In dedication to
Miemiebee 👄******
"Shhh don't move doctor...It's me Sadisu..."taji daidai saitin kunnenta tareda sakar mata baki
Ajiyar zuciya ta sauk'e tareda k'ara lafewa, suna hango sanda daya ya k'ariso tagun tareda hashaskawa.
"Babu kowa..."yafad'a tareda duban dayan.
"Okay... Ka zama cikin shiri cause anytime za'a iya bamu umarnin kashe PMB kuma kasan ba Abu bane mai sauk'i."
Yayi dariyar shak'iyanci.
"Mutuwar PMB ba abu bane mai wuya aguna saboda akwai hanyoyi da dama da zamu gama dashi batare da an zargi kowa ba,yanzu dai matsalarmu dayace wannan jarabbiyar likitan mai taurin kai data kasa jin gargad'i."
"Mtsw manta da shafinta a yanzu,PMB ne a gabanmu ita nata bamai wuya bane, yanzu dai mujira dawowan rankai dad'i zuwa jibi sannan a San abunyi."
Daga haka yace.
"Koma bakin aekinka karka bari kowa yasan daganan kake, nima zanyi k'ok'arin yin hakan dan kar a zargi wani Abu sannan karka yarda ka nuna kasanni mukashiga cikin sauran."
Suna kaiwa nan kowa yanufi hanyarsa suna waige waige dan tabbatar da babu Wanda yajisu, duk abunda suke su miemie najinsu saidai har a lokacin basu samu damar ganin fuskokinsu ba.
Bayan sun tafi suka fito miemie ta dubi ManSadi.
"Sadi tun yaushe kazonan, I mean for how long have you been spying?"
"I've been following your food steps PMB ne ya hango fitarki he was worried that's why he asked me to follow after you cause a yanzu it isn't safe for you to be roaming around...ganin kinzo nan kin6oye kasan flowers yasa nabiyoki saikuma naji maganganu that's why I hid."
Miemie ta jinjina kai cikeda damuwa tace
"I saw them lokacin da suke zuwa nan through glass wall a corridor na kitchen, nasan babu mai zuwa nan shiyasa nabiyo baya cause dagani they're up to no good I also lied to those securities guava da magani nazo tsinka."
"Banta6a gani ko jin Abu makamanciyar wannan ba am confused doctor, hakan na nufi munafukan a cikin gidannan suke, PMB was right komai anan ake shiryawa..."yafad'a worriedly
"That's what I've been wondering sadi... Emperor's life is in danger."ta fad'a tamkar zatayi kuka.
"I'd have to tell him ASAP..."yafad'a tareda juyawa miemie tayi saurin rik'o bayan riganshi.
"Noo... Karka sanar dashi komai yanzu sadi, bai kamata ya saniba."
"Why?"ya tambaya curiously
Miemie tace
"Idan ka fad'a we won't be able to do anything, wadan nan mutanen sunriga da sunsan komai game da gidan nan, we didn't get the chance to see their faces but am sure we can recognize them by their voices, karka sanar da emperor cause zaice zai taking action kuma kaga suna targeting duk wani moves nasa zasu iya sani, hakan zai iya sawa su sauya plan Wanda bazamu iya figuring ba kaga kuma andad'a complicating kenan..."
Shiru Yayi yana sauraronta dan she has a point.
"Nida kai zamu binciko duk Wanda yake behind all this conspiracy without involving emperor,idan muka samu clue sai mu gathering evidence mukai mishi, daganan saiya taking further wajen tona asirinsu gurin kowa kuma ae musu hukunci daidai da abunda suka aekata...yanzu all we need to do is to save and protect emperor batareda sun noticing ba kagane?"
"Bravo doctor..."yafad'a yana murmushi tareda tafa hannu.
Miemie tad'anyi jimm kana tace.
"A cikin manyan gidan nan Waye baya nan?"
Shiru sadisu yayi yana d'an tunani kana yace.
"hakimi ya tafi yola wani taro, sai waziri daya tafi umrah tun last week."
