chapter 25

1.8K 117 17
                                        

SAUYIN RAYUWA! 👩

Written by
H. Jeeddher

In dedication to
Miemiebee 👄

   *****

   "Baza'a badaba sainaji k'arfi..."tafad'a tareda ra6awa ta gefenshi zata wuci.
"Kinsan Allah miemie kifita idona...
"Bud'e idon mugani...!"ta lek'a fuskarshi.
Haushi gaba d'aya ya gama cika ammar,baison biye mata dan yasan sarai fad'a take nema fad'an ma kuwa dambe,bai biyemata yanzu acewarsa da da yanzu ba d'aya bane girma yazo,shekaru sha shida harda d'auri amma miemie Sam babu hankali,gashi maid'an sa ta nutsun bai nan abun nata k'aruwa yake.
Ra6awa yayi ta gefenta zai wuce,cije yatsa tayi dan bataso hakan ba,samasa k'afa tayi tayi gaba tareda buge kansa jikin bango.
  Dariya tafashe dashi tana tafe hannu.Da sauri ta d'ago wayarta tareda video'n
"Hehehe! Su d'an gayu an kife...yanzu zanga yadda zakayi burga aradu instagram zan dire..." Tafad'a cikeda mugunta tana dariya.
  Wani mugun kallo yabita dashi cikeda 6acin rai,saida Tagama d'aukar komai,ganin fa dagaske take zata posting online cikin zafin nama yasa hannu zai amsa amma ina tariga ta d'aura, k'ar6a yakeson yi ya deleting tun kafun a gani amma inaaa k'arfin miemie ba d'aya da nashiba,naushinsa tayi a k'afa tafice a guje tana dariya,dama abunda takeso kenan wasan banza.
  Ammar binta yafara ahankali yana mata gargad'in ta ajiye masa phone kafun hauka yasa ta fasa,itakua sai dariya take tana murgud'a mai d'uwawu,tun yana binta da lallami har abun ya ci tura,a zuciya yabita zai kar6a tanufi k'ofa da gudu.

   Bummm taci Karo da mutum wayoyin hannunta duka suka cillu sama tareda fad'i sai tass a k'asa.
  Baki ta wangale batare da ta dubi mutumin data bugeba.
  "Kutumar uban can... Aradun Allah bazan yadda ba ya fashe sai an biya..."tafad'a tareda nufan gurin da wayoyin suka fad'i tana dubawa, unfortunately natane ya fashe na ammar babu abunda ya sameshi.
  "Jakar ubancan..." Talailayo ashar tareda mik'ewa don balbale Wanda yayi sanadin.
  "Aradun....
Baki ta wangale tana kallon wata kyakkyawar budurwa gabanta ak'alla zata bata shekaru shida,zatakai shekaru 22 a haife.kyakkyawace ta gaske Dan suna mugun mama da miemie saidai miemie tanuna mata haske,sanye take da abaya ta rolling veil d'in a kanta.

  Baki da hanci da Ido miemie tasake tana kallonta Dan azahirin gaskiya bata ganeta ba

Ups! Gambar ini tidak mengikuti Pedoman Konten kami. Untuk melanjutkan publikasi, hapuslah gambar ini atau unggah gambar lain.

  Baki da hanci da Ido miemie tasake tana kallonta Dan azahirin gaskiya bata ganeta ba.
  Itama ba yabo ba fallasa take kallon miemie'n dan abunda tayi yanzu yabata haushi da mamaki atare,instead tabata hak'urin abunda ta aekata,rather gata sai lailayo ashar take tana masifa Sannan data ganta babu zancen bada hak'uri ta tsaya tamkar statue idanunta k'ur a kanta,jitayi gaba d'aya miemie'n ta tsanemata.
  "Oyoyo adda abeedah!"Cewar ammar astonishingly tareda amsar trolley'n hannunta
   Murmushi ta sakar masa dan bamai yawan magana bace ita,ga 6acin ran da miemie ta k'unsa mata.
"Auuu dama abeedah ce tagirma haka!"cewar miemie tana rik'e ha6a
Da mamaki abeedah ta d'ago tana kallonta.
Harara ammar ya bankawa miemie yana mata Ido. 
"Kinji kunya wallahi! Ko ina saikin Nina halinki,at least saiki dubi girman datake bamu..."Ammar yafad'a tamkar ya mangareta.
  Wani harara miemie ta banka masa.
"Ni banga mutum anan ba!" Tafad'a tareda kauda kai tana dube dube.
  Baki abeedah tasake tana kallonta,lallai wannar yarinyar tacika tambatsetsiyan marar kunya.
"You must be very stupid...
"Kai dallah rufamun baki idiot...katambayi mutum in yayi sallama..." Tafad'a tareda kauda kai.
Abeedah haryanzu bakinta a sake tana kallon miemie
  "Adda abeedah don't mind her please batada lafiyane...
"Kutumar uban Wanda yace maka banida lafiya...?" Ta banka masa harara.
Ko kallo bata isheshiba yajanyo akwatin sai a sannan tayi magana cikin muryarta na 'yan matanci.
  "Ammm! Ammy bari kawai zanshigo dashi jeka amso na hannun mummy tana sallamar driver!" Tak'arisa tanai masa murmushi.
Ammar ya dubi miemie yace
"Fav twin help her bari na amso na mummy!"
"Yaushe na zama 'yar dako?" Ta banka mail harara.
  "Ni gun mummy'na zani kuma aradun Allah mutum yabiyani wayana...
  Tafad'a tareda tattare burmemen sket d'inta taruga a guje gun mummy.
  Da kallo abeedah tabita,tasan miemie da rashin iya magana musamman was ita amma batayi tunanin rashin kunyarta takai hakaba, iya tsawon rayuwarta basu ta6a shiri da miemie ba, kwata kwata basa zama inuwa d'aya, ita mutun ci wacce magana Sam bata dametaba,saita wuni daga um sai um um,kwata kwata bata shiga sabgar mutane sai an shiga tata,batason acika yawan suruta Wanda duk miemie ta Tara, they're opposite to each other,kwalliya da d'aukar pics sai chatting sune abokanta,She's so simple,akaf 'yan gidan sunfi shiri da khaleel dan shine sa'anta.

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang