chapter 41

1.7K 146 2
                                    

In dedication to
Miemiebee 👄

******
"Emperor."ta maimaita.
Cak ya tsaya cikeda mamakin abunda yaji, wani yanayi yashiga mai wuyar fassaruw, kansa gaba d'aya tad'au zafi, baita6a bayan marigayi safwan akwai Wanda zai k'irasa da wannan sunan ba, take ya runtsa idanu yana tuno wasu abubuwa gameda rayuwarsu shida d'an uwansa.
"Emperor"ta maimaita Karo na uku, take yadawo reality, tamke fuska yayi tareda juyawa cikin zafin nama dan ganin Wanda ke shirin dad'a masa damuwa bayan Wanda hajjo tasamai.
Gijibbb sukaci gware da miemie data matso kusa dashi.
Atare suka dafe kai lokaci d'aya idanunsu ya shiga na juna sosae,kasa d'auke idanunsa sukayi still hannunsu na goshinsu.
Sunkai 10secs ahaka kamar Wanda aka tsikara da Sauri suka kauda kai, PMB yasake tamke fuska yajuya da zummar cigaba da tafiya.
Da sauri tasake cewa
"Emperor"
"What the..."ya juyo a zuciye tamkar zai mareta da sauri taja jikinta alamar tsoro.
"I... I.. I... I'm s.. Sorry em...PMB"ta stammering tana blinking eye lashes nata cikeda tsoro.
Runtse Ido yayi kana ya bud'e ya zuba mata idanunsa dasuke bata tsoro.
"Don't you ever call me with that em... Whatever kingane."
Da Sauri tafara girgiza kai kamar k'ad'angare still tana rungume da jikinta.
Juyawa yayi zaibar gun ta kuma cewa.
"Emperor..."
Juyowa yayi rai a mugun 6aci, cikeda tsoro bakinta ya kafe shibai rufu ba.
"Am so sorry."tafad'a bayan ta runtsa ido.
Kallonta yayi nad'an dak'ik'u kana yafara tafiya.
Da sauri miemie ta juya bayanta tafara masifa.
"What the... What the... What the... Mtsw Sak yake da jatumarshi aradu, komai masifa,inba emperor ba mezan ce maka,yo yace bayaso a ace masa yareema,bayanso ace masa prince to da uwar me zan k'irashi kalen na k'irashi da sunanshi ya manna mun bindiga irin na jiya,todai aradun allah emperor zan k'ira saidai ka kashene,masifaffe kawai mai ido kamar mage."ta dinga shirmenta tana d'aga hannu.
"IPad d'ina."tafad'a da k'arfi cikin zafin nama ta juya saiji tayi taci Karo da k'irjin mutum.
Wani ihu tasanya cikeda tsoron Wanda ta gani.
"Am dead."tafad'a a le66anta tana kallonshi ganin 6acin ran dake kwance a fuskarsa.
Wani fitsarine ya taso mata, ahankali ta fara tattaro k'asan gypsy skirt nata da zummar guduwa.
  Juyawa tayi da mugun sauri zata arce taji an cafko hannunta.
"Wayyo allah na emperor wallahi bani naceba baki nane, wallahi ban k'iraka mai idon kuliya ba,duk bakina ne ya fad'a."tafad'a cikeda tsoro dukda ba kallonshi takeba.
  Ahankali ya dawo gabanta yana kallonta, da sauri ta runtse idanu jikinta na kakkarwa.
"Shikenan yau za'a bindigeni, dan allah kafun ka kashene kabari nayiwa su mama da yah maheer bankwana."tafad'a still idanunta a rufe kuma bai sakar mata hannu ba.
  Jin shirun da yayi bai gaura mata Mari kamar yadda tayi tsammani ba tafara bud'e idanu a hankali eye lashes nata na blinking eye brows nata na had'uwa bakinta na turuwa gaba har tabud'e idanunta duka ta zubashi fes akansa, mamakine ya kamata ganin fuskarsa.
Idanunsa ya zuba mata bakinsa d'auke da d'an guntun murmushi.
Ganin ta bud'e idanu ya tamke fuska tareda sakar mata hannu.
Gyara tsayuwarta tayi tareda kallonsa idanunta na rufuwa still tsoron na jikinta.
"Me kike buk'ata?"ya tambaya idanunsa na kanta.
Da sauri ta d'ago tareda zuba masa idanunta hak'oranta a waje tana murmushi.
"Laaa.... Dagaske ka yafe."
Lumshe idanunsa yayi yabud'e tareda had'e gira.
"Ba wannan nake buk'atan ji ba."yafad'a cikin husky voice nasa.
"Oooo.... Yanzu zan iya cemaka emperor bazakaji haushiba...
"What the...
"Am sorry..."tafad'a da sauri.
Juyawa yayi da sauri ta rik'o wrist nasa tace.
"Jiya nabar iPad da headphones d'ina a d'akin ka."
Tsayawa yayi tareda juyowa ya kalli hannunsa data rik'e da sauri ta sake tana muzurai.
"Sai akayi yaya?"ya tambaya fuska a had'e.
"Tunda nace yana d'akinka ae kasan me nake nufi, kabani kayana nake nufi inbaka ganeba."tafad'a cikeda gautsin baki.
Had'e girar sama yayi yana kallonta, saurin to she bakinta tayi da hannunta, shaf tamanta a gaban wa take.
Matsowa yayi dab dab da ita yana kallonta, ahankali taja baya saboda wani irin yanayi data tsinci kanta, tasaba mu'amala da maza bata ta6a jin wani abuba sai a yanzu.
"Maimaita abunda kikace."yafad'a yana kallonta.
Kasa kallon fuskarsa tayi tana I ina...
"Dama...dama cewa nayi ka taimaka ka bani zanyi amfani dashi yanzu dan allah."
Dan murmushin fatar baki ya sake kana ya had'e fuska tareda matsawa baya yajuya yafara tafiya tareda cewa.
"Abunda ba nawaba baya kwana a d'akina,so zaifi kyau tundaga yanzu kifarabin dustbins kina dubawa."tafad'a yana tafiya.
"Huh?"miemie tafad'a da k'arfi.
Kafun tace wani abu ya 6acewa ganinta.

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now