"Bayansu babu wani?"
"Chief security."
"You sure?"
Ya daga kai
Miemie tayi shiru na dan wani lokaci tana nazari.
"We're done for now, duk wani update dake cikin fadan nan kayi gaggawan sanar dani tanan ne zamu iya samun clue."
"Okay ma'am."yafad'a sa shakiyanci yana Sara mata.
Murmushi tayi.
"You're not serious sadi komai saikasa wasa."
Sosa kai kurum yayi tajuya da zummar tafiya.
"Doctor..."ya k'irata.
Tajuyo ta dubeshi.
"You need to be very careful cause idan wani abu ya sameki (astagfirullah) emperor will never forgive himself for that..."
Bata gane inda maganar tashi ta dosa ba tad'aga kai kurum kana tace.
"Taimakamun ka tsinkamun guava kafun wadannan 'yan iskan suhau bincika na."
Dariya yayi kana yabi bayanta.*******
_3 days later..._A cikin kwanaki ukun nan miemie ta gujewa duk wata hanya dazai had'ata da murad, koda sun hadu a hanya ko kallonsa batayi,koda kuwa abinci sukaje ci bata zama ta inda zasu had'a Ido gaba daya ta d'auke masa wuta Wanda shima abun gabansa kurum yake baya kulata, tsakaninta da su zarah kuwa sun shak'u matuka kusan koda yaushe suna tare hatta zua yiwa mai martaba magani tare sukeyi suna masa exercise, duk wani shege da fice da ake a gidan duk sadi na sanar da ita, jaleelah tad'auke kafa kwana biyu tun randa miemie ta gaya mata magana.
Tsakaninta da hajjo gaisuwa dan dama ita ba'a fiye ganintaba, sun fixing extra classes da amatullah da daddare take koya mata science subjects, sosae ta sake da kowa banda emperor, sadi kuwa ya zama abokinta sosae, mermu kuwa tana shigewa miemie sosae amma miemie bata bata fuska.
Around 4:30pm Zaune suke duka uku sanye akan bench dake tsakiyan field inda ake sport,babu kowa agun sai securities dasuke dan nesa dasu kadan, miemie ce ta insisting su fito dan bata ta6a zuwa tagun ba.Amatullah tace
"I remember sanda yah safwan yake da rai almost every evening sai mun playing V. Ball, tun yah murad idan yazo bayaso har yazo yafi kowa iyawa, we used to have so much fun but yanzu komai ya sauya kamar ba'ayiba."
Miemie ta kalleta cikeda tausayawa
"Let's play..."
"No..."cewar zarah dake rik'e da wayan miemie tana dannawa.
"Why?"
Duka sukayi shiru.
Miemie tadanyi murmushi.
"It's gonna be fun trust me like it was before..."
"But am not good at sports, ni ban iyaba let's do something else."
"Teacher mu kyaleta please let's play..."cewar amatu.
Zarah ta harareta tareda ajiye wayan miemie kan bench din ta mik'e duka suka kalleta.
"Two against one agreed?"cewar zarah tana dariyar mugunta.
Miemie tayi dariya dan tasan da ita take.
"No vex... Am ready for you two."ta fad'a tareda mik'ewa.
Playing suka suna mata keta duk kwarewan miemie a iya volleyball,gaba d'aya straight skirt dake jikinta yahanata playing dakyau sai dariya suke mata.
Rik'e k'ugu tayi tana harararsu.
"Gaskiya ban yarda ba, you guys are cheating..."
"Really?"suka maidata shashasha suna mata dariya.
Ball d'in da d'auka ta wurga direction din da zarah take tayi saurin duk'awa ya saitin inda murad ke tahowa waya manne a kunnensa dayan hannunsa a aljihu, gaba d'aya hankalinsa baikai kansuba sai kwallo daya gani ya taho inda yake yayi saurin kaucewa.
