058

3 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 58*

JAMEEY

"Tanan ka bullo kenan?Hmm gaskia basirar ka na birgeni saidai kasani bazata taba yi maka anfanin komai ba."murmushi Diga yayi yace"da gaske? aikin ka na kyau kuma na jinjina maka Jami'in tsaro,saidai kasani zakaran da Allah ta nufa da cara.."hmm ta yaro kyau take bata karko banyi tunanin har karfin halin ka zaisa ka tako kafar ka har nan ba, duk da baisan abinda ya kawo ka ba ina so kasani bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane be care ful."tafa hannun sa Diga yayi yace."ba abin mamaki bane idan nace abinda ya kawo ka nima shi ya kawo ni nan ya kaji wannan labarin?" Ya ida maganar yana kashe ma Sanda ido ɗaya gami da sakar mashi murmushi,a fusace Sanda yasha kwalar wuyan sa yace."tabbas dana baka babbar dama saidai kasani nayi maka rata kaima kasani, bana jin zakayi kafada da kafada dani ba na girmi hakan."bige hannun Sanda Diga yayi daga jikinshi yana cewa."well yayi kabani damar kamar yanda ka fada."na baka idan kere na yawo zabo na yawo kasa wannan aranka." Jinjina mashi kai Diga yayi yana cewa."godiya nike, nagaishe da Jami'in tsaro Umaru Sanda fatan alkhairi."jinjina kai yayi da haka yai gaba cikin gidan shi kuma Umar ya shige mota suka bar gidan, tunda suka fito ba wanda yace uffan a cikin su ba kadan maganganun Sanda suka kona masa rai ba yarasa dalilin da yasa Sanda ya saka ido akan shi irin haka ba, mike tsakanin shi da Jamila tambayar da yakema kanshi kenan saidai ya rasa amsar tambayar sa..Koda Sanda ya shiga cikin gidan kai tsaye falorn Baba ya sauka suka gaisa bayan fitar Baba bada jimawa ba Jamila ta shigo kana ganin yanayin zakasan badan tana son zuwa bane girmamawa ra'ayin mahaifin ta tayi daga sama har kasa yake kare mata kallo baki daya fuskar shi babu annuri bakaramin mataki ya daukarma fuskar sa tunda yaga Umar ranshi ya sosu matuka."ina yini."ciki ciki ta gaishe shi kamar anyi mata tilas yanda take cinno baki gaba,wani kallo Sanda yayi mata yana cewa."miye hadin ki da wancan mahaukacin mutumin.?" Sai a lokacin ta dago kanta ta kalle shi yanda taji yai mata tambayan a kausashe kamar zai duke ta har saida gabanta ya dan fa'di yanda taga fuskar sa murtuke dan kauda kanta gefe tayi tana cewa."ban bangane ba wake nan"? Nikam miye hadina da mahaukaci kuma.?" Wannan karon a fusace ya mike tsaye ya matso dab da ita kamar zai duke ta yace."ke kike da hadi da mahaukaci tunda yanzun naga ya fita sai yanzun nagane dalilin  da yasa kike yabonsa." Dan ja da baya tayi tana taɓe fuska tana cewa."koma minene bai dame ka, kai ke mashi kallon mahaukaci amma ni cikakken mutun mai hankali nike kallan sa."Ya isa Jamila"ya daka mata tsawa tareda 'daga mata hannu cikin tsananin bacin rai yace."Saboda kina son sa shiyasa kuka hada baki dashi yai kidnerping din ki?saboda kiyi wasa da hankalin mutune, banda akwai wani abu a ranki minene hadin ki da 'dan iska murder wanda baisan kansa ba."Ɗaga mashi hannu tayi tana cewa."enough Umar bana son wa'annan maganganun naka! miyasa kake neman yima rayuwa ta kutse kana zaton da son raina zanbar iyayena cikin tashin hankali har na tsawo watanni? wai miyasa baka kautatawa mutun zato ne.?" Cikin masifa Sanda yake cewa."bazan kyautataba dolen ki kirabu da wancan jakin marar imani."zuwa yanzun mamakin shi ya gama kasheta itama mikewa tayi tace."bazan rabu dashi ba."kina so ki fada man son shi kikeyi.?" Ɗaga mashi kai tayi tana cewa."kwarai kuwa shi nike so, kuma abinda ya kawo ka shi ya kawo shi."ya ishe ki shut up."cikin tsananin bacin rai yayi maganar har jikin shi na tsuma yanda taga yana tafasa dolen ta ta kama kanta duk tsoro ya kamata dakewa kawai takeyi sai dai zuciyar ta cike take da tsoro."bude kunnen ki da