chapter 98

1.2K 109 0
                                    

In dedication to
Miemiebee 👄

******

Saida meelah ta haihu lokacin Abba yamatsa masa kan yadawo... Shima sosae yayi missing gida hakama meelah Wanda tunda tayi aure bata jeba... Ahaka suka Fara shirye shirye Dan na dawowa gaba dayane... Yasayi gida a abuja da taimakon murad kuma yafara nema masa aeki.

Randa suka diro Nigeria murad ne yaje yadaukosu daga airport zuwa gida batare da kowa yasani ba... Lokacin 2weeks to bikin Su khaleel. Saida suka kwana biyu kafun suka hau flight din bauchi... Muneer kurum yasarwa shidinma Dan ya daukosa... Sosae yayi farin cikin dawowan yayan nasa.

Direct gidan baba suka wuce Dan an ciccika kowa da kowa hatta ummi gidan full house... Su yaa deeku mutanen kaduna an diro hatta Su hydar sun ISO.

Bandirawo ne ya bude musu gate... Yadaiga muneer saidai yana kokonton dayan yamasa kamar maheeru... A gaggauce a rufe gate din tareda isowa gun motar daidai sanda maheer yafito tareda budewa meelah kofa.

Hangangam bandirawo yasake dayaga haikan fatalwa yagani zaisa gudu muneer ya rikoshi... Su usman driver da sauran ma'aikan gidan kowa na neman hanyan guduwa Ga fatalwa...

Muneer sai dariya yake shida meelah while maheer na murmushi... Haidar kuwa yatsane bakinsa yana kallonsu duk ya gani.

"Bandirawo ba fatalwa bane... Ta6ani kaji..."ya Kama hannu shi.

"Aradu ba fatalwa bane maheeru ne... "Ya washe baki "maheeru bawan Allah dama kana duniya..."

Usman yace "dama Ana mutuwa a dawone..."girgiza Kai kurum maheer yayi yaja hannun matarsa bayan ya dauki haidar suka wuce. Daidai entrance suka hadu da Ammah dake rikeda hannun little maheer.

Ammah na ganin maheer tasake hannun maheer tajuya da gudu... Maheer yayi dariya... Oh su ammah angirma ansan ghost... Saima ta gudu tabar takwaransa... Daukansa yayi shikuwa maheer sai kallon Sa yake... Ja kumatunsa yayi yayi dariya.

Hajjah, ummi, mama, yaa deeku, hydar, khaleel, faruk, ammar, abeedah, Sarah, afdal, afeeq, da ikko duk suna zaune afalo suna hira sukaga ammah ta rugo a guje tana ghost ghosh take can bayan kujera ta buya.... Kallon kallon akeyi

Mama tace "Kai faruk jeka duba meya faru..."cikin azama faruk ya mike ya nufi kofa daidai sanda maheer Ke shigo Wa... Suna ido hudu a 360 ya juya...khaleel da ammar sukabi bayanshi.... Mama da ummi suka mimmike, abeedah da Sarah kowa ya cakumo mijinshi... Hajjah kuwa banda salati da addu'ar da tazo bakinta ba abunda take Dan yanzu ba kafa... Sadeeq da hydar ne kurum basu tsorita ba saidai they're very shocked.

Shiko maheer banda murmushi ba abunda yake aeka musu rikeda little maheer a hannunsa...ya jawo hannun meelah dake rikeda little hydar suka karisa shigowa...

Ajiye little maheer yayi akan yazaunar kan cinyarsa tareda jawo  ruwa ya tsiyaya a cup ya mikawa meelah shima ya tsiyaya Wa kansa...kamar zombies suke kallonsa.

Hydar ne yayi karfin halin karisowa ya ta6ashi...confirm mutum ne... "Buddy..."hydar ya kirashi a hankali....

Dago Kai yayi ya kalli hydar tareda masa murmushi "yeah dude..."

Tashin hankali... Nan ummi takariso tareda shafa kansa ya dago ya dubeta yana murmushi... "Ummina kema tsorona kikeji..."ya kallo inda mama Ke tsaye yace "Idan kowa zaiji tsoro na ban tsamman dake ba mama."

Habawa nan guri ya kwacime... Ya matso gurin kafan hajjah tareda daura kansa kan cinyarta "matas bakiyi kewata bane..." Kawai saitasa kuka... Ummi da mamah suka jona daganan babu Wanda yace kanzil kowa mamaki ya cikasa...

"Nikam kukannan ya Isa haka... Wanda kukayi a mutuata MA ya Isa..."hajjah ta kima masa rankwashi "rufa mana baki..."takuma Sa kuka sosae sun bashi dariya

Ana cikin haka baba yajiyo kuka suka shigo shida Abba tareda muneer... KO mamaki basuyi ba "kukan ya Isa haka Dan Allah."cewar Abba.

