chapter 42

1.6K 142 22
                                        

In dedication to
Miemiebee 👄

*****
Firgice, tashin hankali da tsoro suka ziyarci zuciyar miemie alokacin da idanunta suka sauk'a kan sak'on. Goge idonta tayi ko su suke mata k'arya, bud'ewa tayi tasake dubawa idanuta yakuma ganin same Abu.
Tohfa! Ana wata ga wata, wake threatening rayuwarta akan aekinta? Meye dalili? Duk batada amsa.
Ji tayi an dafa mata baya da sauri ta juyo a firgece.
"Lafiya Dr?"mermu ta tambaya tana mata kallon tuhuma.
Narai narai idanunta sukayi tanaso tafad'awa mermu tasakejin k'aran sak'o.
Da sauri ta duba idanunta na narai narai.
_kar ki kuskura ki sanar da kowa dan yin haka barazana ce ga rayuwarki._
Da sauri miemie ta d'ago tana kallon mermu da har alokacin tana mata kallon tuhuma, murmushi ta k'ak'alo bayan ta bud'e hak'ora,shin tagaya mata gaskiya ko a'ah, tsintar kanta tayi da cewa.
"Am fine."
"Banga alama ba."tabata amsa a tak'aice.
Miemie da gaba d'aya ta gama daburce wa.
"Me... Mekika...ga...gani?"
"Nakai minti biyu ina miki magana gaba d'aya hankalinki yayi gaba, banyi tsammani kinji kalma d'aya Dana fad'a saida na ta6aki... Tell me what's going on with you?"
Anzo gurin, a rayuwar miemie bata iya k'aryaba, me zatacewa mermu? Ita bamai tsoro da shakka bace amma abunda ya bata mamaki shine duk yadda akayi Wanda ya turo mata sak'on yasan d'uriyarta, take maganan SG ya fad'o mata a rai inda yake cewa _do not trust anybody_,amma ae ta yarda da mermu a d'an zaman dasukayi, she's so simple and trustworthy.girgiza kai tayi _no miemie don't tell her, you were warned not to tell anyone,wannan akan rayuwarki ne._
"Yanzu yah faruk yamun SMS mama ba lafiya."tayi k'arya.
"Subhanallahi, allah ya bata lafiya."
"Ameen" ta fad'a nervously.

