In dedication to
Miemiebee 👄
*****
Tsaye yake a terrace idanunsa na kallon taurarin dake haska sararin samaniya iska mai dad'i yana ratsashi, lumshe idanu yayi kana ya bud'e yana nazarin wasu abubuwa, Sam kyakkyawar fuskarsa babu alamun fara'a sai tsantsar damuwa,yayi zurfi wurin tunani al'amuran rayuwa musamman a yanayin da Muke ciki a yanzu inda mutane suke abunda sukaga dama babu imani, tausayi dakuma tsoron Allah,tabbas rayuwa abar tsoroce babu shakka Allah na yin yadda yaso kuma a lokacin dayaga dama,ba'aja da al'amuransa saboda shike tsara wa bayinsa abunda yaga dama,akwai lokacin da yake jarabtan bayinsa ta hanyoyi da dama kuma lokacin da baiyi tsammani ba,allah ke bada mulki wa Wanda yaso Wanda koda kuwa mutum bayaso amma babu yadda ya iya saboda haka allah ya k'addara shikad'ai yasan dalilin yin hakan watak'ila jarabawace,mulki nada wuyar sha'ina Wanda akasarin Wanda suke da ita zuciyarsu ta bushe babu tsoron allah,babu alamun tausayi ko imani a cikinta,mulki nakai mutum ga halaka koda kuwa kakai zuciya nesa inhar ba allah bane ya tsareka,shiyasa bai k'aunar mulki ko kad'an, baita6a tunanin koda acikin mafarki zai zama mai jiran gado ba, yanada yayu maza hud'u shiya baita6a damuwa da al'amuran sarauta ba, ya ake gudanar da ita, me akeyi acikinta, baisan komai dangane da da itaba saboda bai rayu a cikin masarauta sosaeba,tun yana k'araminsa hutu ne kurum ke kawoshi gida,bai shak'u da mahaifiyarsa ba bare mahaifi,Mummy Aisha itace uwarsa saboda ita yasani saboda a hannunta ya tashi, ita kad'ai tasan halinshi dake kuma iya kwantar masa da hankali, bayan ga ita kuma sai d'an uwansa safwan, shine kad'ai amininsa Wanda yasan sirrinsa, amma gashi lokaci guda allah ya d'aukesu alokacinda yafi buk'atarsu, yau gashi a inda bai ta6a tsammanin zaijeba,yau babu mummy Aisha balle yaje gareta kozai rage rad'ad'in da zogin da zuciyarsa ke masa,yasan rayuwarsa nacikin hatsari amma ya danganar wa allah konai dan shine mai kariya,mutuwan 'yan uwansa akwai alamar tambaya shiyasa yakeson gano gaskiya da kansa,mahaifansa basusan komai gameda abunda yakeso da Wanda bayasoba, iyayene Wanda suke cusawa 'ya'yansu abunda sukaga dama kuma susa suyi dole, bama shi kad'aiba hatta ga 'yan uwanshi,shi mutum me saurin fushi da k'ulewa wanda yake fatan allah ya yaye masa, sannan yana jajircewa a bisa abunda zuciyarsa ke so, dawuya ake tank'warashi wanda hakanne ke jawo masa matsala gun iyayensa, ya maids hankakinsa kan business wanda shine abunda yafiso a duniya kuma yana d"aya daga cikin uzurin da iyayensa suka masa,sannan shi ba mutum bane ma'abocin bada hak'uri dakuma damuwa halin da wani ke ciki, shi Akan gaskiya ya tsaya koda kuwa wuk'a za'a samasa zai jajirce kan gaskiyarsa komai d'acinsa,yakanji haushi in mutane sun k'irasa da yareema,baiso Ana bashi wannan girman,yafiso a k'irashi da sunansa, hakan ne yasa daya a daga ciki ke k'iransa PMB saboda jin nauyin sunan, shid'inma babu yadda ya iya saboda tasa jarabawar kenan tun fil'azal.Ringing d'in wayarsa ce ya dawo dashi daga tunanin daya fad'a, kallon inda wayar take yayi batareda ya k'arisaba balle tsammanin d'auka harta tsinke,diri tafara Karo na biyu bai d'agaba,ana ukun ne ya k'arisa yasa hannu ya d'auka, jaleelah ya gani akan screen d'in.
Kallon sunan yayi ransa na k'una,ko kad'an baison ganin k'iranta amma yazama lallai ya d'aga saboda wasu dalilai da allah ne kurum ya sani,receiving yayi tareda k'arawa a kunne batare da niyar yin magana ba.
Daga can ta sauk'e ajiyar zuciya kana cikin damuwa tace.
"Thank goodness why yah murad Kasan tashin hankalin dana Shiga kuwa why didn't you picked any of my calls recently?" Ta tambaya cikeda damuwa.
"Tunda na amsaki yanzu ba damuwarki bane sanin dalilin daban amsaba d'azun wannan uzuri nane..."yabata amsa a tak'aice.
