In dedication
Miemiebee 👄******
Da mamaki miemie ke kallonta, me hajjo take nufi da it was never her intention.
"Kowacce uwa zataso kasancewa tareda 'ya'yanta akp da yaushe amma banda ni..."ta share hawayenta zata mik'e miemie tayi saurin rik'o hannayen ta tare da girgiza mata kai.
"Ki sanar dani komai hajjo insha allah zan taimaka miki iya iyawata koda da addu'a ne...trust me."
Kallonta ta tayi nad'an dakiku tana nazari daga bisani tace.
"Banjin zaki iya taimakamun mariam saboda abunda nakeji yafi k'arfin tunaninki, ni kaina nayi k'ok'arin yaki da hakan amma nakasa..."
Still miemie tanace saita sanar da ita dan azahirin gaskiya ta fara kawo kokonto cikin lamarin.
" Akoda yaushe inason kasancewa da 'ya'yana nanuna musu soyayya, gata, kulawa dakuma tarbiya irin na iyaye kamar kowanni d'a amma lokaci d'aya komai yazo ya dagule Tsawon shekaru ashirin da biyu kenan duk sanda jinina ya kusantoni sainaji wani bak'in ciki a zuciyata maimakon farin ciki, zanyi kewarsu amma daga zaran sunzo kusa dani haushinsu ne yake mamaye mun zuciya batareda dalili ba, tsawon shekarun na nayi k'ok'arin yak'i da hakan na kasa,kuma duk sanda nayi yunkurin sanar da wani sainaji na kasa bazan iyaba sai yau allah yabani ikon sanar dake, banta6a zama da 'ya'yana naji damuwarsu ba kuma idan basumun abunda nakeso ba ji nake tamkar zan mutu suyi kawai koda kuwa hakan nada illa garesu,sainayi abun nakoma d'aki cikeda nadama,a kullum mai martaba yana k'ok'arin fahimtar dani illan hakan sainayi kamar zan gyara saikuma ya k'aru,Mariam banjin allah zai yafemun abunda na musu, gasiyar murad ne sauran basanan balle na nemi yafiyarsu..."
Wani mugun tausayinta ne ya mamaye miemie babu shakka abunda take zargi gaskiyane sihiri akaiwa hajjo wajen dasa mata k'iyayyar 'ya'yanta aranta, lallai hajjo abun tausayi tana buk'atar taimako.
"Shin kin ta6a kai kukanki ga Allah, ko an ta6a miki sauk'ar alqur'ani akan haka."
Hajjo ta dago takalleta fuskarta na nuna alamar confusion.
"Akullum ina addu'ar allah ya yayemun nafad'a miki banta6a sanar da kowa halin da nake ciki ba balle har na nemi taimakon wani."
"Insha allah komai zai wuce,kicigaba da addu'a har allah ya kawo miki mafita nima zan taimaka miki daidai iyawata, zaki zauna da 'ya'yanki kamar sauran iyaye kuma suma zasu yafe miki sukaciga da miko biyayya insha Allah..."tayi mata murmushi tana share mata hawaye.
Da mamakinta taga tarik'o mata hannu tana kallonta da murmushi mai ciwo a fuskarta.
"Bansan da wani baki zan baki hak'uri ba, tabbas kinada kyakkyawar zuciya ba kamar yadda na daukeki da farko ba,duk inda kika zauna farin ciki kike kawowa, nasan na miki ba dadaiba a baya dan..."
Da sauri miemie ta katseta wajen girgiza mata kai.
"Karki sa naji kunya wajen bani hak'uri,duk abunda ya faru ya Riga ya wuce kuma harga allah banta6a kallonki amatsayin wanda tamun laifi ba saidai ganin uwa tana scolding yarta, kinyi k'ok'arin fahimtar dani matsayi na kin limiting dina wajen aekata abunda basu dace ba tun farko zuwa na kinga kuwa ni zan gode miki, tun farko nasan kinada kyakkawar zuciya kema."
"Allah ya albarkaci rayuwarki yabaki farin ciki kamar yadda kika baiwa wasu."
"Ameen na gode."sukayiwa juna murmushi*******
Mintuna kusan biyar ta d'iba tana knocking a k'ofar d'akinsa ko alamar zuwa bud'ewa batajiba, harta hak'ura zata juya taji an amsa.