kyau kijini danni kadai aka halicce ki, ba dan wancan wawan ba wanda yaso ya salwantar da arayuwar ki shine kike ikirarin kina so? Abin takaicin ma marar tausayi duk wanda zai dauki 'ya mace ya rabata da iyayen ta tsawon watanni tabbas baida imani be care ful idan cikin satin nan naso na aureki kema kinsan sai na aure ki zan jin kirtane domin naga karshen wancan sakaran inga karshen wasan idan kin tashi kada ki fasa son sa."gyada kanta tayi tace."kada kadamu dan Allah ka aureni cikin satin nan idan har izzarka da isarka takai, saidai ina so kasani nidin ba 'yar sadaka bace!  Son Umar yanzun nafara."takaici iya takaici ya rufesa kalaman ta suna mashi ciwo a zuciya ga mugun kishinta ya rufe shi,mamakin ta ya kama shi da kyal ya saita kansa ya saita fushin sa yace."ke baki isa ki tsara mani yanda zanyi ba, saidai kasani ni da shi masoyin naki muzuba mugani who is the winner."murmushin takaici tayi tana girgiza kanta tace."best of luck"kusan atare suka nufi hanyar fita daidai Dijja ta dauko drinks zata kawo mashi tsaye tayi daga gefen kofa yanda taga ya fita a fusace har yana kokarin ingije ta da sauri ta matsa gefe, itama Jamilan dakin ta ta nufa zuciyar ta na mata zafi, da sauri Dijja ta maye mata baya tana zama itama tana shigowa dakin "mike faruwa dake Jamila? Miyasa kikayin haka? jibi yanda kika fusata shi daga dawowar shi kasa na tabbata ko ahalin sa bai gani ba tsabar daukin ya ganki."bazaki gane ba Dijja, baki daya Umar Sanda baida manner of talk, haba dan Allah haka ake soyayya masiba yake mani kamar zai duke ni fa."zama tayi gefen ta tace."mi kikayi masa"mifa wai daga yaga Umar ya fita shikenan yake ruwan bala'i ko ubana bazaimin haka ba."Hmm my Jameey ki kwantar da hankalin ki ba wani abu bane kishi ne kawai."wani irin kallo tabi kawar tata dashi tace."kansa farau kishi? idan kikace mani shidin matsoraci ne zan fi yarda, duk ya rude dan kawai yaga Umar like yaga zakin nan, in fact har ikirari yake mani idan yaga dama in some days zai aurena irin yar sadakar nan mtsw."calm down mana ki mashi uxuri ya fada ne saboda ya razana ki."My Dijja kenan wallahi har ransa yake fada nace ya gwada tashi iyawar, a gaskia bana kaunar gadarar Sanda da nuna isar sa, abinda baki sani ba take naji nakara kaunar Umar din sai inga ya zaiyi."kin manta iyayen sa sun zo.?" Ahh kinganki neman izinin aure shine aure? Ina da tabbaci Baba bazaimin auren tilas ba, kinga nufa 'dan daban nan ya fiye mani wannan mai girman kan! Saboda shi da'n daban yasan damuwata idan nayi fushi zai sauko da zuciyar sa duk da baisan kalaman da zai fada mani ba amma zai bani hakuri idan inayi masa tijarata zai yi shiru badan komai ba saboda yana kaunata yana so na koda baisan ya soyayya take ba amman yana kamantawa kuma shidin  mutumin kirkine yasan darajar na sama dashi."hakane shima Sanda mutumin kirkine  yasan darajar na gaba dashi."kwarai kuwa nasani, saidai baisan kansa ba saboda bai iya sanin makaman da zai lallashi mace dasu ba saidai nuna isa da gadara."kiyimasa uzuri"nayi masa mana, idan ya isa ya aurenin a lokacin daya furta"kidaina gadara"hmm Dijja saidai idan sadaka za'ayi masa dani na yarda da hakan, amman idan har 'yanci na za'a bani definitely saina za'ba"lallai kam yanzun kina nufin saiki auri d'an daba"kwarai kuwa saidai kisani kuke mana kallan haka ni kam nasan shi din mutumin kirki ne"Allah ya kyauta, yanzun saiki auri da'n shaye shaye"wa'iya zubillah, kidaina fadan abinda baki gani ba Dijja ba abinda Umar ke sha, sannan kiyi masa kyakkyawan zato"gaskia ne, naga da alama kinyi nisa ga son mutumin nan"Hmm kawata kenan baki da dama"murmusawa Dijja tayi sukaci gaba da firar sannan tayi mata rakiya ta tafi gida.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now