In dedication to
Miemiebee 👄
******
"Princess are you with me?"muryar maheer ya katseta tayi saurin d'auke idanunta daga murad tayi murmushi.
"Ina jinka."tana kaiwa nan ta juya ta takalli k'asa bataga murad ba, yanzu shekenan gyalenta zai bak'unci dustbin.
Kusan awanni biyu tsakani tafito daga d'akinta da nufin zuwa gun murad, gaba d'aya jikinta a sanyaye she's very nervous saboda yanayin datake shiga a duk sanda suke tareda emperor.
A hanya takusa cin Karo da sadi dake d'auke da wasu takardu.
"Am sorry ManSadi ban lura bane."
"Ba komai doctor akwai wani abunda kike buk'ata ne."ya tambaya dan kallon yanayinta.
"Umm... Dama inason magana da emperor ne."
Murmushi sadi yayi yace.
"Akwai wani matsala ne Mrs. Emperor?"ya tambaya yana d'aga mata gira d'aya.
"Kacika tambaya ManSadi nikam bani hanya."tafad'a tana harararsa.
Dariya yasa kana ya mik'a mata files na hannunshi.
"Okay am sorry Ms. Emperor,here you go..."
Ta watsa mishi kallo.
"Nayi me dashi."
"Help me deliver these to Mr. Emperor yana study room..."ya damk'a mata yana murmushi
"Why?"ta buk'ata curiously
"I think you two need some privacy..."ya kashe mata Ido d'aya.
Kwad'a masa files din tayi tana harararsa.
"Meye gamena dashi da har muke buk'atan sirri."
"Ke ya kamata ki amsa tambayar bani ba doctor."yayi dariya yabar gun.
Saida yayi nisa ya d'an juya.
"He's very upset right now and I believed ke kadaice zaki iya calming d'insa, please take good care of my boss... Please."ya nad'e mata hannu pleadingly kana yayi tafiyarsa.
Miemie tabishi da kallo rik'eda files baki a bud'e, meh sadisu yake nufi.
Tsaki taja dan maganganunsa basuda wani kan gado, harta isa study room d'in batabar tunani ba, abunda yafaru kwanaki ya dawo mata ta tuna sanda ta mishi 6arna, k'ofar a bud'e yake yabata dama hangoshi tsaye yana Zane gaba d'aya hanlalinsa naga drawing board kamar yana tunanin wani Abu dan yanayinsa zai baka cewa a cike yake.
Kamar 6arauniya ta knocking jikin k'ofar, a hankali ya d'ago kai suka had'a ido take gabanta ya fad'i dan ganin idunsa masu bata tsoro sun sauya kala.
"Is this the right time?"ta murmuring wa kanta.
"Come in."ta tsinkayi muryarsa.
K'arisowa tayi kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta dubeshi tareda runtsa Ido tana gathering courage d'inta.
Files d'in hannunta ne ya su6uce suka zube a k'asa dasauri ta tsugunna tafara tattarowa sai ganin hannunsa tayi yana tayata d'ago fuskarta tayi ta kalleshi hankalinsa naga abunda yake harsuka gama kafun ta mik'e tsaye ta bashi sauran ya juya ya ajiye kan desk.
"Me kike buk'ata?"ya tambaya hankalin sa kan takardun.
"Magana zamuyi."ta fad'a boldly.
D'agowa yayi ya kalli cikin idonta wannan Karon kam k'in sauk'e nata tayi.
Kujera yaja ya zauna tareda crossing k'afa ya had'a hannayenshi idanunsa a kanta.
"Ehm...?"yanuna mata kujera nufin yana jinta.
Matsowa tayi tareda Jan kujeran opposite dashi ta zauna.
"Akan abba ne."tafad'a tana kallo expression nashi.
"What about him?"ya tambaya expressionlessly.
Ta sauk'e numfashi.
"Abba na wasa da lafiyarsa saboda wani dalili Wanda bashida tabbas akai,yanayin hakane saboda gujemun fad'awa matsala, I tried to make him understand babu abunda zaisameni da izinin allah all that matters to me shine lafiyarsa,daga jiya zuwa yau yaki bada had'in kai wajen Samar masa lafiya..."ta dakata tana kallonsa.
"So?"yafad'a bayan ya had'e fuska
"I need you to talk to him pertaining this issue."
