In dedication to
Miemiebee 👄*******
Kallonta yayi karo na biyu ta mirror'n mota yana tunanin ya tafi koya taimaketa...zuciyar imani ta bashi amsa daya taimaka mata.Tun fitowarsa daga cikin asibiti ya lura da ita tanata faman tada motarta tak'i tashi,murmushi yayi yana mamakin yadda Sam k'arfe bai kar6eta ba,kullum da matsalar datake 6allowa, ta gefenta ya wuce amma ko kallon inda yake batayi shima bai kulata ba ya shige tasa motar, yadda ta zage a dole gyara take yasashi dariyar daya jima baiyi irinta ba, yana ganin sanda ta sungumi zabgegiyar dutse tana buga kan battery.
Saida ya gama mai isarsa kana ya Sauko daga motar tareda nufan inda take tsaye kayan Allah sarki tarik'e hannu a k'ugu tareda k'urawa engine Ido helplessly.
K'ariso wa yayi batareda ya kalli inda take ba ya shiga driver seat yana gwada gwada tayarwa, girgiza kai yayi tareda dan guntun murmushi yafito yana dubanta wacce ta tsaya kamar statue tareda zuba masa fararen idanunta, Sam fuskarta ba kamar yadda yasaba ganiba, yarasa meyasa kwana biyu ta sauya kodan gaishesa da da take yanzu tadaina, dukda bai amsawa wani sa'in amma yaji ba dad'i... Kwata kwata baison yadda ta sauya sai guiltiness yafara shigarsa.
"Sannu da k'ok'ari genius mechanic...matsalar ba d'aga nan bane stop wasting your time...well inason motarnan sosae ban shirya rasata ba I could have give you a ride."yafad'a bayan ya rufe bonnet din motar yana kallonta.
"Thank you genius insulter...But I don't remember asking for your help either."tafad'a in a sarcasm.
Zololo ya tsaya yana kallonta... Yaushe wuyanta yayi kauri haka, maganinsa daya bata fuska kwana biyu ta rainashi.
"Well...that's your problem anyway, zanga inda rashin kunyar zata kaiki."
Bata kulashi ba illa nufan motar tayi tareda sake bud'e bonnet din.
Dariya taso bashi ya masge tareda nad'e hannu ya zuba mata ido.
Yana kallo ta ta6a nan ta ta6a can harta ta6o wani abunda ya 6allo hayaki, kan kace me guri ya gauraye dahayaki fuskarta tayi bak'i k'irin, me maheer zaiyi inba dariya ba...
Ma aekatan dake kusa suka tattaso suna tambayar lafiya maheer yace musu ba damuwa suje kawai.
Ya dubi meelah data tsaya kamar Zombie babu abunda kake gani da haske a fuska din bacin idanunta, sake tuntsurewa yayi da dariya harda rike ciki.
Mamaki, farin ciki da annashuwa su suka rufe meelah lokaci guda, bata damu da wa ita yake yiwa daria ba abunda tasani shine dalilinta yayi dariyar daya jima baiyi irinta ba, kwana biyu daya fara sakar mata fuska ba k'aramin jin dad'i tayiba,dukda bawani maganan kirki suke ba amma hakan na mata dadi sosae,the more tana tareda dashi the more tana sake kaunarsa, duk sanda ta tuno he's engage saitaji ba dadi,ayau dataga miemie ta dawo gaba d'aya farin cikinta ya koma ciki saboda tasan yanzu zai maida hankalinsa kan abar sonsa, shiyasa ta yanke hukuncin fita daga sabgarsa ko hakan zai rage abunda takeji a zuciyarta amma a yadda ta fahimta yanzu komai zatayi bazata iya cire shi a ranta ba,sonsa a jininta yake, cireshi a ranta kamar cire numfashin ta ne.
Tafa hahannun dayayi ne ya fasgar da ita,mamakin ganinsa tayi dab da ita dan batasan sanda ya k'araso ba.
Hade fuska yayi kamar bashi yagama cisgar dariya ba yace.
"Poor girl...see what you've done to yourself rashin kunyarki taja miki,yanzu sai a k'ira motar zoo ta d'aukeki ko."
Sam bataji zafin maganar sa ba illa sauk'e kai datayi k'asa tareda Jan gyalenta ta rufe rabin fuskarta.
Batasan ya koma mota ba saijin muryarsa tayi ta mik'o hannunta.
D'aga kai tayi ta dubeshi ba yabo ba fallasa da roban ruwa a hannunshi.
