In dedication to
Miemiebee 👄******
A wunin ranar gidan dai gashinan dan kowa wuni yayi sukuku,mai martaba ya samu bacci shiyasa babu Wanda yasake zuwa sai SG dake zaune gefensa dan shi kad'ai miemie ta yarjewa ya zauna.
Zaune miemie take a d'akinta tana waya da khaleel...
Khaleel ne kurum take iya fad'a masa Abu ya k'ara mata k'arfin gwuiwa sa6anin sauran da tasan hanata zasuyi saboda lafiyarta musamman yaya deeku dake mata kallon yarinya k'arama.
Duk abunda tayi tana sanar da mama kuma alhamdulillahi tana Goya mata baya tareda da sa mata albarka saidai ta damu da lafiyar 'yarta sosae, miemie'n ce ke kwatar mata da hankali tareda tunasar da ita abubuwan data kowa mata gameda taimako dakuma zamanin annabawa yadda suke jihadi wajen kare addininsu da al'ummarsu.Da haka take convincing d'inta har daga k'arshe tayi mata addu'an kariya dakuma sa'a.
Taki sanar da maheer cause tasan bazai ta6a bari rayuwarta ta shiga cikin hatsari ba,yanzu ne ta fahimci maheer na Sonta fiyeda yadda yakeson kanshi zai iyayin komai saboda kare lafiyarta shiyasa bata sanar dashi ba.
Bayan mama sai khaleel ne yasani.
"We're very proud of you lil fanta..."
"I'm also proud to have a family like you guys, em missing you like hell..."
"When are you coming back gidan shiru yadawo da bakyanan..."
"It's just a matter of a week or two...can't wait to see you guys..."
Haka sukayita yar hirarsu ta gida amma koda wasa khaleel bai sanar da ita shirye shiryen aurenta.
Tana katse wayar hajjo ta shigo d'akin, ganinta yasa miemie mamaki dan koda wasa bata ta6a shigowa d'akinta ba.
Tararta tayi da murmushi.
Zama hajjo tayi a gefenta idanunta taf hawaye ta dubi miemie tace.
"Bazan fasa baki hak'uri ba bisa yadda na treating naki a baya, bansan meke damuna ba a baya amma yanzu nagane kurena dan allah kiyafemun..."
"Babu abunda kika kikamun da zan yafemiki... Nicema nai miki laifi wajen mayar maki magana amatsayinki na babba, dan allah kiyi hak'uri..."
Wai Mariam wace irin mutum ce, halinta daban ne kowa zaiyi alfaharin kasancewa tareda ita.
Godiya taimata sosae tana hawaye while miemie na nuna mata Allah yakamata ta godewa.
Komai ya sulhunta tsakaninsu har hajjo tanemi miemie ta had'ata waya da mama takoyi.
Sosae ta yaba miemie tana kuwa yiwa mama murnar samun 'ya kamar miemie.
Nan danan suka 6arke da hira ashe old time friends ne tun university ikon Allah.
********
Kusan mintinsa biyar a k'ofar d'akin miemie amma ego ya hanasa yayi knocking.
Harzaisa hannu ya buga saiga miemie ta wangalo k'ofar da sauri ya juya zai tafi.
Dariya abun yaso baiwa miemie.
"Excuse me..."tace dashi.
Juyowa yayi gira a had'e.
"What?"ya tambaya.
"What were you doing?"
"Pardon?"yace kamar baisan abunda take nufiba.
Gimtse dariyarta tayi kana ta ta6e baki tace.
"Baka bani amsaba...kuma don't lie cause na kamaka."
"Was just passing by."yabata amsa firmly ko shakkar kamasa da karya baiyiba
"Geez...You were pepping through my door weren't you?"
Wani kallo ya watsa mata kana yace.
"Don't have your time..."ya juya tareda shigewa d'akinsa ya rufo k'ofa.
Murmushi miemie tayi tana mamakin hali irin na emperor...
D'akin zarah ta shige dan d'aukar charger na wayanta.
Saida sukasha hirarsu kana takoma nata d'akin domin tasamu bacci.
