Rumaisa Murmushin karfin hali Jummala ta kakalo tace."Aaa Anty na dauke ku amatsayin yan uwana." Murmushi Rumaisa ta sakar mata tana cewa."ko kefa idan hakane ki saki jikin ki,kidaina dararewa sannan idan kina daki kidaina zama da wannan hijabin haba Kawata."kallan ta kawai Jummala takeyi tana mamakin hali irin na Rumaisa bata da matsala ko kadan,saidai tana fargabar kada ta takurata akan saita cire hijabin jikinta."kefa Anty nace,inajin dadin zama dake,kin rikeni da karamci Allah yasaka maki da alkhairi."tayi maganar a raunane zuciyar ta na karewa ga tarin damuwa a saman fuskar ta Kama tafin hannun ta Rumisa tayi tace."idan hakane daga yau inason ki daukeni matsayin kawar ki,ba Anty ba,sannan bansan ina ganin ki a rakube banajin dadi,kada ki manta kefa bakuwar Yayana ce,idan yana ganin ki baki walwala bazaiji dadi ba,dan Allah Khadija ki saki jikin ki idan kina da bukatar wani abu kisanar mani zan maki." Jinjina kai Jummala tayi tana cewa."Nagode."Murmushi Rumaisa ta kuma sakar mata tace."tashi kije kiyi wanka ga kayanan ki dauka kisaka sai mu sauka kasa break,kinsan ahalin ki basu son jira."nan ma gyara kai tayi tana danne damuwar ta,mikewa tayi ta nufi ban dakin da addu'a tashiga,tayi arba da wani tattausan gress kafat shimfide a toilet banda kamshi ba abinda ke tashi,ga komai sai daukar ido yakeyi da kallo tabi ban ɗakin kamar wani makwancin dan adam.Itadai tinda dake bata taba ganin ban daki irin wannan ba tsaye tayi tana al'ajabin irin tarin duniyar dake kwance a bathroom din,a hankali ta saka kafarta saman lallausan kafat din har saida ta runtse idanun ta,jin wani yam da tsikar jikin ta,tayi a haka harta shiga inda aka killace domin yin wanka tsaye tayi tarasa ta ina zata soma kunna famfon tafi minti biyar a wajen tarasa yanda zatayi sake runtse idon ta tayi takai hannun ta saman malatsin fomfon ta danna,batasan sadda ta bude idanun taba a razane jin saukar ruwa daga saman kanta yana zuba zuwa gangar jikin ta,kuri taima shawer dake zuba ta koma gefe tana sauke ajiyar zuciya tsoro yakamata."Ohni Khadija ya zanyi in tsaida wannan abar."ta furta a zahiri sake komawa tayi ta kara danna control sai ga famfo ya kawo a hankali ta shide ajiyar zuciya sannan ta zare tufafin jikin ta ta dauki sabulu da cup ta dibo ruwa tafara sawa kanta,tana wanke jikin ta a hankali,wani irin kuka ta barke dashi lokacin data fara wanke fatar cikin ta,ganin yanda cikin ta fara tashi nashiga Ukku ni Jummala ina zankai kayan kunyar nan ya zanyi da wannan rayuwar a gidan mutane?Tajima tana kukan bakin cikin da takeji idan ta tuna tana dauke da cikin shege a jikin ta,idanuwan ta saida sukai luhu luhu tsabar kuka sannan ta dauraye jikin ta,ta dauki katan towel dake aje cikin wata karaman laka ta daura sannan ta zira katan hijab din ta,ta aje kayan ta saman washing machine sannan ta fita.

Zaune ta iske Rumaisa tana duba hand out,fuskar ta dauke da murmushi ta tari Jummala."sannu kawata zo ki shirya."tace tana nuna mata stole dake gaban mirrow."toh."tace a sanyaye yanayin ta,ta kalla tagane tayi kuka."Khadija lafiya.?"Tayi tambayar itama cikeda damuwa."bakomai."bata kuma takurata ba tace."yanzun bari in baki wuri kishirya ga jalabiya nan kisa tinda naga kawar Yayan nawa batasan saka matsastsun kaya."a sifar zolaya tayi maganar,tare suka sakarma junan su,murmushi."nagode kawata."Ki sameni karamin falor kinji.?"toh."fita tayi zuwa karamin falor dake cikin dakin ta,ta zauna taci gaba da aiwatar da harkokin gaban ta.

