chapter 5

2.6K 186 2
                                    


IN DEDICATION TO MIEMIEBEE👄

*****

Time marches on,twins sun kai wata bakwai, sunyi wayo sosae suna rarrafensu ko ina, b'arna kuwa ba'a magana har gwanda Ammar, komai miemie tagani kusa saita b'arnatashi, bata iya ganin abu ta bari ga shegen k'iriniya da kukan banza ga uban masifa bata yarda da kowa sai mama,ikko da sadeeq,mama takoma aekinta tana barinsu hannun ikko, duk wanda yayi gigin d'aukarta bayansu to zaisha mari ko yak'ushi kokuma ta zunduma ihu tak'iyin shiru harsai kabar gun,so tari da yawa dukan ammar take tayita yak'ushin shi haka zataita cin zalinshi, ko ciwo ne ammar ke yi musu haka zaiyita zazza6i da mura ita kuwa sai aukin k'iriniya idan guri ya lafa to tayi bacci, tana tashi kuwa kowa sai yaji a jikinsa. Caf cikinsu hydar ne baya kyaleta bai la'a Kari da k'ank'antar ta yake bugunta.

Akwai ranarda hydar na kwance kan rug yana assignment bacci ya fara d'ibarshi, miemie dake gefe tana wasarta itada ammar ta rarrafo gunshi,littafin ta d'auka tafara yagawa iya karfinta tana ihunta, bayan tagama yagawa babu paper d'aya data bari da mutunci tad'auki pen tana cakinsa dashi tana kyalkyalar dariya, motsawa yayi batare da yaga b'arnar datayiba ya matsa daga gabanta yacigaba baccinsa, rarrafawa tasakeyi zuwa gunsa tana cakinsa, cikin zafin nama ya kwace tareda gyara kwanciyarsa yacigaba da baccinsa, ihu tasa tana kuka

"Ke kiyi min shiru ko naci k'aniyarki!"Yadaka mata tsawa yad'aga hannu kamar zai mareta.

Shiru tayi tana kallonsa, tsaki yayi tareda rufe idonsa, wani k'aran cin zuciya tayi ta fillesa da mari.

A gigice yatashi yana rik'e da gun. Kallonsa take cikin cin rai ta k'ara yak'ushinsa a fuska. D'aga hannu yayi bugeta tasa wani razanannayar ihu

"Ya haka hydar?" Cewar ikko dake shigowa.

"Ikko wallahi yau saina bugeta, kinji marin da ta shararamin ne"

"Oh hydar bakaga yarinya bace kayi hak'uri mana!" Tafad'a tana dagata

"Dan tana yarinya sai tayita bugun mutane ana kyaleta, mud'in ba yara bane kuke gibgarmu..."yafad'a yana harararta Kafin idonsa yakai kan 6arnar datai masa

"Kutumelesu! Wallahi bazan hak'uraba!"Ikko takai idonta gun abunda yake kallo.Mik'ewa yayi ya taske k'eyarta da mari.take miemie tasanya ihu

"Haba kaikuwa hydar ba'a hak'uri ne, ba yarinya bace!"

"Shegiyar yarinya mai kan roba!"

"Naka kuwa na gwangwani mai rashin kunyar tsiya!" Cewar ikko da ranta yasoma b'aci

Miemie dake k'ok'arin kamowa daga jikin ikko tarik'o kumatun hydar da faracunta taja iya k'arfinta tana cije baki, ihun azaba hydar yasa yana k'ok'arin janye hannunta.

Ikko itama k'ok'arin janye hannun take sun kasa, dakyar suka samu suka janye hannun.

Kumatun hydar yayi ciwo ga shatin faracunta nan mad'au, tsabar azabar zafi baisan lokacin da yafara kuka ba.

"Maganin mai cin zali kenan, mutum rashin hak'uri kamar zawo!" Cewar ikko dake rik'e da ita suna barin gun.

Tattara tarkacensa yayi yabar gun rai a b'ace har yana bangaje ammar dayake wasansa baisan wainar da ake toyawa ba.

