chapter 39

1.7K 138 11
                                    

In dedication to
Miemiebee 👄

*****
  Jerawa sukayi da mermu suna tafiya suna hira,dukda bata saba tafiya a hankaliba yau tsintar kanta tayi da tafiya irin na mermu Dan ita komai a nitse yake, dukda bata saba ba amma haka ta daure,rabin maganan miemie shirmene, wanin mermu tabata amsa wanin kuma tayi dariya, ita miemie burgeta takeyi saboda yanayin yadda take gudanar sa rayuwarta she's a carefree person Wanda komai za'a mata bazata nuna alamar damuwa ko bak'in ciki ba, kullum fuskarta d'auke da dariya sannan wauta yai mata yawa, sai dad'a admiring palace d'in takeyi, can tadubi mermu tace.
"Har inane haka tafiya yak'i k'arewa."ta tambaya tana dubanta.
"Shashin mai martaba ne,babu mai shiga bayan iyalansa saikuma mu amintaccun bayi."tabata amsa hankalinta naga hanya.
"Yauwa mermu na tambayeki mana."
"Karki...
"Ko d'aya tambayace zanyi gameda gidan nan ba 'yan gidan ba."cewar miemie
Sosae ta baiwa mermu dariya ta tsaya ta kwashi mai isarta kana tace.
"You're so funny Dr. Yo ina marabin dambe da fad'a,saboda duk abunda zaki tambaya na game da gidannan ya danganci mutanen dake cikinsa."
Miemie tace.
"To be sincere baina baya iya shiru inhar naga Abu, sannan kuma hankalina bai ta6a kwanciya inba na samu gamshasshiyar amsa ba so please Wannan shine ganbayar k'arshe daga wanna I promise never to ask you any sort of question regarding this palace tunda bakyaso."
Mermu tadube ta tana nazari saikuma  taga bata kyautaba.
"Am sorry Dr. Bawai ina k'in gaya miki bane...
"No! Na fahimceki mermu,gabaki d'aya bakina baida linzami,nima sometimes bana sanin abubuwan danake fad'a in ina surutu,karki damu bake kad'aiba kowa zaiyi shakkar gayamin magana musamman sirri Dan Nima ban yarda da kaina ta wannan fannin dan idan nabar Abu acikina tofa kumbura zaiyi."tafad'a tana dariya.
Mermu tayi murmushi cikeda mamaki dakuma tausayin miemie,she's a very sincere person akoda yaushe gaskiyarta take fad'a, dukda basu wani zama sosae ba amma ta fahimci hakan.
"Kidaina fad'an haka Dr. Nasan akwai abubuwa da yawa Wanda kika rik'e sirri agunki,kuma ae Dr. ciki badan abinci kurum akayishi ba harda rik'e sirri, ki rink'a k'ok'arin rik'e surrikanki saboda rashin rik'e sirri na jawo Matsala babba, at least ko bazaki iya rik'ewaba zaki iya furtawa wa mutumin dakikafi yarda dashi kamar mahaifiya,Dan uwa itace komai kuma zata iya rik'e miki sirrinki fiye da tata."
Jinjina kai miemie tayi.
"Banjin zan iya daina fad'ar magana kawai na riga na saba."tafad'a tana ta6e baki.
"Kul kidaina fad'in haka allah nayin yadda yaso a lokacin daya ga dama,yana iya shirya 6atacce a lokacin dayaga dama bareke da sirrine bakya iya rik'ewa,duk abunda kikasa allah a cikin zakiga yazo da sauk'i, saiki rok'e allah ya yayemiki sannan kina d'aurewa kina had'iye wash abubuwan."
Miemie jinjina kai tayi tana kallon mermu, babu shakka abunda mermu tafad'a gaskiyane, Ada tayi niyyar fad'iwa mama da maheer dama sauran 'yan gidansu komai daya faru a Daren jiya amma jin abunda mermu tace yasata fasawa itama zataso ta gwada rik'e Abu a cikinta.
Cigaba da tafiya sukayi mermu ta katsewa miemie tunani.
"Fad'i tambayarki inaji kuma insha allah zan amsa miki iya abunda na sani."
D'an dariya miemie tayi.
"You can't trust me on this,karnazo na baki kunya."
"Shiyasa nakeson gwadaki a yanzu,nasan ba komai bane kike fad'a so na yarda dake zaki iya rik'e wannan."ta mayar mata da murmushi.
"I promise never to let you down,zanyi k'ok'arin ganin ban baki kunyaba."ta fad'a tana dariya.
"Uhm... Ina sauraronki?"