Zuba mata yayi ta wanke face dinta tas kana ya mik'a mata handkerchief ta goge face nata,yau maheer ya gwada mata good side dinsa da da saidai taga yanama wasu kirki banda ita,yau kirkin kanta ya fad'a.
Godiya tamasa baikulata yanufi motarsa.
Kallo gabishi dashi tana murmushi...maheer ba haka yakewa mutane ba to meyasa ita yake mata haka.
Juyawa tayi ga motarta tareda zufe ko ina tad'auki jakarta da abubuwan amfaninta ta kulle motar ta nufin zuwa ta shiga adaidaita.
Tafiya tafara taji muryar Dr. Adeel gefenta,juyowa tayi ta dubeshi tareda mayar masa murmushin dayake aeka mata.
"Seems like motar taki ta samu matsala."
"Ba kama bace hakane... Kasan halin k'arfe."ta k'arishe da fara'a.
"Amma motar nan ni tayiwa adalci saboda zan samu daman zuwa naga gidanku."
Sam batason binshi saboda zaicikata da zancen soyayyar da bataso, tana ganin mutuncinshi shiyasa bata tsuga mishi rashin mutunci ba.
"Aah... Daka bari wallahi naga hanyarmu ba d'ayaba karna 6ata maka lokaci."
"Haba jameelah... Ae kinfi k'arfin kowani uzuri na koda kuwa k'iran uwace."
Aranta taji ji dan rainin wayo tsabaragen bakasan darajar uwarka ba budurwa tafita,da shegen kayinsa kamar filin ball kamar shine ubanta daya rada mata jameelah, tarasa wani irin nacin tsiya gareshi, sam baisan NO ba.
"Yelwa zance daganan kaga maidaka baya zanyi dan Allah kaje kawai."ta kasa daurewa har sanda ta tsula mishi k'arya ta kuma rok'eshi gaba d'aya ya isheta.
Maheer dake cikin mota yana jiran meelah baiganta ba, tsaki yaja tareda kallon mirror, hangota yayi tsaye da Dr. Adeel sai murmushi sukema juna.
Wata doguwar tsaki yaja Wanda shikansa baisan fitarsa ba, sarai yagane take taken dan banzan adeel dinnan, haka kawai yaji ransa yasoma 6aci (wata sabuwa kunta6a ganin ran maheer ya 6aci?) Tada motar yayi tareda cireta inda aka tanadar dominsa cikin cin rai, yadda yayi reverse din shiga tankad'o hankalin meelah da adeel kanshi.
Meelah ta dubi adeel tace
"Kagama yaa Maheer nake jira yayi reverse."
Baisamu damar bata amsaba saboda nufo kansa da maheer yayi da mota dasauri yaja gefe a tsorace, bashi kadaiba har meelah ta tsorita.
Daidai gabansu ya tsaya tareda zuge glass ya tamke fuska yace
"Get in."
Ba musu ta zagaya ko kallon adeel daya sake baki baiyi ba ya d'aga glass dinshi tareda fincikar motar batare da ta k'arisa rufe murfin ba.
Baiceda ita uffan itama batace komai ba harsaida suka fita daga harabar asibitin batareda ya dubeta ba yace.
"Soyayya kikazoyi anan ko aeki?"
Sosae tambayarsa ta bata mamaki, Aranta face meye gaminsa da sabgata, sannan wani irin tambayane wai soyayya nazo ko aeki, kai din ae soyayya kazo yi tunda kuna tareda miemie, kodan kana gadarar asibitin nakune... Mtsw
Wani burkin d'aya jane saida cikinta ya bada kululu.
Kallota yayi yace
"Maimaita abunda kikace."
Sai a sannan ta lura maganar datayi a zuci ya fito fili, nan danan cikinta ya d'uri ruwa sai muzurai take.
"Yaushe nazama sa'anki iyee? Kinsan mintuna nawa nayi ina jiranki huh? Dan tsabar rainin wayo soyayyarki kikaje kinasha dan kin rainani, wato ga driver'n ki na jira."
Aranta tace masifar ma ko iyawa baiyi ba a zahiri kuma tamke fuska tayi itama tayi tace
"Blame yourself for that... Bacewa kayi you love your car bakaso ta lalaci dan haka zaka bani ride ba saboda ni Allah ya horemun bakin jinin k'arfe."ta k'arishe tana yar harararsa.
Tsintar muryarta yayi tana cewa
"Am sorry about earlier and thanks for the ride..."
"That sounds like a good girl."baijira amsartaba yaja DC dinsa yayi gaba.
Bin motar tayi da harara kamar yana kallonta,kana tanufi cikin gida.
KAMU SEDANG MEMBACA
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romansa"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...