Baba ya juya ya kalli mazan kowa yayi zugum ya zurawa maheer idanu kamar sokaye yace "Da Allah dubeku hardakai sadeeq babu Wanda zai iya daidaita gun."

Abba ya dubi muneer yace "Kai Ja yarannan kuyi waje..."yana mikawa haidar hannu kuwa yaje... Yaja hannu twins da little maheer ya tasa keyarsu... Yadubi ammah yace "ammah c'mon."

Ta make kafada tace "am no more a baby... Am seven years old..."

Wani kallo da abeedah ta watsa Mata sum sum tabi bayan muneer sukayi waje.

Abba da baba suka zauna nan abba yafara musu bayani komai har kawo yanzu...

Nan bayan koke koke hajjah tarungumo maheer jikinta tareda meelah ta karbi little miemie tana Sa musu albarka can tace "Dan nema kakuwa San halin damuka shiga dalilin mutuwarka...au guduwanka..."duka akasa dariya...

Hakuri yakuma basu... Mama tashafa kansa tana Sa masa albarka ummi ne ma batace kanzil ba itada hydar daya cika yayi Fam...

Sadeeq yace "nimadin tamaza nayi da nariga kowa fecewa..."

Khaleel yadubi faruk yace "Ashe bamu kadai bane... Kudinma Dan munanan ne da yaa faruk inaga closet zai shiga."akasa dariya Dan tuna baya

"Ae duk tsoro ba Wanda yakaika tunda laundry basket kake shiga..."

"Ashe nawa da sauki tunda ba kasan gado na shiga ba..."

Su baba suka girgiza Kai... "Kun girma kun Fara ajiye iyalai amma haryanzu shiriritarku nanan."

"Ciwon kan da yaran nan suka bamu Allah ne kawai yasani
..zainabu ba karamin kokari kiyayiba...saratu kene kadai me iyawa mijinki Mai taurin kan tsiya nidai na sallamar"

Sarah tayi murmushi kurum daba su abba agun data maiyar

Khaleel yace "wai Ke hajjah har yanzu bakya ganin abunda twins sukayi saimu..."

"Au kajimun Dan rainin hankali... Anqi a ganin."

Ammah ya matso ya side hugging hajjah yace "yauwa amaryar shiyasa sonki..."

"Yo ae dabadan maheeru ba da wancan Mai bakin halin ya kakkaryaku..."ta nuna hydar.... Shiko KO kallo bata isheshi ba.

Khaleel dake rukeda little miemie yace "auu! Maryamu Allah Sa karkiyi halin masu sunan."

"Gidanku ibrahima..."cewar baba daidai sanda pillown da hajjo ta wurgo ya sauka kansa...

Baba yace "kawomun matana karka shafamata surutun tsiya..."

"Ae baba KO ban shafa Mata ba zatayi hali Dan dama masu sunan akwai dogon baki musamman tagefena bare kuma na abuja waiii..."duka akasa dariya sakamakon rakasa da wayar charger da baba yayi da gudu yafita yana dariya

"Maheeru Ja abokinka kar anjima ya fashe mana anan."maheer yayi dariya "kuma bawai nace ka zauna ba yau hirar nawa ne... Jameelah kwana yadawo nawa saikisan tayi sai kuma randa nayi niyar bar miki..."

Hakadai akeyita raha Ana dariya sai nan nan dasu maheer ake... Little haidar ya makale Wa Mai sunanshi.. Ammah an samu jikin maheer sai fada suke da little maheer... Mama, ummi, ikko, da abeedah sun shiga kitchen hada musu abinci Sarah kuwa taja meelah daki Dan hutawa tabar baby miemie a hannun hajjah.

******

  Maheer da hydar suna fitowa maheer yace "buddy aren't you happy to see me?"

Ko kallo bai ishe hydar ba... Ganin haka maheer ya rungure masa Kai yace "karka amsa..."zai wuce kenan hydar ya Kai masa naushi gefen ciki... Kafun ya dago ya kicking dinsa a baya....

Nan sukahau guje guje kamar yaro hydar saiya daki maheer... Sadeeq daya fito yamusu Allah shirya nan MA wai an ajiye yara... Bayan sukama world war 3 hydar ya rungumi amininsa yace "at least you could have told me..."

"I know...I made a mistake and I'm sorry..."

Nan dai suka sasanta kansu...

Nan dai aka shiga hidimar biki gadan gadan... Meelah tazama yar gida komai da ita ake... Little haidar ya makale wa mai sunanshi... Maheer kuwa saidai baiga baby miemie ba saidai abashi ya dauketa.

Ahaka har miemie tazo...

_End of flash back_

   _jeeddah_
*_MiemJeed#OneLove_❤*

Vote, comment. And share

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora