_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 18*
Sake musabaha sukayi atare suka fito zuwa office din Umar suka zauna numfasawa Umar sanda yayi yana kallon Umar Y da kyau yana cewa."Journal Umar ina son ka rage ma Kanka damuwa haka Please,in shaa Allah very soon Jamila zata dawo gareku nayi maka wanann alkawarin by the grace of God." Goge zufar gashin shi Umar Y yayi yana cewa."damuwa kam ai akwai Acp masoyiya fa ake gaya maka? Ban cikekken bacci tunda aka dauke Jamila ina cikin tarin tsoron da zallar firgici dan ban san ko kwaron wajen da take ya cutar da ita balle azo ga wani mahalukin dan Adam,na rasa da yanda zanyi."wata irin tafasa da zafi zuciyarshi take tun da Umar Y ya kira masoyiyarshi wanda yake kwana da tashi da zallar tunaninta wai masoyiya,taya zan iya jure wanann furucin daga wajen Umar Y?bayan abinda Umar Y din yake so shima ita yake so,yana jin bai taba iya rayuwa babu Jamila a tare dashi ganin farko lokaci guda ta sace mashi zuciya,taya zai fara wanann yankin?taya zai fidda Umar Y a cikin zuciyar Jamila ya saka kanshi dan kuwa shi Umar sanda yafi dacewa da ya zama mijin Jamila ba wani Umar Y ba,ganin irin kallon Umar Y yake mashi yasa ya sakar mashi murmushin da iyakarshi kan laɓe yana cewa."karka damu Umar ba kai ɗaya ba duk wani masoyin Jamila bai sake samun kwanciyar hankali ba tun randa aka ɗauketa kwana muke sallah da fatan Allah ya baiyana ta cikin aminci da kuma koshin lafiya." Murmushi Umar Y ya saki yana duba wayarshi da take famar ringing ganin Momynshi ce yasa ya dago yana kallon Sanda yana cewa."Allah yasa Allah ya ƙara mana ita muna godiya Acp Allah ya ƙara girma." Jinjina mashi kai Sanda yayi yana tashi yana cewa."Ameen." Har bakin motar ya raka Umar Sanda sai da yaga tafiyarsa,sannan shima ya shiga tashi motar dan tafiya gida dan yasan kiran Hajia Kubrah Yusuf ba yana nufin ya dauka bane a'a yazo gida tana son ganinshi kuma yasan dai maganar bai wuce dan ya gabatar da shirin TA FARU TA ƘARE ne,yana rasa mai ke damun Momynshi bai san yaushe ta chanza hali irin haka ba,yasan shi da Momynshi mace ce mai tausayin tallakawa da kuma son ganin ta taimaka masu sai gashi rana ɗaya lokaci guda tana neman sauya hali,da wannan tunanin ya isa government house of Katsina state,sai da ya fara zuwa apartment dinshi ya watsa ruwa ya kintsa sannan ya shigo gida,yana shigowa tsaye ya taddata waya a hannunta sai cizon yatsa take.
Ko amsa sallamarshi Her Excellency Hajia Kubrah batayi balle har ta barshi ya zaune da yatsa ta nuna shi tana cewa."Anya kuwa Son ka ɗauke ni a matsayin mahaifiya.?" Rintse idonshi Umar Y yayi da karfi yana budewa a hankali gami da zuwa dan kama mahaifiyar tashi dan yasa a irin situation din da take ciki zata iya yin furucin da daga baya za'a zo ana innalillahi wa'innalaihirajiun kawai,ja da baya tayi tana aika mashi wani irin kallo tana cewa."wait karka sake ka taɓa ni wallahi Umar idan har ka taɓa ni zan baka mamaki ne,just Answered my Question?" Ɗagawa Umar Y yayi daga shirin kamata yana dafe kanshi da yake shirin tarwatse mashi tsabar bala'in da take neman saka shi bayan yana fama da ba rashin Jamila,matsala saman matsala kenan firzar da iskan bakinshi yayi yana cewa."Momy dan Allah kiyi hakuri,amman banda kamarki duk duniyar nan kece mahaifiyata ina matuƙar Kaunarki Momy." Dogon tsaki taja tana cewa."karya kake Umar,Umar baka sona baka kaunata a matsayina na mahaifiyarka Umar tun da har kake bada gudummawar da wasu mutune zasu dinga zaginmu a gidan Radio,wai Umar uban kake nufi da wanann tsinainiyar yarinyar Jamila?nace uban mai kake nufi a kanta Umar? Uwarka ce aka dauke Umar? Ko ubanka? Ko kuma ƙanenka