Miemie data juya bayanta da sauri ta runtsa Ido tana jiran emperor yafara masifeta dan tad'au ball din ya sameshi, ji tayi an buga mata kwallon a k'eyarta dasauri ta dafegun tareda juyowa sai ganin murad tayi tsaye a gabanta fuskarsa ba yabo ba fallasa.
Dariya su zarah sukasa aka miemie da hura hanci tana harararsu.
"Next time ki rinka lura kafun ki aewatar da abu."yana kaiwa nan ya juya.
Takaici yarufe miemie dan dariyar dasukeyi, ball din tasake d'auke zata wurga musu yabuge murad akai.
Baki ta dafe da sauri tana muzurai.
"What the..."
"Sorry..."ta katseshi dan ta sha bugeta zaiyi.
Zata juya da sauri yajawo rigarta ta baya hakan yasa ta tsaya tareda juyowa tana muzurai, shiko ya zuba mata idanunsa masu bata tsoro.
"You won't go unpunished..."yafad'a yana waina ball din a hannunsa.
Baki ta bud'e
"But nabaka hakuri ae, besides no body is above mistake."
"Really?"yafad'a yana yana kallon cikin idonta.
Da sauri tasauke nata ta daburce lokaci d'aya.
"Huh?"
"Eh...kai kazo inda muke ae kuma ball din bai sameka ba da farko dan neman magana ka kwadamun akai dan mistakenly yasameka kace saika rama Bacon kai kafara bugamun"tabashi amsa bayan ta gathering courage dinta cikeda masifa
To her greatest surprise taga yad'anyi murmushi har dimple dinsa suka motsa sosae murmushin yai masa kyau.
D'aga ball d'in yayi ya buga mata a goshi yana kallonta, sosae taji zafi cikeda haushi itama ta rama nan fa akahau buge bugen ball.
Sadi,zarah da amatu dasuke tsaye gefe aka barsu da kallo cikeda mamakin murad banda safwan babu Wanda yake biyewa amma ji yadda yakewa miemie.
Daga buge suka koma V. Ball inda yayita yarda ita a k'asa tana k'uluwa kuma sam yak'i bari ta amsa sai juyata yake yana murmushin mugunta.
Sadi da amatullah suna hailing PMB while zarah nabin bayan miemie,sosoe suka shagala da abunda suke har basusan isowan jalal da jaleelah ba wacce sai cika take tana batsewa.
Sarai zarah ta gansu ta fuske abunda Ashe jalal ya lura (kamanninsu sak da k'anwarsa suna kuma ibi su murad).
D'aga ball d'in yayi sama miemie tahau tsalle zata kwace ta kasa, suna cikin haka sai ji tayi an fisgota ta baya saura k'iris ta fad'i murad yayi saurin tarota ta fad'o hannunshi.
Bayan ya gyara mata tsayuwa rai a had'e ya dubi jaleelah dake huci kamar zakanya.
"What the hell! are you out of your senses...
"What? Are you really asking me this yah murad?"tafad'a idanunta suka ciko.
Da mamaki duka suke kallonta banda jalal daya hard'e hannu a gefe.
D'an guntun tsaki yaja zai bai gun tashige gabansa.
"Get out my way leelah."yafad'a a hankali idanunsa a lumshe
"I won't until you answer me this one question..."hawayen suka zubo.
Bud'e idanu yayi ya sauk'e akanta.
"Who's she to you? Menene matsayin wancan a gunka?"
Had'e fuska yayi ransa ya soma 6ace.
"Leelah don't make me loose my temper,get out of my way."
"Answer me...have you ever smile for me? Shin ka ta6a koda mun magana mai dad'i a matsayina na wacce zaka aura?"
"Leelah get out of my way..."yafad'a da tsawa sanda ta tsorita.
"Cut it out bros..."jalal ya k'ariso yaja kanwarsa baya tareda shiga tsakani.
"Kafun ka tambayeta kai bazan maka tambaya d'aya, ka kuwa San mekake aekatawa? She's wife to be Sam baka damu da dignity naka ba here you're playing with a characterless girl wacce batasan mutuncin relashionship ba."