Doorknob din ta murd'a kana ta shiga, tsaye ta hangoshi wajen balcony na d'akin ya hard'e hannu a k'irji yana kallon sararin samaniya dagani kasan ransa a 6ace yake.
A hankali ta taka zuwa ciki, fridge d'in data gani a d'akin ta nufa tareda bud'ewa, juice taciro mai sanye ta tsiyaya acikin glass cup din data gani.
Gefensa ta tsaya tareda mik'a masa,bai amsaba itama bata fasa mik'a masa ba, can yad'ago yakalli fuskarta ta sakar masa murmushi, bai d'auke idanunsa a kantaba na seconds kana yasa hannu ya amsa tareda kauda kai ya mayar inda yake kallon d'azu, tana kallonsa sanda yakafa kai bai d'aukeba saida ya shanye tas ya lumshe Ido na mintuna bayan ya bud'e ya dubeta yayi smirking kad'an yace.
"Thanks..."
"You know what?"ta fad'a tana dariya
Juyawa yayi ya dubeta alamar yana sauraro.
"Actually this kind of behavior doesn't suit a man like you..."tafad'a teasingly
Still kallonta yake bai gane inda ta dosa ba.
"I know you've a good heart perhaps kullum cikin turmutsa fuska kace but I never expect this from you..."
Had'e gira yayi tareda kauda kai, miemie tayi dan dariya.
"Haha... My suspicious was right you get angry so easily Mr. Emperor."
"Get out... Banason magana"
"Karka 6ata bakinka cause am not going anywhere unless nayi abunda a kawoni."
Bai kulata sai girgiza kai da yayi irritatedly ya lumshe Ido.
"I know you feel like hiting me right now but the truth is always bitter... I knw sometimes things can be out of control but at least you can learn some skills that will help you to regain this control whenever you lose it..."
Juyowa yayi ya dubeta.
"What are you trying to say..."
"Finally kayi magana..."tayi dariya sillingly
Dan guntun tsaki yaja yace.
"Stop running around the bush and come straight to the point..."
"Bossy as always..."ta juya Ido tareda ta6e baki.
Kallonsa tayi taga idanunsa a kanta ya had'e girar sama da k'asa
"Oops sorry..."
"Idan bazaki fad'i abunda yakawoki I think I'd have to chase you away..."ya 6ata rai.
"Nooo you wont be able to do that emperor cause anan zan tsaya har sai ka dawo hankalinka kayi abunda ya dace."tafad'a cikeda shakiyanci.
"Really?"
"Of course..."
Juyawa yayi zai bargun tayi saurin rik'o hannunsa ta tsayar dashi, juyowa yayi ya kalli inda ta rik'e tayi saurin sakewa tareda daidai ta nutsuwarta tazo gabansa ta tsaya.
"Da bulala zaka d'auko?"
Runtsa ido yayi dan da alama haukatashi takeson yi.
"Okay okay...dont get irritated actually what you did to hajjo is not right..."tafad'a seriously
"And who're you to tell me what to do..."
"Cause bazan iya gani nayi shiru ba, emperor no matter what she did she's still your mother uwa uwace a kowani hali."
Baice komaiba sai kallonta da yakeyi hakan yabata damar cigaba da cewa.
"You've every right to be angry with her but Kun ta6a zama kun tambayeta dalilin dayasa take muku haka? Ko kunta6a sata cikin addu'ark? It's obvious duk abunda take bada son ranta takeba koda tana guje muku bai kamata ku kugujeta ba, ko kasan allah yana hukunta duk Wanda yayi sanadin fitar hawaye daga idon mahaifiyarshi koda kuwa itace batayi daidaiba, ko yanka fatan jikinku take bai kamata ka gaya mata magana hakaba, uwa tawuce wasa emperor you really need to apologize to her idan kanason ganin daidai..."tana fadar haka tayi tafiyata.
Binta yayi da kallo har tafice, lumshe Ido yayi tareda sakin d'an guntun murmushi, ji yaddq take masa fad'a wane itace uwar tashi, sha she's right dan shima saida yayi yafara dana sani he'd surely apologize to her but abunda ya sani bazaiyi abunda tace ba, all thanks to miemie a hankali yace.
"Thanks duckie..."
******
"I did exactly as you said doctor..."cewar ManSadi.
