008

8 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 8*

Muhi ne cikin dakin shi wanda yake cikin katan jejin da suka hana kowa bi tsabar hatsabibancinsu na kamen mutane da suka maida bayi tare da karbar kudin fansa inka hana kayi ta ranka,kimamin watan su Jummala Ukku a hannunsu Muhi wadda a yanzun ya maidata kusan matar shi kullin yana manne da ita,wadda yakema tsaro na musamman dai-dai da yatsanta wani yai kokarin tabawa bako shakka yana kashe shi,tunda ya samu Jummala bai kuma taba wata ya' mace ba sai ita kadai yau dinma haka tana saman jikinsa sai shafar karan bayanta yake cikin tsantsar shauki...Itako kukan zuci ya zama ibadarta duk da bata yanda zatayi ne,tanajin yanda hannayen sa ke yawo ko wane bangare na jikinta musamman kirjinta da yake matsatsu son ransa gami da hade bakin su waje daya yana mashi sashihin sha kamar ya samu sweet.

Haka yake chakuda Jummala yanda yake so yana gurnani gamida jan numafashi mai zafi tanaji tana gani ya gama kusantarta ga jaraba bai gajiya da kusantarta kusan kullin ko tafiya sai tayi da kyal take yinta tsabar azaba dake sha hannun Muhi,baisan ko kuda ya sauka saman fatar jikinta,tattalinta yake kuma ba abinda ta nema tarasa,fatar kunnenta yake lasa yana cewa a hankali kamar wani mai jin bacci."Jummi."Kallansa tayi da idanunsa wa'anda basu da mararraba da barkono tace."Na'am."Hawaye na zirarowa saman fuskar ta,harshensa yasa yana lasar su ita dai idanunta a rufe tsabar kuna da ranta ke mata,sakar mata nauyenyen iska a saman fuskarta yana cewa."Ke matatace bazan iya rabuwa dake ba,kina nan har abada ban bukatar kudin fansar ki,domin kin gama yimani kowace fansa,inason ki haifa mani magajina karki kujeni."Sake fashewa da kuka tayi tana bugun kirjinta cikin tsantsar tsanarshi tana cewa."Natsaneka ban kaunarka,ka sakeni inkoma hannun iyayena bansan ganin fuskar ka." Ta ida maganar tana watsa mashi yawan bakinta a fuskar shi.

Murmushi yayi tare da fisgota ya kamo kanta gab da fuskar shi numfashin su na hadewa ua tura harshensa cikin bakinta yana tsotsar shi cike da gayya sa ida ya galabaitar da ita sannan ya saketa zugi radadi da zafi ke addabar bakinta,bai damu da irin azabar da take ji ba,sai ma tallabo fuskarta yayi yana saka idonta cikin nashi yana cewa."Saime dan kin tofan yawo karki manta yawonki sun fiye mani zuma zaƙi da dadin sha,dan haka idan sun maki yawa ki sanar dani zan zuke maki su,kuma daman ban buƙatar ki sone ko ki kaunaceni abinda na sani ɗaya ni Muhi nayi mata ba inda Jummala zata koma tazo nan kenan zaki haifa man yara masu kama da ke."Yana gama fadan haka ya tashi yana zura  wandonsa da rigar shi ya fita, har ya kai bakin bukkar ya jiyo yana mata wani kallo gami da sauke numfashi yana cewa."Ki killace mani dukiyata."With killer smile gami da kashe mata ido ɗaya yana karasa fice cikin bukkar ranshi fas.

"Buga kanta tayi kasa tana kuka jitake inama ta mutu ta huta,ahaka gwara ita saboda su Halima da sauran matan da aka kamasu rana ɗaya namiji ukku har hudu na iya kwanciya da mace ɗaya ba wani gata a wulakace haka suke keta masu haddi..kuka kawai take tanajin komai na duniya ya fice mata da ace Oga Muhi zaibi ta yanda take yasa bingida kawai ya tarwatsa mata kai tabar duniya ta huta dan ya gama da ita ya gama wulakanta mata rayuwa baki ɗaya,bata da wani sauran mutunci da zatayi tutiya dashi nan gaba a matsayin ta na ƴa mace ya rabata dashi tana jin inama ba'a haife ta a cikin wannan duniyar ba mai cike da kalubale iri-iri na rayuwa duniyar nan cike take da masifu daban daban-daban daga wannan sai wanann mutunen cikinta zuciyarsu cike take da zalunci da kuma rashin tausayi da imani.

       ☆☆☆☆

       _ABUJA_

Katafaren dining ne iya ganinka ba abinda ke yawo sai kayan abinci iri iri na gida dana waje,ga tarin kayan fruits and drinks iri iri,kai kace dinner mutun ashirin akeyi,amman kaf illahirin wannan kasaitaccen dining kirar turkish royal ba wa'anda ke kai zaune a dinning din sai mutun ukku rak iyaye biyu tare da ɗansu rak wanda sukema sahihin so,goge baƙinshi da tissue yayi yana ɗagowa ya kalli dan nashi cikin natsuwa ya kira sunanshi."Farouk." Dakata wa da shan ruwan ruman da yake yana ɗagowa yace."Na'am Dad." Sai da Mrs president yayi kusan 3mn da kiran Farouk sannan ya furzar da iskan baƙinshi mai zafi yana cewa."Yaushe zakayi aure.?" Kai tsaye ya jefa mashi tambayar dan a halin yanzun ba abinda Mr president yake son gani sama ga auren Farouk,sai dai ya lura kamar Farouk ba abinda ya saka a gaba ba kenan,mai yake jira da har yanzun baiyi aure ba?abinda yake yawan tambaya kenan kudi ko mai?koda bai zama president of Nigeria ba to har Farouk ya mutu ba zai taba kukan talauci ba ta ko wane bangare dan gata ne gaba da baya,idan kuma matane kullum cikin kawo ma Farouk tallar mata ake tun daga kan yaran ministocin da gwamnoni har da sarakuna ma da manyan yan kasuwa,amman yake ya kwantar da hankalinshi ya zabi mata a cikin ba abinda ya saka a gaba sai shirme kawai da zuwan club da join shi abun ya isheshi.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now