"Iya sanina a masarauta Ana gudanar da abubuwan gargajiya dasauransu, misali irinsu bushe bushe, zaman fada, bayi kuyangu da sauran abubuwan gargajiya, meyasa a wannan masarautan ya banbanta, naga suna gudanar da rayuwarsu kamar ba hausawaba."
Shiru mermu tayi yanayin fuskarta yacanza daga fara'a yakoma alamun damuwa.
"Bazan iya cemiki ga daliliba saboda mai martaba da kansa ya buk'aci hakan,ya buk'aci ke6ancewa tareda iyalansa bayan ya mik'awa hakimi ragamar komai a hannunsa,ya baro a asalin fada ya dawo nan saboda wani dalili nasa wanda babu wanda ya sani,sannan PMB ne ne ya hana gudanar da duk wani abu daya danganci gargajiya da'ake a cikin fada.shine kurum abunda na sani."
Shiru miemie tayi tana nazari, tabbas hasashenta ya zama gaskiya akwai wani 6oyayyen al'amari dangane da wannan masarautar.
  "Akwai wata tambayar?"mermu ta tambaya tana murmushi.
Tattare k'asan gypsy skirt nata tayi Dan tun yanzu yafara takurata.
"Wad'annan 'yan mata guda b...
  "Babbar itace fateemah zarah,dayar kuma amatullah."
"Su basa maganane."
"Haka suke basu fiye magana ba musamman zarah,sun saba da zaman shiru kowacce a d'akinta take wuni da wuya kiga sun fito."
_wannan wace irin rayuwace?_ shine tambayar da miemie tayi a ranta.
Jinjina kai miemie tayi zata sake magana mermu takatseta.
"Bismillah kishiga dagama aekina nizan koma."
"Mermu na manta...
"Jan k'ofar zakiyi... Na ciki na iya ganin na waje so kishiga kafun na shiga matsala."
So take ta fad'a mata cewar ta bar iPad da headphones nata d'akin PMB sta jinjina kai tareda k'arusawa kusa da glass door d'in tareda turawa gabanta na fad'i.
Ahankali ta lek'a kanta tana k'arewa gurin kallo,anyi gurun ne kawai Dan cin abinci gefe guda wani had'adden dining table ne Wanda a k'alla zai d'auki mutane ashirin, an jera warmers kala kala ga fruits da sauran kayan karin kumallo,fad'in tsaruwar gun is a waste of time ku imagining da kanku.
  "Dr. Mariam k'ariso ciki mana."ta tsinkayi murya dabatayi tsammanin jiba saida ta d'an tsorita.
Kallonta yake fuskarsa d'auke da murmushi Wanda ya k'ara masa k'ima.
k'arisowa tayi ciki bayan ta gyara skirt nata tana kalle kalle smilingly.bata damu ta gaisheshi ba coz bata iya wannan karan ba.bayan tagama kalle kallenta tamaida kallonta kan  tana murmushi.
"Awesome! I've never seen a dinning room as beautiful as this before until now..."tafad'a in between laugher.
  Dariyarta ne ya yatsaya ganin wani fari kyakkyawar dattijo a k'alla zaikai shekaru sittin da biyu (62) gefe guda zaune akan had'adden gold wheelchair sanye da kayan alfarma fuskarsa d'auke da annuri.
  Kallonsa takeyi babu ko kyaftawa, bata ta6a ganin mutum mai k'warjinin sa ba,Sam kasa d'aga k'afa tayi still tana kallonshi.
"K'ariso mana 'yata."yafad'a d'an guntun murmushi d'auke a fuskarsa.
Kallon SR tayi yai mata alama taje da hannu.
  harta k'arisa gabanshi bata d'auke Ido a kanshi ba.tsintan kanta tayi da tsugunnawa.
"Kintashi lafiya? Ya kwanan sabon guri da kuma hak'uri damu?"shine maganar data fito daga bakinsa mai d'auke da murmushi.
Karon farko a rayuwarta taji kunyar rashin gaisuwa Wanda a zahirin gaskiya mantawa takeyi da ana gaisuwa.
Sunkuyar da kanta tayi k'asa saboda kunyarsa dataji.
"In... Ina.. Kwa.. Kwana?"
Murmushin sane ya fad'ad'a.
"Lafiya qalaw 'yata yakuma kewar gida, nasa kin baro mama da baba koh?"yafad'a bayan ya d'aura hannunsa na dama akanta.
_ya ilahi! is he the king for real? Nooo he isn't._ tafad'a a ranta
"Kina mamaki ne 'yata?"
