_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 24*
A takure take jikin bango banda kuka ba abinda takeyi kamar ranta zai bar gangar jikin ta,tsabar kukan da takeyi tun da ya shigo yake tsaye yake kallanta yana dubawa da hangawar maiye ya sata kuka haka?ko dai ita kuka yana mata dadi ne?ya lura da ita abu kaɗan ta saka kuka komai komai dai tayi mashi kuka,wata kila kukan nishadi yake sakata bai kowa mata wata lalurar shiyasa ta mai dashi abokinta,dan ƙaramin tsaki yaja dan so take ta zamai mashi ciwon kai dan bai son damuwa da takura,da ace bata ci amanarshi ba da yanzun tana gidansu amman tunda har ta iya kiran Sanda a waya ba zai taɓa maida ta ba har sai Sandan da kanshi yazo ya dauke ta har zai juya ya tafi sai ya dan dakata yana maida numfashi yana cewa."Mi akai maki.?"A tsorace ta dago kanta dake sara mata tana saukewa a kan fuskarshi maida kukan tayi gami da maida kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tana cewa."Dan Allah ka maidani wajen iyayena kaifa kace mutumin kirki ne kai." Kallon ta yayi da kyau yana cewa."Nayi dake.?"girgiza mashi kai kawai tayi ba tare da ta iya furta komai ba, karasa shigowa cikin room din yayi yana cewa."Miyasa kikai kokarin guduwa.?"A kidime take kallan shi take jikinta ya dauki mazari ta ko ina a jikinta rawa yake taya akayi yasan tayi niyar guduwa? Bayan kaf gidan suka fice shi da yaransa suka barta ita ɗaya, innalillahi ashe abinda ta furta a saman lip dinta a hankali bata yarda ta kalli ko inda yake ba,tsaki ya ja mai tsawo yana cewa."Badan sunsan matsayin dana bakiba,da kin jima da zama gawa miyasa zakiyi kokarin guduwa.?" Share hawayenta tayi da bayan hannunta,dan ita tasan bata ga kowa ba ina ya bar mutunen da har suka ganta suka gaya mashi taso gudawa?ko daye ba abun mamaki bane dan babban gidane mai cike da part part dan koda tayi kokarin guduwa bata san inane hanya ba, numfasawa tayi tana cewa."Sunce maka zan gudu ne.?" Girgiza mata kai yayi yana cewa."Aaa yanayin ki sun tabbatar mani da hakan." Dan shiru yayi zuciyarshi tana mashi zafi tabbas da ace bai nuna matsayin Jamila a wajenshi ba da tuni tabar duniyar baki daya sai dai kawai ya tarar da gawarta take kamanin fuskarshi suka sauya dan shi a rayuwar Umar Diga bai san taurin kai da rashin jin magana ya kuma lura yarinyar tana dasu,iska ya kaima bugu har sai da ta ƙanƙamai jikinta, numfasawa yayi a hankali yana cewa."Jamila."Na'am"
kukan da takeyi ya kuma karuwa rufe idonsa yayi sannan ya bude."Koda zansa asakeki tun daga safe har yamma bazaki iya gane hanyar fita daga gidan nan,ba tsafi bare sihiri."Dan Allah katai maka mani."Bakin ce Umar Sanda zaizo ya dauke kiba."Wlh Allah bansan shiba kayar dani Umar"Yanda ta furta sunan shi saida tahu wani yanayi ya fisge shi."Repeat."Kallan tuhuma tai mashi."My name." Lumshe ido tayi tana cewa."Umar."Wannan karan saida taja sunan nashi."Gobe zan mai daki gida promise koda wasa bazaki kuma zubda hawayen ki ba." Ɗaga mashi kai tayi tana cewa."Alqawali."Ansar handkerchief daya miko mata tayi ta share kwallan ta sai dai tayi mamakin yanda yasan zata gudu bayan wanda ya kamata yai mata alkawali bazai gayama Diga ba."Yafaɗa maka ne."Mike nan.?"Zan gudu."Murmushi kawai yai mata baice komai ba,saima bude karin da tai mashi yayi alamun karatu,itama gyara zama tayi alamun yafara a nutse yai bissimillah yakaran ta tass ko gyara batai masa ba."Daman ka iya karatun ka ko.?"Eh Babana malami ne."Dandanan idanun sa suka kada jajir kamar zaiyi kuka."Miyasa ka shiga damuwa lokaci ɗaya.?"Idan kika zamani zan gaya maka sirrina."Kamarya idan na zama kai."Bai fada mani zaki gudu ba sai dai ina shigowa na gane ta hanyar yanayin falor daya hade kadan."Ya canza maganar ta hanyar bata amsar ta ta farko jinjina kai tayi tana al'ajabin Umar."Umar."Banda mahaifiya ta,ke kadai ke cika mani sunana da zuciya ɗaya."Wannan karan Murmushi tayi wanda ya bayyana kyawunta."Sauran dake kiran sunan naka da wata manufa suke kiran ka da Umar."Jinjina kai yayi alamun eh sannan yace."Karamin tunda nakaranta maki duk da baki yaba mani ba."Kayi kokari sosai kanada basira."Haka Babana ke cewa."Nan ma zuciyar shi ta raunana karin ta cigaba da yima shi ta jima sannan yace."Zanyi kewar ki musamman karatun da kike mani kece kika fara yimani wa'azi bayan Babana."Bin bayan shi tayi da kallo harya fita daga dakin ta,tana juya kalmar Baban sa kalmar dake saurin karya zuciyar Umar Diga.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.