Bismillahir~Rahmanir~raheem
Miemiebee👄 this novel is honoured to you ❤Just know that your rising star loves you to the moon round and back❤
~~~~~~
"INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN" shine abunda hajiya ZAINAB keta nanatawa durkushe ak'asa dafe da tulelen cikin dake gabanta tana runtse idanu tareda ciccije leb'e da alamar nak'udar ta tsananta.
Matashiyar matace kyakkyawar gaske wacce bazata wuce shekaru 32 ba.Yarone dan shekaru 14,wankan tarwad'a kyakkyawa wanda kana ganinshi kaga jinin hajiya zainab. Sanye yake da uniform d'in islamiyya da alama makaranta zashi. D'akin maamansu yanufa dan yi mata sallama.
"Assalamu alaikum maamana ni.... "
Bai idasa maganaba ganin maaman nasa tana rik'e da ciki tana salati. Dagudu ya k'ariso gabanta ya durkusa.
"Maamana meh sameki? Ya k'arishe maganan tareda sa kuka.
Dakyar bakinta ya iya furta.
"SADEEQ kira ikko "Dagudu ya kwasa yayi hanyar kitchen yana k'walawa ikko k'ira.
Ikko 'yar dattajiwar mata mai ak'alla shekaru 40 dake wanke shinkafar tuwo taji kamar ana k'iranta, bata idasa tunaninba saiga sadeeq ya shigo dagudu.
"Lafiya maigidana? "Dakyar yana haki yace
" ikko maamana!" Saikuma ya kasa k'arisawa yana nuna hanya.
Nan da nan ikko tagane mai yake nufi wato uwargijiyarta na nak'uda.da Sauri ta kashe gas cooker, dagudu tanufi d'akin sadeeq nabiye da ita.Shigarta d'akin har zainab tafara fita hayyacinta. Dasauri ta k'ariso tanaimata sannu tareda k'ok'arin d'agata.
"Sadeeq jeka maza kace baba driver ya matso da mota za'akai hajiya asibiti"Batare da yabata amsaba yanufi waje, daidai dazai fita sukaci karo da alhaji Anas
"A'ah abubakar lafiya? "
Cikin kuka yake nuna masa d'akin da maaman sa take.
"Baba maama ce ke nak'uda"
"Subhanallahi" dasauri yanufi d'akin zainab.
Lokacin ikko na k'ok'arin fito da ita.
"Sannu maman sadeeq! "
Yadubi ikko yace
"Ikko je ki d'auko akwatin"
"Toh yallaboi" tareda komawa ciki.Kanta fito har ya Sanya zainab a mota, sadeeq yabud'e gidan gaba ya shige.
Baba baijira baba driver ba ya shege abunsa,ikko nashiga ya figi motar, maigadi ya wangale gate suka fice,sauran ma'aikatan gidan suna addu'ar allah ya sauk'i hajiya lafiya.Isarsu asibiti akayi gaggawan shigar da ita labour room, alhaji Anas ya kasa zama sai safa da marwa yakeyi yana addu'ar allah ya sauk'e matarsa lafiya Dan jinta yake tamkar ransa kuma yana addu'ar Allah yabasu 'ya mace. In aka cire hajiya babba wato mahaifiyarshi to zainab ce ta biyun sai kuma 'ya'yanshi.
Ikko na a zaune itama sai addu'ar take ta rungumo sadeeq dake kuka jikinta.Sunkai kusan 45minutes amma ba labari duk hankulan su yafara tashi.
GIDAN HAJIYA MARYAMA (HAJJA BABBA)
tsohuwace kyakkyawa, zatakai shekaru 63 aduniya, kanaganinta kaga asalin kanuri. Kamarsu d'aya sak da d'anta wato alhaji anas, tanada kirki da taimako,ga kyakkyawar zuciya,saidai akwai fad'a inka tab'ota.
Sanye take da gilashi tana karanta Husnul Muslim.
Gib gib gib kakeji alamar ana bubbuga Abu.
Sharewa tayi tacigaba da duba littafinta.
K'arar sai tsananta yakeyi amma ta danne tatoshe kunnuwa,ji kake gaaaabbb alamar rushewar abu.
"Ohh allah na!" Hajja tafad'a tareda dafe goshi, yanzukam kasa hak'uri tayi tamik'e domin zuwa cin mutuncin mai b'arnan nan.Da shigarta falon tsaye tayi bata k'arisa shigaba, dama tasan za'a rina.
Yaro ne d'an shekaru 11 ya dage sai k'wallo yake acikin falon wane yasamu football field,ya sha jessi nashi da Boots. Gabaki d'aya yayi baja baja da falon, home theatres kowanne yayi hanyarsa, pillows na kan kujera duk kowanne yayi nasa hanyar, hatta da agogon bango shima an dugurguzoshi, kuma hakan baisa yafasa ba yadage sai bugawa yakeyi."yau ni naga takaina! ALIYU lafiyarka? Yau kuma salon iskancin naka kenan iyee! Karasa inda zakayi shegantakar naka sai anan! Kawani sako shegiyar tambulaye (boots) kamar mai raka shanu, to dai ba'anan ba wuce kayi waje maza! "
Ko kallo bata ishesaba
"Hydar badakai na... "
Bata idasa maganaba saiji bumm kakeji sauk'ar ball akanta.
"Alhamdulillahi." Tsabar rud'ewa rasa abun fad'a tayi sai hamdala.
"Ouuchh! So sorry hajja "
"Sorry'n gidanku! Wato kamayar dani sakarya ko iyee! " tafad'a cikin fad'an tana masa dank'wale.