Itako Jummala sauri tafara dan shiryawa saidai tana daukar mai zata shafa taji wani irin tashin zuciya ya taso mata da gudu tayi bathroom takama kyara amai kamar zata fiddo hanjin ta,ta jima tana abu ɗaya sannan ta wanke bakin ta,ta gyara wajen data bata ta fito jikin ta ba kwari,bata kuma komawa wajen diresing mirrow ba dan shiryawa.

Kaya kawai tasa,tana kallan kanta a jikin madubin wardrope kayan sun mata kyau sannan basu kamata ba,yafa gyalen tayi mai fadi har saida yakai mata kirji kamar himar haka yai mata tayi kyau,takalmi tasakala flat shoe,sannan tafita falorn,ta iske Rumaisa tana waya."Eh inada Exam 11am ne."ta ida maganar tana duba agogon hannun ta daga bangaren Umar yace."ya zakiyi da yar amanata ko zaki kaita wajen Baba.?" Ya ida maganar yana danna hancin motar shi cikin harabar Jounarl dinsu."Haba Yaya ga Momy sannan yau Hunaisa bata jarabawa basai taje wajen yar aiki ba,yanzun fa ta zama yar gida."yaji dadin maganganun Rumaisa hakan saida ya bayyana saman fuskar shi."shikenan kanwata yanda kika ce haka za'ayi,ina Jummalar.?"shiru tayi tana kallan ta,ganin yanda tayi kyau sosai sakar mata murmushi tayi."Jummala dai?"Oh i forget Khadija."Murmushi tayi tace."gata."mika mata wayar tayi,ta karaso ta amsa cikin ladabi zama tayi kasan kafat."ina kwana."Lafiya lau yar amana,sorry nafita bamu gaisa ba,ina sauri ne."Bakomai yallabai,ya aikin."yanda tace yallabai saida yaji wani iri a ransa."alhamdulillah yanzun zan shiga office."Allah yataimaka ya bada sa'a."ameen yar amana."Ya Antyn taki hope kinajin dadin zama da ita.?"wannan karan murmushi tayi tana kallan Rumaisa."tana da kirki sosai nagode da karamcin ku a gareni."Shima murmushin yayi yanajin dadin addu'ar ta."bakomai ki kara sakin jikin ki,sannan zataje school saiki tafi wajen Momy fira ko.?"nudding kanta tayi tace."toh."Bata phone din."duk da batasan mi ake cewa phone ba amma ta gane waya yake nufi mikamata wayar tayi."kanwata takaina Allah yabada sa'ar Exam."ameen yayana."take care bye."Da haka ya kashe wayar,ta kalli ta tace."kinada another name ne naji yace Jummala." Ɗaga kai tayi tana cewa."eh haka Babana ke kirana saboda inada sunan maman shi." Murmushi ta saki tana cewa."Ayyah amman Khadija yafi dadi ko.?"eh."tace tana murmushi."okay muje muyi break fast ko.?"toh."tace tabi bayan ta,tana mamakin miye kuma haka.