Fitowar ta keda wuya tasamu murad tsaye k'ofar d'akinta kamar zaiyi knocking saiya fasa.
A hankali ta k'ariso ta tsaya d'an nesa dashi tana kallonsa tana k'ok'arin rik'e dariyar ta.
K'arisawa tayi ta folding hannuwanta kana tace.
"Hy Emperor..."
Cak ya tsaya batare da ya juyo ba can ya juyo alamar surrender.
Murmushi miemie tayi ta ra6a ta gefensa zata wuce, abunda kunnuwanta sukaji ne yasa ta kasa motsa hannunta dake kan doorknob ta tsaya cak batare da ta juyoba.
"Mariam..."ya kuma k'ira for the second time.
Tunda take bata ta6a jin Wanda yafi iya k'iran sunanta ba sai emperor bata ta6a sanin sunanta akwai dad'i ba sai yau.
Juyowa tayi ta dubeshi inda yake watsa mata wani kallo mai wuyar fassaruwa.
"Thank you..."yafad'a cikin kakkausar murya.
Kafun ta bud'e baki ya cigaba saikuma yayi shiru kamar mai tsoron wani Abu...itadai idanu ta zuba mishi,can yayi dan murmushi ya sauk'e idanunsa daga kanta yace
"You're a blessing mariam...thanks."yana kaiwa nan ya juya ya da sauri ya shige d'akinsa.
Tsayuwa miemie tayi motionless takasa ta6uka komai, yau kallon da murad ke mata yasha babban da yadda yasaba kallonta, karon farko taga tsoro a idanun murad yakasa mata magana,me hakan yake nufi?_*Two days later...*_
A cikin kwana biyun nan rayuwa ta komawa iyalan mai martaba daidai, da taimakon miemie komai ya daidaita tsakanin hajjo da 'ya'yanta, ta nemi yafiyarsu musamman murad kuma suma sun nemi nata alhamdulillahi komai yadawo daidai, suna gudanar da rayuwarsu cikin walwala da raha, ba k'aramin dad'e hajjo kejiba idan tana akusa su suma haka, sai yanzu sukasan dad'in uwa,sosae suke sanar da ita duk wata matsalarsu kuma tana fahimtarsu tareda magance musu, zarah zata koma makaranta while amatullah zata tafi baze university abuja...har a lokacin jikin mai martaba baiyi kwari ba but yana samun sauk'i da taimakon Allah dan miemie tana bashi taimako daidai iyawanta.
Wani kulawa suke baiwa miemie tareda wani girmamawa, sosae hajjo keji da miemie dan idan suna 'yar fad'arsu da murad bayan miemie hajjo kebi.
Jalal da jaleelah kuwa har alokacin basu sake kullum cikin damuwa suke ganin irin abubuwan da iyayensu suka aekata ballantana jaleelah kullum saitayi kuka, ganin haka abba ya umurta sudawo kusa dashi dan jikinsa ne yana amatsayin ubansu kulawarsu yanzu a k'ark'ashinsa suke, dukda har alokacin basa wani shiri da miemie amma ita tana iya k'ok'arinta wajen ganin tamanta da abubuwan dasuka faru.
Su hajia laelah kuwa an repenting dan har gida tazo tanemi yafiyar kowa kuma an yafe mata.
Tsakanin murad da miemie kuwa though za'a ce sun zama friends but always fighting, murad jida kai da son girma while miemie tsokana kuma karya mata masifa yanzu zasu haura sai hajjo ta shiga tsakani.Ana washegari za'a gurfanar dasu hakimi gaban court miemie taje duba mai martaba, bayan yar gwaje gwajen datayi tana murmushi ta dubeshi tace.
"Alhamdulillahi abba kana responding to treatments,BP'n ka ya dawo normal and komai naka na functioning daidai...Allah dai ya k'ara maka lafiya"ta k'arishe tana murmushi.
Murmushin yai mata tareda gyara kishingidarsa,yanzu yamaida komai kamar ba faruba, yayarda duk abubuwan dasuka faru a baya k'addararsa ce haka Allah ya tsara ya kar6a hannu bibbiyu yamaida komai kamar ba komaiba, all he needs to do is to face the future, sosae zai tsare iyalansa sannan ya tsare mulkin da Allah ya d'aura masa.