Sai a sannan tasan maganar zuci ta fito.
Mantawa tayi a inda take da kuma gaban wa take ta d'aga Ido ta kalleshi tareda kwashewa da dariyar tan nan.
"I was wondering ko kaine mai martaban danake jin labari...nasha jin labarin saraku na dakuma miskilancin su Wanda a jininsu yake but ganinka yasa nafara kokonto ko anya kaine sarkin da gaske,dan tunda nashigo gidan nan banga hak'oran koda d'aya SG cikin masu gidan ba..."
"Dr. Anas kisan a gaban wa...
D'aga masa hannu da mutumin yayi yasashi dakatawa.
Sai a sannan miemie tayi saurin toshe bakinta cikeda wauta.
"I'm sorr...
"Shhh fad'i abunda ke ranki."yafad'a still fuskarsa d'auke da murmushi.
Kasa k'arisawa tayi tana cizan yatsa idanunta suna wik'i wik'i.
  "Ina jinki."
  "Amm.. Ermm.. Eh  dama inason sanin are... Are you really the king?"tafad'a cikeda wauta.
  Fad'ad'a murmushinsa yayi har hak'aransa suka bayyana,lallai ya jinjina wautar yarinyar nan ta wani fannin kuma ta matuk'ar burgeshi.
"Dakyau mariam,lallai na jinjina k'wazonki dan inason mutum mai fad'ar abunda ke ranshi batare da kokonto ko shakkar waniba,wannan na nuna alamun gaskiya da kuma tsoron allah, Da mutane zasuna fad'ar gaskiyar abunda ke zuk'ansu da dayawa ba'a fad'a ga halaka ba."
Sosae miemie ke murmushi tana jin k'aunar mutumin nan a ranta,SR kuwa da mamaki yake kallon abunda ke faruwa,babu shakka zuwan DR. MARIAM alkhairi ne tunda harta farasa mai martaba fara'ar da kusan shekaru shida kenan rabon da yayi irinta.
  "Banda abunki mariam ae ba duka aka taru aka zama d'ayaba,ra'ayi ya banbanta haka zalika zuciya kowa da irin tasa,duk sarakunan da kika gani a doron k'asa allah ne ya haliccesu,kuma dukanmu bayinsa ne,sarauta, mulki da arzik'i duk shike badawa wa Wanda yaga dama bawai dan ya fifita wasu akan wasu bane a'a saboda babu wanda yafi wani agun allah sai wanda yafi tsoronsa,wani lokacin allah kan jarabci mutum saboda yagwada k'arfin imaninsa,meyasa ni zanyi wasa da damar da allah ya bani na wulak'anta na k'asa dani,kinga in nayi hakan nakai kaina ga halaka..."ya fad'a still murmushi d'auke a fuskarsa tareda kauda kan gefe can yace
"Ni sarki ne amma banda damar aewatar da al'amurN sarauta saboda lalurar da allah ya d'aura min wanda nayi imani duk a cikin jarabawa tace, karki damu da abunda ke gudana a cikin gidannan ki fuskanci abunda ya kawoki, ke bak'uwata ce dani kikeda damar mu'amala, karki shiga abunda bai shafeki ba saboda tseratar da rayuwarki daga shiga fitina ko hatsari."yadawo da kansa gareta tareda fad'ad'a murmushin sa
Jinjina kai miemie tayi alamar gamsuwa dakuma mamakin furucinsa na k'arshe.
"Kisa a ranki ni ba sarki bane,ki d'aukeni tamkar mahaifinki zanfi jin dad'in haka,kimun magana tamkar yadda kikeyiwa mahaifanki,sannan ki gudanar da rayuwarki kamar yadda kikeyi a gida karki shakkar komai, duk matsalar ki karkiji shakkar sanar dani,feel at home kinji?"
Hak'oran miemie ne suka bayyana SG kuma mamakine k'arara a bayyana a fuskarshi ganin fara'a sosae a fuskar mai martaba wanda rabon da yayi irinta tun bayan shekaru shida (6) lallai zuwan  Dr. Mariam alkhairi ne.
Juyawa yayi yaga miemie na surutu fuskarta d'auke da fara'a mai martaba na murmushi alamar shirme take ta zubawa.
   Mik'ewa tayi tareda tura wheelchair d'in zuwa gurin dinning inda gurinshi daban ne, SG ya nemi hanyar fita.
Seconds tsakani hajjo ta shigo tareda zarah a bayanta, Wanda suke kama da hajjo sosae dan babu abunda ta baro mata, sanye take cikin doguwar rigar Swiss atamfa fari da ratsin mint blue ta yafa gyale a kanta.