Tab'e baki yayi alamar ke kika jiyo dan hydar akwai rashin son magana, bai iya jure hayaniya sai kuma uban b'arna."Hahahahaha"
sukaji ana kwasar dariya agefe, atare suka juya suna kallon mai dariyar. Yarone d'an shekaru 7 zaune a gaban tv ya babbaza k'afa yayi kaca kace da decoder na strong tas babu abunda bai kunceba adole yana gyara, dariyarsa yake shararawa bai ko kallon inda suke, ya duk'ufa wajen harhad'a wayoyin Dabaisan kansuba baimasan me yakeyi ba.
Sallallami hajja tafara tana tafe hannu.
"Kai kaci uwaka IBRAHIMA! "
Khaleel yad'ago ido d'aya yana dubanta had'e da smirking.
"Meh kikace 'yar matas? " Yafad'a yana kakkane mata idanu.
"Uwaka nace dan gidanku, wato bakaji ne iyee! Wani irin kunne ne dakai khaleel? Baki nawa nayi nace karka kuskura ka tab'a abunnan sai mai gyara yazo... "
"Ohh! Yafad'a yana juya idanu
"Yo what's my faulth anan dan ina gyarawa! Naga ai taimakon ki nakeyi dan naga bakida kudin gyara"
"Uban wa yace maka ban... " bata idasa ba yace
"Yo da kina dashi da tuntuni anwuce gun, ki irga kwanan ki nawa baki kalli sunna tv ba iyee! " yafad'a had'e da murgud'a baki.Baki da hanci da ido hajja tasake tana kallon khaleel,shiko cigaba da aikin gabansa yayi yana wak'arsa
Gugur gugur gugur alamar anashigowa da abu, atare duka suka maida dubansu ga k'ofa.
Yarone d'an shekaru hud'u, jikinsa duk futu futu wane wanda aka tsamosa daga tab'o duk ya rine, tsakaninsa da Allah yake turo kekensa cikin falon, basket nagaban keken cike yake da laka ga uban karare yana turawa dakyar.
Rasa abun fad'a hajja tayi tana kallonsa baki bud'e.
"Wasshh! Hajja nagaji! " yafad'a yana mik'a cikeda manyance.
"UMARU FARUKU daga ina kafito? " hajja tafad'a cikeda mamaki tana k'are masa kallo." farautan tab'o(Clay) of course!"
Yafad'a yana wani shan k'amshi shi adole yayi gwaninta.
"kuma duk nafiso samowa" yafad'a yana zama bayan ya jingini keken."Yau ni naga duniya! " cewar hajja cikin b'acin rai tana rik'e hab'a.
"Bakidai ganiba tukun yanzu kikafara harsai kinsa an maidamu gidanmu" cewar hydar yana gimtse fuska yana k'ok'arin zama.
"Ohoooo! " hajja tafad'a tare da matsowa tarik'e k'ugu.
"To kasa kunne kujini dakyau 'yan hofin yara! Komai zakuyi kuyi nidai bazaku kasheni lokacina baiyiba,bazaku kuma d'aura min hawan jiniba, abunda nasani shine babu ubanda zaibar gidannan sai jatumarku ta sauk'a,ta santalo mun jika mace insha allahu wacce bazata bamu ciwon kai ba, kafun nan babu wanda zaije yad'aura mata hawan jini. " tak'arishe sounding serious
"Kai idan baka rusa kayan dake cikin gidannan ba tas baka cika ALIYU HYDAR ba, idan kaga dama kabi d'aki d'aki kana buga ball dan ubanka! "
Tajuyar da kanta kan khaleel.
"Kai kuma dan gidanku inbaka ciro caf electronics nagidannan kayi rugu rugu dashiba sunanka ba IBRAHIM KHALEEL ba. "
Tamaida dubanta kan k'aramin kuma wanda yafi kowa k'iriniya.
"Kai kuma dawani kayinka kamar burodi nakuskura nasake ganin k'afufuwan ka a waje gurin monster zai kaika yacinye, ja'irin yaro kawai! "
"Kuyi tayi!, zamadai anan saikun zauna daram inkunga dama ku lashi kawunan ku tasama. ""Rabi! Rabi!! "
"Na'am hajja. "
"Ja faruku kije kiyi masa wanka,inkin gama kifitar da keken nan kibaiwa usman ya wanke. "
Yanajin haka yatashi yana k'ukuni shi adole ya iya abarsa uayi kayansa. Haka yana ihu rabi ta tattarashi.Hajja takallesu
"Sai kuci gaba daga inda kuka tsaya. "
Zatajuya kenan landline na falon yafara k'ara .Babu wanda yakula duk sun chona baki sama su adole fushi suke da ita.
" yan kaniyar yara masu kawunan k'arfe inkunyi zuciya ku dakeni. "
Daidai lokacin tasa receiver'n a kunne
"Assalamu alaikum"Dagacan akayi magana
"Subhanallahi! Ganinan zuwa allah ya sauketa lafiya. "
Tanakaiwa nan ta ajiye tana kwalawa rabi k'ira.
Hydar da khaleel suka mik'e don sun gane mamarsu ce."Ki kula da gidan nizani asibiti maman sadeeq na nak'uda, karkibari kowa yafita. "
"Toh hajiya allah ya sauk'eta lafiya. "Usman driver ne yazo hajja nashiga tanajin borin hydar da khaleel sai sun bita ,sharesu tayi tace
"Usman ja muje" shikuwa yafigi mota.
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romance"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...