Dubanta yayi tareda fad'ad'a murmushinsa yace.
"Ameen Allah yayi maki Albarka mariam..."
Ta amsa da ameen harta juya zata fita ya k'irata juyowa tayi tareda komawa.
"Wani abune kakeji?"
Girgiza mata kai yayi alamar a'ah yace
"Zauna inada magana dake..."
Ba musu ta zauna tareda maida hankalinta kansa kana yace.
"Bansan da wani baki zan gode maki ba mariam,Allah ne kawai zai iya biyanki da abunda kikai mani da iyalina ke alherice a rayuwarmu,nago..."
Bai idasa ba ta dakatar dashi,ji yadda yake gode mata tamkar ba sarki ba...
"Babu godiya tsakaninmu abba sadai tsakaninka da Allah saboda shi ya cancanci ka gode masa,duk abunda yafaru bisa ikonsa ne..."
Murmushi yayi yanajin k'aunar miemie har cikin ransa, inama da zata dawo cikin zuri'arsa gaba d'aya dayafi kowa farin ciki.
Umurtar ta yayi da ta d'auko masa wasu files dake cikin safe dan kai tsaye ya sanar da ita password d'in (He trusted her).
Bayan ta d'auko masa ta mik'a masa, pen ya d'auka ya fara signing duk abunda yake miemie na zaune a gurin.
Bayan ya gama ya dubeta tareda mik'a mata.
Da mamaki take kallonsa ba tareda ta amsaba.
"Wannan k'aramar kyautace daga gareni amma karki bud'e har sai randa Allah yasa kikayi aure...kiyi hak'uri da wannan dan abunda kikamun yafi k'arfin sa."
Girgiza miemie tayi da sauri tace.
"Duk abunda nayi saboda Allah nayi bawai dan abiyani ba,kayi hak'uri amma bazan iya amsaba."
"Umurni nake baki a matsayi na na Wanda kika d'auka uba, zanso kimun biyayya ki amsa kyautata...kisa a ranki ba biyanki nayiba kyautace kawai."yafad'a yana d'an murmushi.
Ahankali tasa hannu hannu ta kar6a tareda masa godiya sosae.
Daganan kuma ya rink'a tambayarta wasu tambayoyi tana bashi amsa,ya yanke wani hukunci Wanda yake fatan Allah yasa ta tabbata.******
Bayan gurfanar dasu hakimi da akayi gaban kotu an yanke masa hukuncin kisa ta banyan rataya, wazeeri kuwa shekaru arba'in a gidan yari tareda horo mai tsanani, hajia kalthum kuwa shekaru goma sha biyu saboda tasan duk abunda mijinta ke kullawa tayi shiru, mermu & co an yanke musu hukunci daidai da laifukan dasuka aekata.
Mai martaba ya gana da hakimi daketa sunbatun hauka yana saiya kashe Murad da miemie,ya share kwallan idanunsa yana kallon hakimi daketa kwasar dariy yace.
"Na yafe maka baffa hakimi Allah ya gafarta maka..."yana kaiwanan namik'e yabarshi yanata dure duren ashar Wanda dagaji kasan bai cikin hankalinsa.
With time yasan hajjo ma zata yafe masa (Duk laifin da wani ya aekata maka aduniya kayi k'ok'arin tursasa zuciyarka da yafe masa sannan kasa a ranka komai yafaru rubutacciyace haka Allah ya tsara, Ubanginmu yana yafe mana meyasa mu bazamu sa salama a zuciyoyin mu mu yafi juna ba...Dan Allah muna k'ok'rin yafiya ko ba take ba ko muma Allah zai yafe mana zunuban mu).
Jalal da jaleelah sunyi kuka tare da takaicin abunda iyayensu suka aekata, sun gane duk gatan da iyayenka suka nuna maka idan basu baka tarbiya duk a banza ne, ko wanne a cikinsu ya shiga taitayinsa.*****
Sorry for the long wait
Vote, comment. And share
Much Love ❤
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romance"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...