Sam Mai martaba da miemie basu lura da alamar shigowan mutane ba saboda surutun da miemie take tana dariya.sai k'aran Jan kujera dasukaji, a tare suka kallesu, fuskar nan dai ta hajjo nanan yadda yake kullum ba yabo ba fallasa, ita kuwa babu Wanda ta d'aga Ido takalle bare asaran zatayi magana, fuskarta Sam babu alamar fara'a kamar na mahaifiyarta, ta6e baki miemie tayi ta kalli mai martaba, shima kallonta yayi tareda lumshe mata Ido alamar babu ruwanta fuskarsa d'auke da murmushi.
Maida kanta tayi ta kalli zarah suka had'a Ido, murmushin ba shiri miemie ta sakar mata, maimakon ta maida mata sai wani kallon rainin wayo data mata kana ta d'auke kanta.
Da mamaki miemie ke kallonta, dukda rashin hak'uri irin na miemie tsintar kanta tayi da mata uzuri ita har mamakin kanta takeji, da Dane da ta goge bakin yarinya.Ta6e baki tayi.
  Bata idasa tunaninta ba sukaji k'aran k'ofa.
Amatullah ne ta shigo Wanda ita kamanninta yafi nunawa da murad Dan mai martaba suka d'auko, sanye take da Pakistan rigar me A-shape Wanda ya wuce gwuiwa ta yafa babban gyale a kanta.
Ahankali ta fara takowa fuskarta na nuna alamun gargaba amma ta dake tareda had'e rai,tun karfun ta k'ariso hajjo tad'aga kai tamata wani irun mugun kallo kallo d'aya kana ta d'auke kai fuska a tamke tace.
"Stop there and Find your way out!"
D'agowa tayi ta dubeta.
"I said out!"ta maimaita muryarta na nuna alamun 6acin rai.
Batareda datace komaiba tajuya tafice.
Miemie sake baki tayi tana kallon ikon allah, kallon fuskokinsu tayi Dan taga yanayin dasuke ciki.
Sam alamun mai martaba da zarah bai nuna wata damuwa ko wani abuba.Had'a idanu sukayi da mai Martaba yamata alama irinta d'azu.
Maida kallonta tayi ga hajjo dake mata mugun kallo, kutt tahad'iye yawu kana takauda kai gefe.
Suna zaune shiru kowa na sak'a Abu a ranshi, babu Wanda ya kula abunci Wanda abun yabaiwa miemie mamaki, ita a gida duk Wanda yazo yaci nashi sannan tasaba ta wannan ya tsokani wannan gidansu very lively ta d'an yi murmushi a bayyani duka suka d'an kallota, murmushin takuma yi har hak'oranta suka bayyana.
Mintuna biyar tsakani saiga amatullah tashigo sanye da native wear complete Riga da skirt na atamfa, batareda sun dubeta tasamu guri ta zauna gefen zarah batareda ta kula kowa.
"I've warned you several times kidaina sanya kayan da ba na al'adarki ba,you're neither a foreigner nor pegan sannan ke ba jahila bace,idan na sake ganinki da 'yan iskan kayannan saikin gamu da 6acin raina,this should be the last warning."hajjo tafad'a tana kallon amatullah fuska a had'e.
Nodding kai tayi batare da ta dubi mahaifiyar tata ba.
Miemie dake zaune galala saitaga kamar da ita hajjo takeyi, wato itace Christian kuma batada tarbiya, gaba d'aya saitaji ranta ya dagule kasa hak'uri tayi tace.
"Am sorry to say but sanya wad'annan kayan bayana nufin kaiba musulmi bane,ae musulunci a zuciya yake,ko bikini mutum yasa yana yawo baikamata ayi judging d'insaba saboda ba'asan tsakaninsa da mahaliccin sa ba,balle ita Pakistan tasa Wanda nayi imani k'asar da ake sasu 75% musulmai ne kuma shi suke sawa,so outfits doesn't matter as far as akwai tsoron Allah."tafad'a boldly idanunta kan hajjo da itama takasa d'auke Ido a kanta.
Mai martaba d'an murmushi yayi zarah da amatullah kuwa mamaki ne k'arara a fuskarsu, yau wata ta challenging hajjo.

*****
Masha allah! Longest chappy so far...
Ehm... How far? Shin miemie na tsayawa a matsayinta kamar yadda aka kafa mata doka no tana wuce gona da iri?
Wani mataki hajjo yakamata ta d'auka akan miemie?
Vote,
Comment. And share

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now