*****
Da shigarta d'aki ta zauna bakin gado kwakwalwarta gaba d'aya ya cunkushe, bata ta6a tsintar kanta a wannan halin ba, meke faruwa? Wayake barazana ga rayuwarta? A wani dalili? Duk batada amsarsu, d'an tunani tayi da sauri ta ware idanu dan tuna abuda mai martaba yace mata da safe _karki shiga abunda bai shafeki ba dan tseratar da rayuwarki daga shiga fitina ko hatsari?_
"Wannan na nufin akwai wani 6oyayyen al'amari gameda gidannan,to meyasa zaishafeni?"tafara nazari.
_miemie you're here to cure the king, you've nothing to do with their royalty stuff, an d'aukokine saboda wannan dalilin, you believe in allah kuma you believe in yourself kinada tabbacin shi zai taimakeki, you're fearless da allah kika dogara,ke mutum ce maison ganin kin cimma burinki akan aekinki,karkiji tsoron kowa ki aewatar da abun alkairin daya kawoki, so forget about the the stalker bai isa yamiki abunda allah bai k'addara ba._
  Sharewa tayi tajawo wayarta ta k'ira mama, bugu d'aya ta d'aga.
"Assalamu alaikum hello mama."
Mama kasa 6oye mamakinta tayi ta amsa.
"Wa'alaikumus salam miemie kece?"
Dariya miemie tayi tace
"Mekika gani mama?"
"Yau kece da sallama?"
"Iyi mana ae dama inayi,tukunna ma ina wuni, ya gida ya kowa da kowa."tafad'a tana murmushi.
Mama runtse idanunta tayi tana hamdala a ranta cikeda farin cikin addu'ar data jima tanayi ya fara kar6uwa, yau ta k'irga duk sanda sukayi waya saita gaisheta.
Karo na farko da miemie tafara sensible maganganu tana tambayar mama muhimmancin alk'awari.
  Da mamakin furucinta mama tace.
"Miemie are you okay?"
Dariya miemie tayi tace
"Mama am fine, kawai inason Sabine."
"Kin tabbata?"
"Eyi mana."
Mama ta numfasa kana tafara da cewacewa
" Cika alkawari yana daya daga cikin muhimman al'umuran rayuwa da ya doru a wuyan mutum. Dabi'ar mutum ne ko da wane addini yake bi ya ji bacin rai idan ya karya alkawari, murna da farin ciki kuma sukan lullube shi idan har ya cika alkawarinsa, miemie Cika alkawari yana da muhimmanci ga wanda yake kaunar ya zauna a cikin jama'a, shi ne kuma tushen farin cikin zaman tare da ci gaba da cin nasara.
  Miemie tayi shiru tana sauraron mama.
"Kina jina?"
"Inaji mama..."tabata amsa jikinta duk yayi sanyi.
  " Idan har aka kulla alkawari da kiyaye shi a bisa asasin imani da halayyar kwarai da karamci, to shi ne mafi dorewa kuma mafi karfi. Mutunci ya wajabta cika alkawari ko da kuwa na baki ne wanda aka kulla tsakanin bangarori biyu, ko da kuwa babu wata rubutacciyar hujja. Karya alkawari yana jawo ficewa daga da'irar daraja da mutunci. Ketare haddin wa'adin da aka yi alkawari shi ma rashin mutunci ne...kinga cika alk'awari nada matuk'ar amfani."ta dakata.
"Mama Wanda ya karya alk'awari fa?"
"Duk wanda ke kauce hanya madaidaiciya ta hanyar karya alkawari cikin sauki, to yana shuka kangarewa ne da kyama a zukatan wasu. Sannu-sannu mai karya alkawari zai kunyata ya yi kokarin nade tabarmar kunyarsa ta hanyar kame-kamen dalilai da warware tukkar da ya yi, har daga karshe mutane su gane cewa dai shi dama mutum ne batacce, munafuki.
Babu shakka karya alkawari yana daga cikin abubuwa mafiya saurin kawo tangarda a al'umma da raunana dangantaka a tsakanin jama'a. Tabbatacce ne al'ummar da ke cike da gardandami da rashin yarda za ta sukurkuce a tsarin zaman jama'arta, kuma sakamakon haka mutane ba  taba yarda su amince da kowa ba hatta danginsu na kusa.acikin al-Qur'ani mai girma cikin suratul muminoon aya ta takwas allah (SWA) bayyana  masu imani da cewa _wadanda su masu kiyaye amanarsuce da alkawarorinsu_ kinga kenan alk'awari na cikin rukunan imani, wannan karya alk'awari na cikin alamomin munafuki."
  Shiru miemie tayi tana nazarin kalamun mama wata zuciya na k'arfafa mata gwuiwa Akan burinta.
"Zaki iya tuna hadisin dake magana akan munafiki?."
Girgiza kai miemie tayi kamar tana gabanta kana tace
  "Inda manzon allah yake cemana akwai abubuwa hud'u duk Wanda yakeda su to munafuki ne. Idan kuwa yana daga cikinsu to yana munafurci harsai ya rabu da shi, wato idan yayi magana saiya tsuuuga k'arya, idan yayi yarjejeniya sai ya sa6a, idan yayi alk'awari sai ya karya, idan kuma yayi husuma sai ya zak'e, ina duk bana ciki ko mama?"tafad'a sounding serious
