IN DEDICATION TO MIEMIEBEE👄****
Maama na a toilet tana wanka, ta goga soso kenan taji fad'uwan abu gijib a k'asa, jin ihun twins yasata rud'ewa. Ko d'auraye jikinta bata tsaya yiba ta d'aura towel, gashi tafiyar ahankali take saboda aekin da aka mata.
Fitowarta yayi daidai da shigowan sadeeq da ikko.Maama salati tahauyi Dan batayi tsammaninsu a wannan lokacin ba. Gaba d'aya ranta ya gama b'aci rasa abunyi ma tayi.Da sauri ikko ta d'aga macem dake k'asa tana tsala ihu. Mama ta d'auki namijin tana jijjigashi.Sadeeq ne yanufi shoe rack na maama yad'auko takalmi da nufin jibgarsu rai a b'aci.
Ganinsa da takalmi yasasu sakin juna suka falfala a guje harsuna ture ikko sura k'iris tasake jibguwa a k'asa Allah ya taimketa bango ya tareta.
"Mtsw!" mama taja tsaki tamik'awa sadeeq namijin ta k'ar6i macen a hannu ikko dake kuka har yanzu, zama tayi a bakin gado tafara bata nono. Sadeeq ya mik'awa ikko namijin"Yaushe suka iso?" Mama ta tambaya.Sadeeq dake maida takalmi yace "nima ganinsu kawai nayi"
"Usman ne yadawo dasu dama jiya hajja tace zasuzo duba k'annensu." cewar ikko."maama yarannan basajin magana kwata kwata! Daga zuwansu harsun kusa targad'a ikko" sadeeq yafad'a ransa a b'ace.
"Maza babana jeka dubo usman yanzu ya maidasu."
"Maama yau suka dawo fa ko minti biyar basuyi mai kyauba."
"Inbaso kake amaidamu asibiti dagani har k'annen naka ba maza wuce"maama tafad'a sounding serious.
Ikko zatayi magana maama ta katseta. "Karkice komai ikko yarannan hawan jini kawai zasu samana, bassu kawai in an koma hutun makaranta sa dawo gaba d'aya.""Ca nayi da an barsu ko kwana d'aya suyi..." Maama tayi jim can tace "Anjima kad'an zasu koma tare da hajja in tazo."
****
"Nifa hankalina bai kwantaba da komawan yarannan" cewar hajja tana duban rabi dake ajiye basket d'in abinci a falon.
Dariya Rabi tayi"Wallahi kuwa hajja! Duk yanzu zasu birkita lissafin gidan"
"Mtsw! Yara kaman masu kan dutse, kwata kwata magana bata shigansu, kai anjima tare zamu dawo! Tun farko bansan meh yakaini cewa su je ba"
"Da dai anbarsu ko kwana suyi"
"Wa? A ina din?" Cewar hajja "Ae inkinga sun kwana to hutunsu ya k'are kamunnan 'yan biyu sunyi arba'in" hajja tafad'a tana mik'ewa.
Dariya sosai rabi tayi."Kawai suje su birkitamun 'ya da 'yan jikokina haka kurum! Su dawo muyita tuk'awa anan, ko wani d'an banza sai yayi hankali!" "Allah ya kyauta""Maza bawa usmanu yasa a mota, yau 'yan jikokina zasuci girkin hajja"
*****
"Assamamu alaikum!"Hajja tashigo tareda usman d'auke da basket d'in pepper soup dinta.
Hydar, khaleel, da faruq zaune a falo kowa yayi zugum kamar mutanen kirki sanadiyar kwadin maama dasukasha dalilin fasa magungunan twins dasukayi garin k'iriniya.Wannan Karon banda hydar.
"Sannu da zuwa hajja" cewar sadeeq dayafito daga kitchen d'auke da ruwan Lipton zaikaiwa maama.
"Yauwa d'an albarka!"Ta gefen ido take kallon sauran ukun da ko kallo bata ishesuba, sun wani chona baki sama.Ikko ce ta karb'i kayan hannun usman tashige dashi.
Zaune ta iske maama tabawa namijin nono, macen na akan gado tana kuka ahankali har alokacin.
"Ya salam!"Cewar hajja tare da d'agata sama tana jijjigata.
"Sannu da zuwa hajja!" mama ta fad'a.
"Subhanallahi!" Hajja ta furta ganin goshin princess ya kumbura yayi jaa."Meya sameta a goshi maman sadeeq?"
Sadeeq dake ajiye Lipton yace."Fad'uwa tayi hajja!""Fad'uwa? Garin yaya?" Duka sukayi shiru suna kallonta.Can tace
"Yaran nan ko?" Tafad'a sounding serious.Nan ma shiru suka"Bamagana nakeba kuna jina?"
"E..eh" cewar sadeeq.Mik'awa mama tayi"Rarrasheta ina Zuwa!"Wayan radio hajja ta zare tayi waje tana fad'in
"Duka ubanku zakuci yau"duka sukabita da kallo.
***
Khaleel na kwance a k'asa kan carpet ya babbaza k'afa yana kallo. Hydar kuwa ya d'uk'ufa Sai cizgar cinyan kaza yake yana lullumshe idanu, faruq kuwa har yafara gyangyad'i ga popcorn Baja baja a bakinsa da jikinsa gaba d'aya sunyi kaca kaca da falon.
"Yau sai jikinku ya gayamuku 'yan hofin yara. "Babu wanda kalli inda inda take balle sulura da wayar hannunta.

BINABASA MO ANG
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romance"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...