Koda suka isa dining ba kowa a arean,jan kujera Rumaisa tayi taima Jummala alamun ta zauna.Zama tayi tace."nagode."itama zaman tayi tana danna wayar ta Saving girl din su tazo tagara kokarin zuba masu karin kumallan."ranki shidade mi za'a zuba maki.?"cewar Aysha."plantain and egg."cewar Rumaisa.Zuba mata tayi sannan ta dauki flat zata zubama Jummala,Rumaisa ta katseta ta hanyar daga mata hannu."baki tambayeta ra'ayin taba."Yi hakuri ranki shidade,mi za'asa maki."ta tambayi Jummala."dankali."tace a matukar sanyaye.Zuba mata chips tayi ta aje mata kechap sannan ta koma gefe ta zauna..Kowa a cikin su fara cin abincin sa yayi cikeda natsuwa ba wanda ke magana,inda Jummala ke yaba dadin abincin da takeci kamshin turaren Hunaisa ya sanar dasu isowar ta dining arean domin ba wanda yaji tafiyar ta saidai suka ganta tsaye ta rike kugu tana karema Jummala kallo cikeda mamaki ga tarin kyamarta a saman fuskar ta."Hassana miye haka.?" Ta tambayi Rumaisa tana nuna Jummala aje spoon din hannun ta,tayi tace."Khadija ce wani abu.?"tayi maganar ba yabo ba fallasa taɓe baki Hunaisa tayi tana cewa."A dining gidan nan,kina zatan tayi break fast damu a sit daya kuma thesame time mike damunki Rumaisa.?"girgiza kanta tayi tana mamakin halin Hussaina tace."Calm down haba Hunaisa bai dace ba,we're thesame ba wani banbanci,koba komai ki dubi girman wanda yakawo ta wajen mu."Lafiya mike faruwa."Cewar Momy dake saukowa saman benen falorn zuwa dining."bakomai Momy."cewar Rumaisa zama Momy tayi tana faɗaɗa annurin fuskar ta."Momy good morning."Rumaisa tace tana sakara Momyn tasu peck a goshi."Morning dear ya shirin exam.?"alhamdulillah yanzun zan tafi."Barka da safiya Momy."cewar Jummala tana soke kanta kasa."Yawwa Khadija hope kina lafiya.?"ahamdulillah."Maida kallan tayi kan Hunaisa da har yanzun take tsaye tana cika tana batsewa,murmushi Momy tayi tace."have a sit."zama tayi tana cinno baki."Mikewa Rumaisa tayi ta dauki hand bag dinta tace."Momy zan wuce ga Khadija saita tayaki fira saina dawo."Well Allah yatsare yabada sa'a."ameen."juyawa tayi zata tafi taji anrike mata jikka juyowa tayi ta kalli Jummala."ki zauna ki huta."aaa muje in raka ki."gaba tayi tabiyo bayan ta suna fitowa driver ya bude mata back sit ta shiga ta zauna,Khadija ta miko mata jakkar tace."Allah yakaiki lafiya yadawo dake lafiya"Ameen kawata,mi zansiyo maki."kidawo da wuri dai."gyada kai tayi tana jin kamar ta hana Rumaisa tafiya waving juna sukeyi hartabar harabar.

Komawa tayi cikin falorn da sallama dauke a bakin ta,Momy ta amsa mata,a darare tayi hanyar dakin Rumaisa ganin wulakantaccen kallan da Hunaisa ke aikata mata shiyasa tayi deciding komawa daki kafin Rumaisa ta dawo."Ke zo nan."Wani irin tsoro ya darsu a zuciyar Jummala,juyowa tayi ta duka gaban Hunaisa tace."Gani."Jacking din gyalen kanta tayi da karfi tace.

☆☆☆☆

Sanda ya tura case din Hafiz Ma'azu Kotu dan yake mashi hukuncin laifin daya aikata kamar yanda addini ya tanada duk yanda Alhaji Ma'azu yaso ya murku she shari'ar amman komai yaci tura.High Court yakai shi inda Kotu ta yanke mashi hukuncin gidan yari na wata ukku akan gangancin da yayi na bige mutun sannan yabar shi batareda ya bawa wanda ya ture hakuri ba karshe yabisa da dukan dayai sanadiyar kwanciyar shi Asibiti sannan yaje ya rusa masu muhalli da tarin cin zarafi da yaima iyayen sa hakan yasa Umar Sanda nunawa Hafiz karfin hukuma da yanda doka ketaka kowa komai darajar ka ko tarin nasabarka sannan Kotu taci Hafiz tara na gyara muhallin daya bata da kula da lafiyar sa har sai ya warke,wannan hukunci ne akai masa wanda akema taken Idan kunne yaji......Ranar yan Jaridu da kafafen sadawarwa maganar da ake kenan musamman da akaga mahaifin sa shine Ɗantakarar gwamna akarkashin Jam'iyar (NPP).Hakan kuwa yajanyo cece kuce a cikin al'umma wannan kenan.

Share pls

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now