  "Bakya ko d'aya mariam...kuma bana fatar ki fara a yanzu, cikin surar isra'ila aya ta 224 allah na cewa _kuma ku cika alk'awari, lalle alk'awari abun tambayane a gareshi._kinga allah zaiyi tambaya ranar k'iyama, shiyasa tun farko kar muyi alk'awari akan abunda munsan bazamu iyaba."
  Shiru miemie tayi tana tuna maganar da tayiwa Mai martaba a d'azu.
_"mariam zanso kizama mai juriya da hak'uri sannan kid'auke Ido akan abunda ke faruwa a gidannan, yin hakan shine zaman lafiyarki, idan kikace zaki tafi zanyi matuk'ar bak'in ciki saboda kece mutum na k'arshe Dana yarda zaki Samar mun lafiya..."_
Ba tare da tunanin komaiba miemie tayi murmushi tace.
_"Abba indai tanine karka samu damuwa, ALK'AWARI na dauka wajen ganin na Samar maka lafiya dadai iyawata,mutuwace kurum zai hanani aewatar da k'udirina akanka wannan alk'awari ne,abunda ke cikin gidan nan bazaisa na gujeka ba, Sam ni banida rik'o kuma banasa komai a raina, komai mai wuce wane."_
"Mariam!"taji mama ta k'irata.
"Na.. Naam."
"Akwai abunda ke faruwane, jikina na bani akwai abunda ke faruwa dake dan ba haka nasan miemie na ba."
  "Mama zuwana na nan yasa *SAUYIN RAYUWA* yafara zuwarmun a yanzu,kici gaba damun addu'a Sanya kisanya min albarka harna cimma burin dake gabana."
Mama da farin ciki yagama dabaibayeta tana hamdala a cikin ranta, lallai tafiyar miemie alk'airi ce tunda gashi *SAUYIN RAYUWA* yafara zuwa mata.
"Kullum kina cikin addu'ata Mariam, albarka kuma kullum muna cikin samiki ita."
"Nagode mama, allah yabar mana ku."
Sosae mama taji dad'in hirarsu ayau da miemie dukda har yanzu tana saka shirme amma sensible magana yafi yawa,ranar kasa 6oye farin cikinta tayi ta sanaf wa baba komai.
Bayan sun gama waya da mama lokacin maheer ya k'irata daidai yafito daga gida zai shiga mota don zuwa asibiti.a lokacin k'arfe 9 ta gota.
Sallama ta masa kafun ta k'ara da yarda tasaba.
"Alooo my pladin."
"Princess how are you? hope dai kina cikin k'oshin lafiya? inace babu mai ta6amun ke? are you alright over there? Answer me."ya tsaya gefen motar sounding worried
Dariya tayi
"Duk tambayar nan wanne d'aya zan amsa, am absolutely fine Dr. Shareef."tafad'a tana dariya.
Tanajin sanda ya sauk'e numfashi.
"Are you sure? I don't seem to believe you,"
"Meka gani yah maheer?"ta tambaya.
"Your voice sounds different princess, ba haka kika saba magana ba, tell me is something bothering you?"
"Not at all yah maheer, am fine trust me."
"You are not princess, are you tired of the contract already? Kifad'a inbakyaso I'll come over and pick you and nobody will question me for that."
  Dariya sosae tayi.
"Ooo yah maheer, so you care for me that much."
Had'e fuska yayi kamar tana gabanshi.
"Are you kidding me? Princess I can't believe this, baki ta6a k'irana da sunana ba yakai so biyu a rana."
Shiru tayi tana nazari babu shakka gaskiya ya fad'a.
  "You sound very different today ba princess Dina da nasani ba."
"My paladin am sleepy ne shiyasa."
"Yaushe kikafara jin bacci in muna magana and what happen to your iPad?."
Batason wannan tambayoyin dayake mata dasauri tace.
"My paladin d'azu ummi tacemun bakada lafiya,kuma baka fad'a munba."
"Stomach pain ne princess kuma na samu sauk'i."
"Again,why are you stressing yourself too much,you're a Dr. My paladin, please ka binciki ciwon cikin nan, sannan kadaina aeki sosae saboda jikinka."nan tafara surutu.
Tunda ta fara take murmushi shi kad'ai, ya yarda k'aunar miemie a jininsa ne, yanajin bazai iya rayuwa babu itaba.
"Princess you're my everything."yafad'a a hankali Wanda yasa surutunta tsayuwa.
"What?"ta tambaya.
Sai a sannan yasan me yafad'a.murmushi yayi tareda cewa.
"Princess I got to go... Abba na nemana, bye take care."yayi saurin kashe wayar yana murmushi.
"I love you mariam."tafad'a yana kallon wayan tareda ajiyewa yatada engine.

*****
  Itakanta batasan meke damunta ba, amma tsintar kanta tayi da kasa bacci,tagama nazari kuma ta yanke hukuncin cigaba da aekinta batare da tsoro ko shakkar komaiba, alk'awari babban abune kuma yazama wajibi tacikashi saboda gujewa hukuncin allah tunda tanada iko, ta watsar da shakka saboda tasan allah ne zai kareta saboda addu'ar iyaye na tare da ita.
Kasa bacci tayi tamik'e tareda ficewa zuwa saman terrace tunda baccin yak'i zuwa.
Batare da tunanin komaiba ta Sanya hularta dama pajamas ne jikinta, takalmi ta zura tareda ficewa.

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now