Umar? Dubi yanda ka koma kazama wani banza ka rame kayi baki akan mace, Umar anya kuwa?anya Umar kana son albarka uwa ta bika.?" Kasa motsi Umar Y yayi yama rasa mai zai ce hawaye ne yaji suna zubo mashi akan kumatunshi ba tare da ya shirya zubowarsu ba yana auna yanda zai yi da mahaifiyarshi ta barshi ya auri Jamila da ba abinda yake hange a cikin kwayar idon mahaifiyar tashi face zallar tsanar Jamila innalillahi wa'innalaihirajiun abinda yake cewa kenan a cikin zuciyarshi,yana numfasawa yana cewa." Sorry Momy ban gabatar da shirin TA FARU TA ƘARE ba dan cin fuska a gareku har kullum ina nuna maki shirin TA FARU TA ƘARE shiri ne da tallakawa suke samun damar kawo kokensu a wajenku gwamnati nasa hakan dadi zaku ji dan kun samu hanyar da zaku gyara kuskurenku idan kunji anfada Momy,kuma shirin TA FARU TA ƘARE ba ruwanshi da wata hamaiya ba'a zagin gwamnati sai dai kowa ya fadi ra'ayinshi dan kawo gyara Momy." Dan shiru yayi yana kallonta ganin yanda take mashi wani kallon ya maida kanshi ƙasa kawai,cikin masifa take cewa." Ba wani Umar karya kake ba wani ba shirin hamaiya bane,maiyasa tun can da Hikima station bata kirkiro shirin TA FARU TA ƘARE ba sai da muka hau kan mulki?abun baƙin cikin da takaicin ma wai har da kake ake gabatar da shirin,ba wannan ba nace uban mai ke tsakaninka da Jamila idan baka gayaman gaskiya ba wallahi yau sai ranka ya ɓaci a gidan nan zan nuna maka nice nan na haifeka ba kai bane ka haifeni bar ganin komai kace kana so ina barinka kana yi okay kana amfanin da son da nike maka shiyasa kake ta abinda ka gadama ko?to kaine bango har aikin jaridar sai ka daina shi Umar." Sauke ajiyar zuciya Umar Y yayi yana cewa." Momy ina son Jam..marin da ta sauke mashi a saman kumatu ya dakatar da kalmar inason Jamila da yake kokarin gaya mata ya makale a saman harshenshi,tunda ya girma yayi hankali ya mallaki hankalin kanshi Momynshi bata taɓa nuna mashi yatsa ba balle har azo ga mari ba Momy ba har His Excellency Alhaji Yusuf Umar bai taɓa yi ma koda fada ba saboda son da iyayen nashi suke mashi komai yace yana so to ne kawai dan gudun ɓacin ranshi,har aikin rediyon da yake ba dan suna so ba sun barshi yana yi dan farincikinshi tunda yace yana so,yau ga Momy apple of his eye ta ɗaga hannu ta mareshi akan mace, idanunshi jajir sukayi kamar wanda gauta haka suka koma,cikin bata umarni Hajia Kubrah ta fara cewa." Har abada bakai ba Jamila wallahi Umar kai ko zaka mutu akan Jamila na gwanmace da ka auri matsiyarciyar yarinyar nan na tsaneta ban kaunarta ba zata taɓa zama matar ɗana ba ɗan ma wai kai Umar Allah ya sawaƙa man asarar addini,kai koda mata suka ƙare baka ba Jamila gwamna ka ƙaraci rayuwarka a haka ba mata,dan haka tun wuri ka cireta a cikin zuciyarka idan kuma ba haka ba wallahi duk abinda ya samu Jamila kaine ka ja mata sakarai ɓaceman da gani ko ranka ya ɓaci." Cikin Muryar kuka Umar Y ya girgiza mata kai yana cewa."A'a dan Allah Momy naji kiyi man ko wane irin hukunci kima hanani aikin Radio amman karki rabani da Jamila,Momy wallahi inasonta ba zan iya rayuwa babu ita ba dan.... Ya isa haka Umar" ta katse shi tana mai cigaba da cewa." Nace ka ɓace man da gani ko?zaka tafi ko sai nayi furuci a kanka Umar?" Hawaye ne ya share yana nufar hanyar fita yana jin kanshi yana mashi wani irin ciwo yana sara mashi tsabar masifar da Hajia Kubrah ta jefashi a cikin,ikon Allah ne ya kai Umar Y apartment dinshi zubewa akan three seater parlonshi yana rintse idonshi yana jin yanda zuciyarshi take mashi wata irin tafasa kuka ne kawai yaje ya kubce mashi haɗe kai da gwiwa yayi yana kuka kamar wani ƙaramin yaro.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.