"I hope the snake isn't poisonous cause a yanzu banason komai ya sameta da ita zamuyi amfani gaba."
Ya girgiza kai
"I really hope Mai dafin ne doctor saboda ya bugawa 'yar kutumar ubaa Saran da gobe bazata sake yiwa wani mugunta ba."
Miemie tayi murmushin mugunta tace.
"Tukunna ManSadi ae mugu ba ae masa gaggawa, saita gane kurenta sannan...amma please don't tell emperor any of this..."
Sadisu yayi murmushi yana kallonta tareda girgiza kai.
"Kina tsammani duk abunda muke bai saniba?"
Miemie ta kallo sa da mamaki.
"Kamar yadda kike k'ok'arin protecting d'insa shima protecting d'inki yake?"
"Kamar ya?"
"Well I Won't tell saboda karki karaya in fact emperor hired a secret agent to be spying on your every move so kings yasan duk wasu plans dakike shiryawa..."
Sosae miemie tayi mamaki, dama all this while yasan abunda take shiryawa but yayi shiru kamar bai saniba.
"Gaskiya soyayyarku na burgeni doctor...kowa lafiyar dan uwan sa yafiye masa komai dukda yawan fad'an ku"
Wani mugun harara ta banka masa, yasa dariya.
"You won't admit it so fast but you guys are blindly in love with each other..."yayi saurin barin gun dan yasan k'arshenta miemie zata kai hannu.
"You are crazy sadisu,allah ya tsareni da 6ata lokaci abanza,I would never fall for anyone in this world not now not ever duk abunda nake saboda allah ne"tafad'a ranta na tafasa dan ta tsani amata maganan soyayya musamman yadda sadisu ke had'ata da emperor saitaji zuciyarta nashiga wani hali yana bugawa.******
Kwance take tanajin conversations na mermu inda take cewa.
"Am really scared right now... Inaga kamar am fara ganomu..."
"Wallahi ba karya nakeba idan ba hakaba how many traps have we set for PMB amma yana tsallakewa, somehow someone is really ruining our plans batareda mun sani ba.."
Bataji abunda aka fad'a acan mermu muryata na rawa tace
"Kasan bazan maka k'aryaba but wallahi naga maciji a d'akina a k'asan pillow kamar yadda nasawa doctor allah ya taimaka nayi gaggawan kashewa dan yanzu yamun illa amma ban bari kowa ya saniba...kaga kuwa dole naji tsoro."
Bayan d'an shiru tace.
"Okay... I'd do as you said but right now banda suspect saina bincika duk abunda nasani zanyi gaggawar sanar dakai asan abunyi dan ni a tsorace nake..."
Daganan bata sake jin abunda aka ceba, miemie tayi murmushin mugunta.
A wunin ranar miemie ta tsoritar da mermu bila adadin batare da ta gane ba, a tsorace ta wuni Wanda ita kanta mermu tasan miemie tasan ba lafiyarta ba.
Da misalin k'arfe Tara na dare miemie ta k'ira mermu har d'akinta.
Da sallama tashigo with innocent face kamar kullum ta sakarwa miemie murmushi.
"Doctor sannu da hutawa..."
"Sannu da aeki mermu."
"You called for me ko kina buk'atan wani abune?"tafad'a with smily face.
Miemie ta girgiza kai bayan ta mayar mata da murmushin.
"A'ah... Kawai inason tambayarki abune"
"Toh allah sa na sani..."
Miemie ta mik'a mata cup d'in coffee d'aya itama tad'auki d'aya, babu musu mermu ta amsa tareda mata godiya.
"Ko kinsan wani Abu gameda zuwan maciji nan d'akin?"
Da sauri mermu ta kallo miemie.
"Kamar ya kenan."
"Noo karkiji tsoro sha coffee d'inki..."tafad'a tana murmushi.
A tsorace mermu takai cup d'in baki miemie taxi saurin turewa mug d'in ya fad'i k'asa a tare suka mik'e tsaye.
Take jikin mermu yafara rawa sakamakon abunda tagani a k'asa (Poisonous lizard d'in data sawa PMB a coffee).
Arazane tad'ago miemie ta d'aga hannu ta sharara mata Mari saida taga w******
Vote, comment. And share

ESTÁS LEYENDO
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romance"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...