If I believe in love and you believe in love, then we can be in love somehow, if you want the best for us like I want the best for us then we gotta learn the trust right now.
~Trust~
~*~*~*
Mamaki,kunya,haushi duk ya cikasa a lokaci daya,Meh take nufi? Lallai yarinyar nan bata da hankali.
hajja data idar da sallah tadubeshi. "Malam lafiya kake binta da harara? K'arya tayine? Ganin ka korasu kai bakayi sallah'n bane yasa ta tambaya ko mensuration kakeyi!"
Meh hajja take nufi? Wato bataga rashin kunyar da miemie tagama yi masa yanzuba ta tsaya tanai masa masifa,wani k'ululun bak'in cikine ya tokaresa harzai tanka yatuna gargad'in da mama tai masa yayi calming kansa.
Bayan ta idar da addu'a yadubeta ya had'e girar sama da k'asa "Hajja gunki nazo zamuyi magana."
"Nikuma ban shirya magana dakai ba!"tabashi amsa kai tsaye.
Danne zuciyarsa yayi tareda runtsa ido,shi da badan mama ba baiga dalilin dazaisa yabiye mata tana masa yadda ranta yaga damaba,dole hak'uri zaibata kamar yadda mama ta umarceshi,kamar yadda takeda hakki akan yaranannan shima yana dashi a matsayinsa yayansu.
Tsuke bakinsa yayi yana kallonta harta gama tattare tattarenta zata shige ciki ya daure yace"Hajja kiyi hak'uri da abunda yafaru d'azu!" Yafad'a tareda runtsa ido ya kauda kai.
Da baya tadawo ta kallesa "Ayho! Saiyanzu kasan da zancen girma,d'azu dakazo katsayamun akai kana yayyafamin ruwan rashin kunya bakasan dashiba sai yanzu? yanzu kasan abunda yadace?"
"Magana ya riga ya k'are tunda har nabaki hak'uri ko? Ki yarda dani hajja tunda kinsan ba dad'in baki zanzo namiki ba."
"Toh anki hak'uran! Nasan ka sarai aleeyu bayin kanka bane kabani hak'urin! maman sadeeq ne ta saka,dan haka Karka 6atamun rai da lokaci ka tattara sayyado dinka kabar mun gida."
Kamar ya tashi ya tafi dan jiyayi kamar ya mangareta dan tsabar haushi yadai daure yace.
"Haba hajja! Hak'uri fa nazo baki ba fad'a nazo ne maba,shikenan! Inakan twins ne namiki alk'awari bazan sake koda d'aga musu muryaba bare harta kai ga duka kinji?"
"Do Allah rufamun baki! Aleeyu nafa sanka,baza kazo nan kana mun dad'in baki ba,kuma nasan abu ne a ranka shiyasa kake wani sussunne kai kana ladabin kwad'i nasan ba har cikin ranka bane!"
Dafe kai yayi dan masifarta yafara sa mishi ciwon kai,rasama abun cewa yayi dan maganar tafara ishar shi,daya tuna abunda yakawoshi saiya matse yadubeta tareda k'ak'alo murmushin dole yace"Habaaa hajjana kiyi hak'uri mana,yanzufa kika gama cewa kin sanni kinsan halina,da dane har zanzo ina baki hak'uri kuma na miki alk'awari,kema kinsan da saidai kawai nayi abunda naga dama babu Wanda ya isa yahanani." Yafad'a scoffingly cikeda haushi amma murmushi ne a fuskarsa.
"Uhuuum! Hardawani hajjana dan kanaso ka yaudareni Zaka aekata abunda yafi hakama hydar..."
"Ohhh! Please hajja kiyarda dani."Saida tad'anyi jimm
Yace."Alk'awari nayi kisa ranki a inuwa babu abunda zan musu!"
"Yanzu naji zance! Alk'awari kayane ka d'auka aleeyu karnaji wani zanci kana jina? Karaje wannar cin zuciya da fad'in rai dan babu inda zata kaika"
"Naji hajja zauna toh muyi magana."
"Ko kaifa umm! Ka zauna kayi magana ta fahimta da mutane kanad'an murmushin nan bakaji dad'iba amma saika had'e rai ko bomb nan yaganka ya barka don tsabar bak'in hali da masifa har gudunka akeyi"
"Yanzu dai zauna kiji!"
Zama tayi akan kujera kana tace "Ina sauraronka aleeyu mazan fama anbuga dakai anbarka"
BINABASA MO ANG
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romance"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...