Sosae miemie batada hak'uri, komai yayunta sukai mata tofa saita rama, wani sa'in har idan anfara bawa ammar nono kafun ita to ranar mama ta dinga shan cizo a wajen feeding din miemie, kokuwa ta mareta, idan kuwa aka d'auki ammar ba'a d'auketa ba tadinga jan k'afafunsa tana ihu tana bugunsu.sadeeq ne kurum bata yiwa fitina shikad'ai ke iya lalla6a ta.
Ana haka har suka yi shekara da wata takwas,babu inda basa zuwa nan k'iriniya ya dad'u, sosae basajin magana inba na yah deeku ba (sunan sadeeq da miemie ta rad'a masa kasancewar shine Wanda tafara Kiran sunansa a kaf 'yan gidan) shima kuwa gwuigwui yake k'iranta, kasancewar 'yar guntuwa a k'asa gata babu jiki tananan fingil fingil ga shegen surutu gata da shegen k'arfin tsiya,komai da k'arfi takeyinsa Sam bata Abu ahankali.faruk shine abokin wasansu miemie,in ammar yamata Abu dukan tsiya take masa yayita kuka, saikuma tazo tana lallashinsa,Idan tahau dambe da faruk wane sa'anta kuma wani sa'in duka take masa, abokin wasanta khaleel ne,hydar kuwa kamar wuta da auduga suke, kwata kwata basa zama inuwa d'aya.
Rayuwar miemie tamkar ta maza takeyi, fad'ace fad'ace da wasan banza, uwa uba neman tsokana,kaya kuwa inba Riga da wando akasa mataba to ta dinga ihu kenan harsai an Sanya mata ita a dole irin ammar zatasa.Hajja tana mugun ji da miemie,bata bari a takura mata ko kadan.

_THREE YEARS LATER_

Acikin shekarunnan abubuwa dayawa sun faru ciki kuwa harda shigan twins makaranta Wanda kullum sai anyi drama da ita kafun taje.

Ayau zasuje gidan hajja, ikko tai musu wanka,ammar aka fara yiwa

"Mamana zo muji kiyi wanka!"

"O oo!" tafad'a tana make kafad'a
"Nikam ooo bajaki kayyamun uwawu ba!"

Dariya ikko tayi Dan kullum darun da ake tuk'awa da ita kenan.

"Matso kiji"

"Nak'i jin wayo jakimin"

"Idan bakije ba tafiya zanyi na barki"cewar ammar

"Fad'a mata kam! Muje nasa maka kaya yah deeku yakaika kai d'ayanka banda ita"

"Yeeh! Banda wata!"Miemie ta d'aga hannu ta zabga masa duka a gadon baya tana hura hanci.Baki ya wangale zai fara kuka.

"Ammar rama Karka barta"cewar hydar dake shigowa.Ae kuwa ammar ya Rama. D'aga hannu zatayi ta Rama

"Kul! Kika kuskura kika tab'asa saina miki suka!!" Yafad'a yana zare mata ido

"Meya kawoka nan hydar kullum saika had'a yaran nan fad'a" ikko tafad'a

"Kurum saiya barta tayita cin zalinshi bai ramawa, shine ne fa namiji"

"Baka ganin yarane yaushe sukayi wayo iyee! Maimakon ka sulhun tasu saika tada fad'a, bacin kafi kowa sanin rashin hak'urin miemie!"

"Ikko bawani abarta, barintan ne kesa take abunda taga dama, yarinya sai shegen masifa da taurin kai!"

"Ammar duk randa tasake tab'aka ka tak'ar k'ara ka Rama kaji!"B'are baki tayi zatasa kuka. "Karki kuskura!!" Yadaka mata tsawa

"Uwaka!" Tafad'a ware fingers nata tana tura baki da gudu tayi hanyar waje. Hydar cafkota yayi yahau kilarta, miemie kuwa dan tsabar cin rai ramawa take tana ihu.

"Kyaleta hydar mana,kaiwani irin yaro ne,banga laifin miemie ba gado tayi!" Ikko tafad'a rai a b'ace tana janye miemie.Hydar yasaketa yanacin rai.

"Aaton banja" miemie tafad'a tana lab'ewa a bayan ikko.Cikin zafin nama hydar ya janyota ta zunduma uban ihu harsai da gidan ya d'auka.

Shigowar sadeeq kenan yajiyo ihun gwuigwui d'insa da sauri yanufi d'akin twins yasamu hydar na janyo miemie.

Dasauri ya tura hydar "Lafiyarka kuwa hydar! Meya gaminka da yarinyar nan iyee!"

"Haba ya sadeeq meyasa baka ganin laifin yarinyar nan,zagina fa tayi Harda cemun k'aton banza"

"Arya yakeyi ya deeku!"Cewar miemie.

"Nine mai k'aryan!" Yafad'a kamar zai cinyeta

"Eh in" tafad'a tana murgud'a baki.Gadan gadan yayi kanta.

"Badole tak'iraka k'aton banzaba! Kai kwata kwata ba hakuri,ba yarinya bace!"

"Haba ya sadeeq this isn't fear!"

"If you've been ignoring her it wouldn't have come to this stage! Kaf ciki wata raina inba kaiba, rashin hakurin ka da saurin hanu shiya jamaka komai. "

"Fad'a masa kam! " inji ikko.

"Ya deeku na jo kashamun kaya Anje gulin hajjana na fa'a mata!"

"Zo gwuigwina!" Yafad'a yana janyota.

"Bawa yaya hak'uri maza."

*******

Jeeddah♥

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now