Sanin halinshi yasa bata kuma maganarba ta canza da cewa.
"Hope you arrived safely?"
"Stupid like always,da ban sauk'a lafiya ba I wouldn't have answered you from the first place..."
"Oops sorry, so how was the trip?"
Runtse idanu yayi cikeda jin haushin unreasonable questions d'inta.
"Yah Murad how was...
"Leelah stop! Meyasa common sense naki bai baki lokacin daya dace kiyi surutu, for havens sake let me be..."ya fad'a annoyingly
"Haba yah murad,ina laifin wanda ya damu dakai? Meye laifina dan na tambayi lafiyarka,kasan hankalina bazai ta6a kwankiya na inba na tabbatar da k'oshin lafiyarka ba, meye lafina dakake mun haka? Is it because I Love You?..."
"Hea please cut it out!" Ya katseta cikin 6acin rai.
"For goodness sake don't add to the headache I already have, I need to rest so don't call me again." Ding ya kashe tareda dafe kai,shi Sam baison fitina, wannan kalma shine weak point nasa a kullum, jaleelah 'yar uwarsace ta jini, yanasonta son 'yan uwantaka bayaga wannan bai ta6ajin sonta ta wani 6angareba, batun wannan lokacin ba yasan tana sonshi Wanda bata iya 6oyewa a ko ina saita bayyanshi, tawannan hanyar iyayensu suka fahimci abunda ke faruwa batareda tambayar ra'ayinashi ba suka yanke hukunci, babu yadda Dole ya amince sabids tahanyar da aka biyo masa babu yadda zai iya 6ullewa Dole ya amsa badan yanaso ba,yasha fahimtar da ita son 'yan uwan taka ne tsakaninsu saicewa take asalin so zai biyo bayan aure, dole yasa ya kyaleta shikuwa ya fawwala wa allah komai yamasa za6I mafi alkhairi a rayuwarsa.
Sam baijin haushin bak'ar maganganun dayake fad'a mata dan ta cancanci fiye da haka, baison mace ta kasance mai naci da rawar kai, shiyasa a rayuwarsa baison abunda yashafi mata coz mata matsalane ta kowani fanni.
Jin alamar shigowar SMS yayi,d'agowa yayi dan ganin waye
_am so sorry sweetheart I didn't mean to upset you,am terribly sorry my hands holding my ears,please accept my apology,I made something special for you tonight and I hope you'll enjoy it trust me it'll cheer you up (wink) take your time and rest tonight I Love You._ d'an guntun tsaki kafun yaji Sallamar sadi a bayanshi, juyawa yayi ya dubeshi fuskarsa ba yabo ba fallasa.
"Yalla6ai ga coffee d'in!"
"Thanks!"yafurta kana ya amsa.
"Sadi"ya k'ira sunansa bayan ya juya masa baya.
"Na'am yareemah"
"Murad!" Ya fad'a bayan yajuyo ya zuba masa ido.
Take bakinsa yafara rawa dan yasan yayi laifi
"A... Allah huci zuciyarka ranka... Mu... PMB."
Murad ya kallesa sosae kana yace
"Kaine mutum na farko dana yarda dashi a wannan gidan kuma nake tunanin duk abunda nake buk'ata a gareka zan samu, kafi kowa sanin halina harma nace fiye da iyayena,kawuce bawa aguna tunda dakai nake iya fad'awa matsalolina, na d'auka kaine mutum na farko dazaka daina k'irana da wannan sunan..."
"Ba Abu bane mai sauk'i yalla6ai... A naka ganin k'iranka da sunanka abune mai sauk'e amma a garemu abune mafi wahala saboda kaine zaka iya zama sarki a kowanni lokaci, koda kuwa jini d'aya garemi dole na baka wannan girman." Yafad'a kansa a k'asa.
Murad lumshe idanunsa wanda hakan nature'n sa ne.
"Idan kad'au keni da wannan mahimman cin inaga komai na umarcika dole kayi, so nace kadaina."
Bai bari yayi magana ba yakatsesa
"Sau nawa hakimi yazo duba abba bayan tafiyata?"
"Ehtoh! Shigowansa gidan nan sau biyu, na d'aya shine wanda nakeda tabbacin yazo gaida mai martaba, na biyu kuwa bai mai martaba yazo ganiba."
Da alamun tambaya yake kallonshi.
"Gun wa yazo?"
"Chief security!"
Shiru yayi yana nazari can yace yadubi agogon hannunsa kusan d'aya saura.
"Inaso kayi binciken maiya fitar dashi daga gidannan a wannan lokacin...Zaka iya tafiya!"
Yana kaiwa nan ya zuri wayoyinsa ya yafara sauk'owa sadi biye dashi.
