003

12 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 3*

Komawarta office keda wuya,wayarta tahau ruri sunan da ta gani a jikin wayar yasa taɗan waro idanu waje ɗagawa tayi cikin natsuwarta da ta gama game mata jiki tana cewa."Assalamu alaikum Ranki ya daɗe barka da yau.' daga can bangaren ko sallamar ba'a ansa mata ba sai ma cewa da akayi." Jamila inason ganinki gidana yanzun." Kallon time Jamila tayi tana dan jinjina kai tace." Afuwan Ranki ya daɗe yanzun lokacin tashi na ne daga wajen aiki ina buƙatar zuwa gida dan na huce gajiya ina neman ayi man uzurin zan shigo cikin dare ko kuma gobe da safe." Furzar da iskan mai zafi akayi ana cewa."urgent nike buƙatar ganinki dan haka after isha'i kizo." Bata jira mai Jamila zata ce ta kashe waya sai huci take..da kallo Jamila tabi wayar tana taɓe baki gami da mamakin isa da izza irin ta yan siyasa da kuma bada order dan kawai ta kasance matar commissioner sai tace zata matsa zata duba idan har bata samu fita ba bata ga wanda zata fiddata cikin dare ba saboda shirmenta na banza da wofi,dogon tsaki taja tana haɗa kayanta dan tafiya gida.

Ajiye wayar tayi tana zagaye babban parlon gidan da ya gaji da haduwa dan cike yake da kayan more rayuwa iri-iri,kallon ɗaya zaka yi ma parlon kasan parlon yaci sunan na gidan commissioner tsabar haduwa,wayarta ce ta dau ruri taje ta ɗauka tana cewa." Ƙarki damu mai girman Her Excellency kibar case din Jamila a hannuna ni nasan yanda zanyi da ita idan har tace zata ja da siyasarmu dan haka yau zata zo gidana bayan sallar isha'i zakiyi yanda muka yi da ita." Kwafa tayi bayan ta gama sauraren maganar Her Excellency Hajia Kubrah tana cewa." Her Excellency sai kace bani bace?kar manta wacece Hajia Khadijah mana kin san ba abinda ba zan iya ba akan siyasarmu dan haka calmdown and reliex pls and pls." Murmushi kawai tayi tana ajiye wayar a wani stool tana hayewa sama.

☆☆☆☆

Gudu yake shekawa kamar zaibar kasar baki ɗaya tsabar gudu ko gaban shi bai gani bisa babban titin birnin tarayya dake cikin kwaryakwaryar Abuja Amadu Bello Way ba,da misalim karfe  bakwai da rabi na yamma..duk motocin dake faman tsere a bisa Central way din amman matashin saurayin mai jin jini a jikinshi bai sararama motocin dake saman kamilallan titin ba,haka yake zuƙema motocin kana ganin shi kasan shafaffe ne da mai ɗan wani ne,ba inda ya dosa sai tamfatsetse Mall na Grand Square dake cikin birnin tarayya,Koda ya shiga compound din wajen inda zai saƙa haɗadɗiyar motarshi ƙirar Lambogini  da gudu securities din wajen sukayo wajen shi dan bashi wajen daya dace da parking motar tashi.

Tsaye suke bakin motar inda Saurayin yake ciki kana ganin shi kasan ya gaji da haɗuwa gami da tara kayan jin dadin duniya wato dollars..Kama handle din motar yayi yana kokarin fitowa cikin zama wani securitya ya wage mashi kofar,inda ya ziro kafafun shi waje cike da gadara gami da izza...Tsaye yayi bakin motar yana ƙarema mutanen wajen kallo ɗaya bayan ɗaya sannan yaja kafar shi zuwa gaba kadan bayan anrufe kofar motar,duƙawa da kanshi wani security yayi yana cewa."Ranka shidade sannu da zuwa Allah yataimakeka."A hankali yaɗan zame glashing idon shi ya ɗan kalleshi tare da ɗaga mashi hannu kadan sannan yai gaba cikin tankamemen wajen na Grand Square,yana shiga ba inda ya dosa sai sashen da ake siyar da ice cream cike da girmamawa aka taroshi tare da bashi seat ya zaune yana daura kafa ɗaya kan ɗaya,ko minti ukku bai ƙullaba aka kawo mashi ice cream domin sunsan abinda yakawo shi kenan har flavor din da yake ra'ayin sha sunsani.
Yafi ten minute da ajiyewa kamar baisan da sun aje ba saida wipe din wajen tace."Sir ur order is ready."Still bai kalleta ba sai aikin danna waya daya keyi yana sakin smile mai tsanin fidda fasalin kyawunsa tare da haibarsa gami da rantsastsen kwarjinin dake shimfiɗe bisa killatacciyar fuskar shi.

A hankali yakai hannu ya ɗebo ice cream kamar baison sha yakai baki tare dan lumshe idanunshi masu kama da shanyayyu irin maijin baccin nan a hankali ya waresu bisa screen din wayar shi...Faruk Umar Faruk kenan wanda yakeji da tarin kuriciya gami da nasaba uwa uba kudi dake kai mashi karo ɗa ɗaya tillo a wajen mai Girma Shuganan Ƙasa kuma Jika ga Sarkin Jihar KATSINA STATE,Faruk ya kasance cikakken namiji mai haiba sannan rudun dukiya yasa kome ya gani yana so ya imani da kudi zasu bashi shi,komai darajar abun haka komai kaskancin shi,sai dai ya kasance wanda baisan daraja,martaba da girman na gaba dashi ba,a lokacin dayaga dama yake taka wanda yaso koma wanene,saboda shidin ya kasance ɗan gata kuma ɗan usulin Jihar Katsina a wajen mahaifiyar sa,mahaifin sa haifaffen asalin Jihar KADUNA STATE ne,sannan shine shugaban Kasa dakeci a halin yanzun kuma suna cikin tenure dinsu na farko.
Ya kasance mai tarin ilimin zamanine har degree na ukku Phd ya gamashi a Hill Cons University England UK.
Amman a bangaren arabi ilimin addini baisan komai ba sai abunda ba arasaba,wannan kadan daga cikin nasabar Faruk Umar Faruk kenan.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now