_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 92*
"Ba'a yi ma Umar Fatah warning kuma ba'a yi mashi barazana Buba idan yanzun naso sai na binne ka a cikin gidan nan binnewa ta har abada." Dan shiru Diga yayi yana numfasawa yana mai cigaba da cewa."Amman a yanzun ba zan binneka da ranka ba har sai lokacin da na bukaci hakan dan haka ina son ka sani daga kai har su kananun kwarin da suka aiko ka wajena ka ce masu su guji ranar da Umar Diga zai waiwayesu dan ranar ba zata yi masu kyau ba,kuma ban hanaku cigaba da bibiyar rayuwarta ba inason ku cigaba karda ku tsaya daga inda kuke ku cigaba har yaran da suke maku aiki a cikin gidan nan nawa ina sane dasu na barsu suyi iyakar yin su kuma nida ku ne mun saka kafar wando ɗaya ne." Sakin Buba Diga yayi yana wullar dashi saman kujera yana komawa ya zauna zaman kujerar shi yana nuna mashi kofar ba tare da ya ce ma Buba komai ba..Buba babu abun yake sai uwar zufa yana share jiɓin da yake zubo mashi a saman goshi sauke ajiyar zuciya yayi a karo na ba adadi ya dago yana kallon Diga yana cewa."Yanxun ni Umar zakayi ma haka?ni Buba zakayi ma haka ko Umar?zaka gani naji ɗin mu zuba nida kai shege ka fasa." Ɗagowa Diga yayi yana cewa."Inason irin wanann wasan Buba,daga yanzun zamu zuba nike kai za'a gane waye shegen a tsakanin Umar Diga da Buba." Jinjina kai Buba yake zuciyarshi tana mashi zafi akan abinda Diga yayi mashi dan kuwa shi kadai yasan abinda zai yi ma Diga a wannan rayuwar, numfasawa yayi zaiyi ma Diga magana ya dakatar da shi ta hanyar nuna mashi kofa ba tare da yace komai ba,ganin Buba bai da niyar tashi ya taɓa hannunshi sai ga Dila ya shigo yana cewa.'Allah ya taimaki mai gida." Lumshe idonshi Diga yayi yana cewa."Dila Sarkin wayau ina son hutawa bani buƙatar takura." Murmushi Dila yayi yana cewa."Angama Oga."gyaɗa kai kawai Diga yayi yana maida idonshi ya lumshe, shi kuwa Dila tashi yayi yana kallon Buba cikin rashin mutuncin yake cewa."Kai tashi ka fita daga dakin nan bama iyakar dakin ba duka gidan ko kuma na saka ka dogon bacci."wani kallo Buba yake ma Dila yana cewa."Kai Diga har wuyanka yayi kaurin da zaka iya korata?wato duk aikin da kake man na kawo man sirrin Diga duk ka...katseshi Dila yayi yana cewa."zaka fita ko kuwa sai na baka mamaki.?" Hannu Dila ya kawo ma Buba da wani ƙarfe a hannu da sauri Buba ya tashi yana nufar hanya yana cewa.'zaka gane ne daga kai har Diga din daman kaima kasan ina ciki dake."cikin rashin mutuncin Dila ke cewa."ka daɗe ba'a gane ba din kai din banza ai daga kai har shi Muhi din da kake takama ya dawo a wajenka baku isa kuyi man komai balle ma yazo kan Maigida dan kuwa Maigida yafi karfin duk tunaninku sakarkaru."haka Dila ya raka Buba cikin wulaƙanci da kaskanci har motar shi sai da ya fita daga gida sannan ya koma yana cigaba da sabgar gabanshi.
★★★
Ɗagowa yayi yana kallonta cikin da damuwar abinda mahaifiyar tashi take mashi yake cewa."Dan Allah Momy kiyi hakuri tunda kika kirani nazo kike ta faɗa kina ta maganganu wallahi ni ban gane inda maganar take ta dosa ba baki ɗaya,ban san mai nayi ba ban san laifin da nayi maki ba Momy,amman dan'adam ai ajizine Inason ki gaya man laifi na sai na baki hakuri na kuma gyara Momy dan Allah." Cewar Umar Y cike da natsuwa yake ma Hajia Kubrah bayanin, sauke ajiyar zuciya Hajia Kubrah tayi tana mai cewa."Wato ma Umar hayagagar banza kawai nike kenan?kana nufin kai duk abun nan bakayi man komai ba ko.?"Girgiza kai yayi yana cewa."Ko ɗaya Momy ba hayagagar banza kake ba,amman dan Allah ki gayan mai nayi dan wallahi na duba na kuma hanga ni ban ga abun da nayi ba."furzar da naunauyen numfashi tayi tana cewa."Umar ban isa da kai ba ban isa na saka kayi ba a matsayina na mahaifiyarka ban da wannan matsayin Umar banda shi a wajenka dan baka dauke ni da daraja ba balle har nace kayi, kayi nidai haka qaddarata take ban da iko da abinda na haifa."cike da damuwa yake girgiza kai yana cewa."innalillahi wa'innalaihirajiun Momy,dan Allah Momy kibar cewa haka Momy baki ɗaya kalaman nan naki basu da dadin ji dan Allah Momy karda kiyi man baki mana a matsayinki na mahaifiyata wanda banda kamarta a duk fadin duniyar nan, Momy idan har baki isa dani ba to wa zai isa dani Momy?Momy kece fa kika yi silar zuwana duniyar nan fa."Ai Umar duk kana mantawa da haka,kana mantawa da nice nayi silar zuwanka duniya tunda har idan nace ga yanda nike so kayi ba yi kake ba."numfasawa yayi yana cewa."To Momy Kiyi hakuri ba zan sake ba gayaman maine kika ce nayi banyi ba yanzun naje nayi na tabbata shafa'a nayi ko a lokacin da kika saka ni."Numfasawa tayi tana cewa."Umar."Gyara zamanshi da kyau Umar yayi yana cewa."Na'am Momy." Firzar da naunauyen ajiyar zuciya tayi tana mai cigaba da cewa."Maiyasa da nace maka kaje kaga Nafisa ku sasanta kanku akan maganar aurenku baka je ba.?"
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.