Lumshe idanu murad yayi dan Sam baison hayaniya yabud'e idanu ya kalleshi.
"Just because you're older than me that doesn't you the right to talk to me in this way or question my actions..."ya fad'a yana kallonsa.
"As far as am concern yar uwarka tasan ba sonta make ba coz I don't waste my time on stupid love stuffs, I said it clearly jalal I don't love your sister tasa hakan a kwakwalwarta, that's the least I can expect from her kagane... Mind you karka kuskara kasake tsayarmun haka dan gaba abun bazatai mana kyau ba."
Baki bud'e kowa yake kallon murad dan Sam bai ta6a maida martani ba kan duk abubuwan da ake mishi.
Har zai wuce ya dawo da baya ya dubeshi.
"Don't you ever call her characterless cause she's far more better than your precious sister, she's worth more than her cause all she cares is to put smile on to someone faces, she always share happiness aduk inda take batare da ta damu da bata farin cikin ba kaga shine cikakkiyar maintaining relashionship not like your sister da kanta kawai tasani, I warn always think twice before talking to me."
Yanakaiwa nan ya yarda ball na hannunshi ya wuce sadi yayi saurin bin bayanshi.
Zarah ta tafa hannu ta dubi jalal.
"You heard what my brother said to you..."
Hannu ya d'aga zai sharara mata Mari yaji an riqe.
Bin hannun yayi da kallo har idanunsa suka sauk'a fuskar miemie data rik"e hannunsa idanunta a nasa.
"Ke! Have you lost your senses."
"Of course..."ta ajiye hannun tareda dan guntun murmushi.
"Ko ba'a fad'amun ba nasan kaine jalal... Ahakan kake k'iran kanka mijin da zata aura?"
Shiru yayi yana kallonta da mamaki.
"Image yanzu kagama fighting wa sisternka... Shin ka zakaso a rairaya taka kai kana bugun na wani?"ta d'aga masa gira biyu
"Kaji kunya kuma kasa wannan a ranks zarah would never get married to a monster like you mark my words..."
"How dare you talk to my brother..."
"Shhh jaleelah badake nakeba cause kinyi kad'an kingane..."
"Wow pretty I love your courage."ya tafa hannu yana dariya
"Whatever..."tana kaiwa nan tadubi zarah da amatu tamusu alamar su tafi duk sukabi bayanta.
Tanajin sanda yace
"You're so beautiful pretty..."
Sukayi banza dashi suka wuce.******
Mik'a tayi tareda addu'a kana ta bud'e idanu, a hankali yajawo wayarta ta duba time kusan k'arfe bakwai da rabi, har zata jawo bargo ta koma idanunta ya sauk'a kan MacBook d'inta data kunna da asuba,ganin recorder ya turning kanshi on yasa tayi saurin mik'ewa zauna da pajamas nata baby pink hulan kanta ya zame.
Kasa kunne tayi tanajin maganar dake tashi take komai nata ya tsaya ta gama firgicewa.
"Emperor..."ta furta a gigice.
Da sauri tajawo wayarta ta fara dialing numbern sadi.
Ringing biyu ya d'auka a hakan gani tayi ya jima.
Zaiyi magana ta katsesa.
"Sadi I... Ina emperor?"
"Yana terrace,wani Abu ne?"ya tambaya jin yadda tayi magana.
"Ka... Ka kaimishi coffee da safen nan?"
"Eh yanzu na sauk'o akwai..."
Bai k'arisaba tayarda wayan ta batareda ta dubi yadda takeba ta fice da mugun gudu tahaura stairs zuwa saman terrace batare da lura da taji ciwo a k'afarta ba.
Tana isowa tahangeshi tsaye rik'e da mug a hannushi idanunsa na kallon k'asan building d'in.
D'agawa yayi zai kai baki tayi saurin cewa.
"Nooo..."tareda buge mug d'in ya fad'i kan k'afarta.*******
Vote, comment. And share

ŞİMDİ OKUDUĞUN
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romantizm"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...