In dedication to
Miemiebee 👄******
Jaleelah ce tsaye taci uwar kwalliya wane wacce zata gidan biki sai tauna chewing gum take tana wani karairaya,ta watsa wa miemie mugun kallo tana wani fari da Ido tareda Jan k'aramin tsuka.
"Sai ki matsamun tunda k'ofar ba na gidan ubanki bane."
Kan ubaa miemie ta raya a ranta,lallae wannan batasan halinta ba,ta lura akwai wasu almatsutsai da suke yawo akanta amma saita cire mata su sannu a hankali,saita koya mata hankali ta gwada mata ita ba kanwar lasa bace ko ita 'yar wacece.
"Nakega ke din nan k'ofar na ubanki ne, naga kema zuwa kikayi kamar yadda nazo."
"Me kike nufi?"jaleelah ta fad'a a hasale.
"Maimaita magana sai irinku masubin gidan saurayi kullum zance."ta fad'a tana smirking.
"Ke da wa kike?"jaleelah ta fad'a cikin masifa
"Auu...dama akwai wani rai ne anan bayan ni da ke?"
"Na lura bakida tarbiya Doctor,you do not have respect for others at all amma zan koya miki yadda a girmama mutane..."
"LOL...I guess those who criticize others often are not perfect either..."cewar miemie
Dariya ta kwashe dashi tace.
"Eyya allah sarki...ina hankali anan dahar za'a koya wa wani? Karkiji haushina saboda idan da kinada hankali bazaki tareni da fad'a ba, tukunna ma me namiki kikejin haushina?"tafad'a bayan ta d'aure fuska.
Shiru jaleelah tayi dan batada amsar bayarwa, ita kanta bazatace ga dalilin dayasa takejin haushin miemie ba saboda ta tabbata abunda take zargi bazai ta6a faruwa ba.
"Kifita hanyar murad sai mu zauna lafiya."ta fad'a a hankali
"Murad?"miemie ta tambaya sarcastically.
"Ehm..."
Miemie tayi shiru zuciyarta na mata wani k'una da tarasa dalili haka kawai taji jikinta yayi la'asar sannan ta kalleta tayi murmushi.
"Ohh shiyasa kikejin haushina,don't you trust him?"
"I do..."
"Then meyasa kike zarginsa,ina tsammanin duk wanda ya yarda da fiance nashi komai yaji ko yagani bazai ta6a kawo zargi a raiba."ta sauk'e numfashi dan wani k'una da zuciyarta keyi
"Ki kwantar da hankalin ki jaleelah I've nothing to do with him and never will kingane?"
"Whatever... But abunda nakeso just stay away from him."tafad'a tana juya idanu.
Murmushin da baikai cikiba miemie ta k'ak'alo.
"Okay as you wish...but mind you, respect is reciprocal idan kinaso muzauna lafiya respect me and I'll respect you in return."tana kaiwa nan ta matsa tareda nuna mata hanya da hannu tana murmushi.
Wani kallo ta watsa mata tareda shigewa ciki gurin zarah dake gaban mirror.
Miemie tabita da kallo tareda sauk'e ajiyar zuciya, rufe k'ofar dazatayi sukayi Ido hud'u da murad dake fitowa daga d'akinshi ya k'uro mata grey eyes dinshi da suke bata tsoro,da sauri ta rufe k'ofar tareda dafe k'irjinta dake bugawa tana jinta a wani yanayi.
"Gashi ya jalal na son miki magana."cewar jaleelah tana mik'awa zarah waya.
Take annurin fuskarta ya d'auke tabi wayan da wani mugun kallo.
"In bakida abunyi ni inada,karki 6atamun lokaci."cewar jaleelah.
"Nima ae abu kikaga inayi ko? saiki jira in bazaki iyaba kiyi gaba dan ba'a cemiki inason magana dashiba."cewar zarah bayan ta cigaba da kwalliyarta.
"Ni keke gayawa magana zarah? Okay fine kijira sammaci daga gun hajjo."tafad'a tana harararta.
A hasale zarah tamik'e.
"Sannu 'yar gwal d'in hajjo Meyasa kukeson threatening d'ina da hajjo huh? saboda itace ta haliccine dazanji tsoronta iyee...ta bari kiji a da kenan banda yanzu kingane? So do your worse"
"Zarah please..."miemie takatseta da sauri.
Jaleelah da ranta ya gama 6aci ta juya zata fita miemie tayi saurin shan gabanta tareda mik'a mata hannu.
"Bani wayan."
"In nakine sai ki kwata."tafad'a a hasale.
Miemie ta runtsa Ido tanason gusar da 6acin ranta.
"Please..."ta fad'a with pitiful face.
Damk'a mata jaleelah tayi tana wani cika tana batsewa,miemie tayi murmushi.
"You can go I'd try to convince her idan tagama your phone would be returned back to you ASAP..."
Batareda ta bata amsaba ta ra6a ta gefenta ta wuce.
Miemie ta bita da kallo har ta fice kana ta dawo da kallonta kan zarah.
"Gashi please talk to him."
"Akan meye?"ta fad'a cikin k'unan rai
"Zarah please... Kicigaba da yadda kikeyi a da, idan kika sauya ayanzu what did you think would happen huh? Bakya ganin hajjo zata gano akwai wani Abu a k'asa? Ko so kike komai ya ruguje tun daga yanzu?"
Tayi saurin girgiza kai.
"Idan bakyasa you have to talk to him kuma please treat him with respect."
Amsar wayan tayi ta shiga dialing numbernsa suka fara magana miemie na gwada mata yadda zatayi.
Bayan sun gama miemie tayi murmushi tadubeta.
"Kings yanzu everything would work as planned."
Itama ta mayar mata.
"I hope so."

YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romance"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...