Direct d'akinsa ya nufa, baiyi mamakin a bud'e yakeba coz yasan sadi ne,yana wangalewa yaji k'irjinsa ya buga runtsa Ido yana mamakin bugawan dayayi, yata6a jin wannan buguwan k'irjin shekarun dasuka wuce, kutsa kai yayi ciki bayan yakaranto addu'o'i,baidamu da kunna wutaba saboda haka yake ba mutum bane maison haske,fad'awa toilet yayi tareda sakar wa kansa shower abubuwa dayawa na gudana a ranshi. Baijimaba ya fito d'aure da towel yafad'a closet tareda sanya pajamas nasa yagama shirin kwanciya fitowa yayi yadawo cikin d'akin yanufi gado,gefen damansa ya kwanta bayan ya karanto addu'o'in tsari.
Sanyin AC ne yafara d'an damunsa saboda yanayin garin akwai sanyi,laluma blanket yayi bakin ta gefe, mamaki ne yakamasa jin blanket d'in a bud'e, sharewa yayi daboda a tunaninsa sadi ne ya ware masa saboda shi kad'ai ke shigar masa d'aki, ja yayi ya lullu6a.
Duk abunda yafaru bataji ko d'ayaba kasancewar headphones dake kunnenta tafara gyangyad'i, cikin gigin baccinta taji blanket nata ya kwaye, sake ja tayi ta rufa saita kuma ji an janye, wangale idanu tayi waje take taji tsoro ya shigeta, shikenan fatalwan yareema safwan ya shigo mata,cire headphones d'in tayi da k'arfi ta janye blanket d'in takuma ji an fiske.
K'ok'arin laluma socket na wuta saiji tayi ta cafki hannun mutum,tsikan jikinta ne ya tashi tareda sake damk'ewa tayi ta tabbar ko mutum ne, laushi da kuma d'umin dataji shiya tabbatar mata da abunda take zargi take wani mummunan tsoro yashigeta batasan sanda ta wawuro wani Abu ta kwad'a a inda taji alamun mutum ne tareda tsala wani ihu saida mansion d'in ya amsa daidai lokacin aka kunna switch na gidan take haske ya bayyana ako ina har cikin d'akin.
Murad dafe da kansa inda miemie ta kwad'a masa iPad batare da tasani ba, d'ayan hannunsa rik'eda bindiga ya k'ura mata idanu cikeda mamaki, atare suka mik'e daga kan gadon kowa na mamakin ganin d'an uwansa, dafarko yakusa tsorita ganin gashinta daya gama tukuikuyewa kana yarufe mata fuska, saida tasa hannu ta tattaroshi gefe tareda zaro masa idanu take ta zunduma ihu
"Wayyo jama'a kwarto!"miemie ta runtuma ihu.
Cikin 6acin rai ya nufota
"What the hell are you doing here? Who are you? how dare come into my room?"yafad'a angrily yana kallonta.
"What? It supposed to be other way round coz I was about to ask you this why are you in my room?" Itama ta tambaya cikin nuna isa da gadara tana nunasa da iPad d'in data kwad'a masa.
Da mugun mamaki yake kallonta, take yaji ransa ya harzuk'a, take yaji wani mugun tsanarta, who the hell did she think she is dazata shigo masa d'aki, za kwad'a masa Abu kana da k'irasa kwarto lallai ta janyo wa kanta.
"What the... " bai idasaba sukaji k'aran bud'e k'ofa take soldiers uku suka shigo rik'eda bindiga suna muzurai.
Nufan miemie sukayi gadan gadan ya dakatar dasu da hannu kafun ya matso gabanta dab dab, d'aga idanu tayi tana kallon kyakkyawar fuskarshi da babu komai sai 6acin rai da tsana k'arara.
"Tell me... Who sent you here?" Yafad'a tareda nad'o hannun rigarsa yana gyara rik'e bindigar idanunsa cikin nata.
Tunda miemie take a rayuwarta bata ta6a tsorita irin nayau ba, bindigogi hud'u duk a kanta,ta shiga ukunta, any a wannan ba 'yan fashi bane sukeson mata basaja, yaza'ayi ya shigo masauk'inta yayi claiming d'akinsa ne sannan yana tambayanta waya turota, take taji wani fitsari ya taso mata.
"Don't let me repeat myself stalker." Ta daka mata tsawa
Baki na rawa tafara
"What?...What are you...
"Who hired you to stalk on me answer me!"ya daka mata tsawa dasaida ta kusa sakin fitsarin a wando.
"Murad!"suka tsinkayi murya daga bakin k'ofa.
Atare suka maida dubansu ga hajjo dawasu 'yan mata guda biyu a bayanta Wanda d'aya zatayi shekaru ashirin d'ayar kuma sha bakwai.
******
Who's laughing already 😂😂😂 yau the whole miemie taji tsoro a Karon farko a rayuwarta, shin ya zamanta da PMB zai kasance bayan wannan al'amarin,kibiyoni danjin ya zata kaya.
Jeeddah love y'all ❤❤❤
VOUS LISEZ
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Roman d'amour"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...
