038

5 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 38*

Jikin Hannatu yayi kyau ciwukan da aka jimata sun warke yau kimanin sati ɗaya kenan rabon Ubaidu da fita koda waje yana zaune yana bawa kanwar sa kulawa ta musamman har tasamu sauki zaune yake cikin dakin shi ya aje dutsen kankara yana wasa wukaken sa daketa faman daukar ido suna walauniya saidai fuskarsa bata bayyana komai sannan ba wani annuri a jikinta kamar yanda ba wani fushi a tare da ita.Sallamar Hanne ya tsinkaya ta shigo dakin hannun ta dauke da koshiya daga kansa yayi daga aikin wasa wukar da yakeyi ya daura su kanta yana sakar mata murmushin dake nuna tsantsar so da kaunar ta agare shi kallon wuƙaken Hannatu tayi tana numfasawa tace."Sannu da hutawa yayana."jinjina kai yayi yana cigaba dayi mata murmushi."Yawwa yar yayan ta."yace yana karbar koshiyar dake hannun ta dame na fura taji kindirmo sai daukar ido takeyi."Aaa inyeh yan matana angirma da kanki kikayi wannan aikin.?" Ya ida maganar yana kallonta,rufe fuskar ta tayi da tafin hannunta alamun jin kunya tana cewa."Eh nice."Yaji dadin hakan ainun domin fuskar sa ta bayyana hakan."motso kisha kinji Hannata."girgiza kanta tayi alamun Aa."miyasa."Ya tambayeta cikeda damuwa firzar da naunauyen numfashi tayi tana cewa."dan kai nadamata naga bakacin abinci ba kuma bansan yunwa ta kama mani yayana."matsowa yayi kusa da ita yana tallabo habar fuskarta ganin damuwa akan fuskar ta."Mike damun ki.?"Ya tambayeta yana tsareta da idanunsa dake manya dasu,masu saka kwarjini a zuciyar wanda ake kallo."kasha dan Allah zan sanar maka abinda ke damuna."A sanyaye tayi maganar,bai kuma yimata musu ba ya dauki ludayi yafara shan furar da yakejin dadin na ratsa shi kamar bai taba shan fura mai gardin taba,yasha tafi rabi sannan yayi gyatsa yace."Nagode maki Allah yaimaki albarka."ameen."tace tafara shan furar."Hannatu."yakirata da cikakken sunan ta,hakan yasata saurin kallin shi,tasan magana mai mahimmanci ce zaiyi da ita."Na'am.""Baki da wanda tafini a duniyar nan kigaya mani damuwarki." Dan murmushi ta sakar mashi tana cewa."hakane Yayana dan Allah ka sanar mani abunda kuka jima kuna boyemani dangane da mahaifiya ta da kuma Baba Ladidi."Gyara zaman sa yayi yana ture takubban dake gefen sa yace."yanzun kuwa zan sanar maki tawan."yace yana Murmushi itama Murmushin tayi tace."inajinka yayana."cigaba da cewa yayi.

_LABARI_

"Shekaru sha bakwai da suka shuɗe anyi wata baiwar Allah mai suna Maryama tana da ɗa ɗaya dan kimamin shekaru goma cif aduniya,tana dauke da juna biyu wanda take gabar haihuwa a kowane lokaci.
tana zaune a gidan mijin ta,tareda mahaifiyar sa,kullin ba abinda takeyi sai ganin ta kyautatawa iyayansa ta kula da hakkin mijinta tun daga dukiyar sa har zuwa mutuncin ta,watarana da bazan taba mantawa da ita ba ranar wata litinin da safe Allah ya kawoma wannan baiwar Allah haihuwa tafara nakuda a cikin dakin ta,tun tana yi ita kadai har abu yaci tura,baki daya gidan kukan ta keta shi da tsananin nishin da take fitarwa ɗai ɗai,tana cikin wannan hali,sai Allah ya jefo mata danta ya dawo daga wasan sa,kallo ɗaya taimasa ta kauda kanta tana faman fitar da zufa,a gigice wannan ɗan nata ya iso gareta ya tallabeta yace."Umma miyasame ki,kike kuka.?bata iya bashi wata amsa ba sai zufar dake faman tsatsifi mata abinka ga yaro baisan halin da mahaifiyar tasa take ciki ba sai yafara kuka yana riko hannun ta.tashi Umma kidaina kuka Ba'ba ce ta dake ki,ko?kiyi shiru zan rama maki.ya ida maganar yana cigaba da kuka,saidai baida karfin da zai daga mahaifiyar tashi.Deeni kirawo mani Ba'ba kace tazo ta taimaka mani zan mutu."jin kalaman mahaifiyar sa ya kidima shi da gudu ya fita daga dakin zuwa dakin kakar tasa tana kwance tana bacci,ba abinda ke damun ta. Cikin kuka Deeni ya shiga ɗakin Ba'ba yana cewa kizo kitaimaki Ummana zata mutu."yace yana bubbuga kakar,da kyal ta tashi ta shararama wannan yaro mari tasa kafa ta halba shi tana."'Dan iskan yaro ina ruwa na dan waccen yar isakar uwar taka zata mutu,ince cikin shege ne ta kunsa dan wancan cikin ba jinina bane dan haka saidai ta mutu ba zanje ba,wuce kabani waje lalatacce.haka yaron ya dawo yana kuka saidai yana shigowa dakin su ya iske mahaifiyar sa kwance jini na zuba a jikin ta ba rai.wata uwar kara ya saki mai gigitawa hakan yai sanadiyar fitowar makotan sa,saidai wannan kakar tasa batai yunkurin fitowa ba bare ta tallafi sirikar tata.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now