"Really?"ya d'aura hannunsa kan desk.
Miemie ta kallesa aranta tana fata ya tayata cause shine kad'ai hope nata.
Tad'aga kai a hankali.
"Baiji na doctor nasa ba saini kika tsammanin zaiji nawa?"
Kallon mamaki miemie kemasa
"But you're his heir."
"Well... If you can't handle your job properly then there's no need for you being in this palace, but don't you ever drag me into this."
"Me kaka nufi? ta tambaya cikin k'unan rai.
"I suggest you should leave kitafi kawai now get out."yafad'a bayan yamik'e ya cigaba da abunda yake.
"But..."
"What the...I said you should leave."ya daka mata tsawa hakan yayi sanadiyar mik'ewarta.
Cikeda takaici tafara magana hawaye nason zubo mata da ranta yayi k'ololuwa a 6ace.
"Okay fine. Am leaving for good."ta juya a zuciye da zummar fice.
Hartakai k'ofa ta juyo tana fuskantarshi idanunsa kan abunda yake yak'i d'agowa ya kalleta.
"Life is unpredictable saboda a kullum mutane suna ganin abun al'ajabi kala kala, factly speaking upon all people I never expected such from you, na d'auka you were the last person that I can seek help from, nasha you will stand with me through this journey but nayi kuskure, kowa a cikin gidan nan halinku d'aya,babu Wanda ya damu da damuwar wani haka kukeso rayuwarku ta d'aure?"
Har a lokaci bai d'ago ya kalleta ba yana abunda yake.
Ta share hawayen ta.
"Ina da burin kawo farin ciki gida musamman Zarah da Amatullah da sukasa hope d'insu a kaina...saboda akwai ingancacciyar hadisin dayayi magana akan haka..."
"Kinyi kuskuren yin haka Doctor saboda you can never put a smile on someone's face..."ya dakatar da ita
"Cause am a fool right? Shirme da shirita yamun yawa right?"tabuk'ata idanunsa a kanta.
"That's for you."ya fad'a a dak'ile baya ya juya ga abunda yake.
Share hawayenta tayi.
"Okay... Am sorry cause nayi kuskuren kawo kaina inda bai gamata najeba, na manta da inda nafito dakuma halayyata nabi yadda tsarinku yake anan, na gode kwarai da kuka fahimtar wani wasu al'amuran rayuwa anan wanda da can ban sansu ba..."
"You're welcome... Now you may leave."yanuna mata hanya har a lokacin bai kalleta ba.
Miemie tajuya da sauri zata bar gun hartakai k'ofa muryarsa ya katseta.
"Not from this room I mean daga gidan gaba d'aya."
Batare da ta juyoba tasa kai tafice da gudu tayi d'akinta.
Kan gado ta fad'a tafashe da wani kuka Wanda tunda take a rayuwarta bata ta6a yiba.
Saida tayi mai isarta ta sannan ta mik'e ta jawo akwatinta ta shiga closet ta fara kwaso kayanta tana zubawa tana hawaye, ita kanta batasan dalilin kukanta ba amma abunda tasani shine tanason cika burikanta data d'auka a nan gidan, duk Wanda yayi sanadiyar kawo murmushi a fuskar wani allah na bashi d'unbin lada, sannan duk Wanda ya ceci ran mutum d'aya tamkar ya ceci ran duka al'umma ne, meyasa sukeson hanata cikin alk'warin data d'aukar wa allah wajen cika su.
Tana cikin wannan yanayin mermu ta shigo d'auke da fruits, ganin abunda miemie keyi yasa tayi saurin ajiyewa tanufeta.
"Doctor me kikeyi haka?"
"Am leaving..."ga fad'a cikin muryarta data dishe dan kuka.
"Why?"mermu ta fad'a bayan ta sha gaban miemie.
Matsar da ita miemie tayi ta d'auko wasu kaya.
"Please don't leave Doctor..."
"And why wouldn't I mermu."ta katseta
"They don't need me here, do they? Kowa anan baya buk'ata ta so I don't see the reason for me staying here."ta wuceta zuwa kwaso wasu kaya mermu tayi saurin dakatar da ita.
"Su kuwa sukafi buk'atarki saboda you're the only person who can bring happiness back into the saddest family..."
"Ni?"ta buk'ata
"Kwarai kuwa musamman PMB."
Miemie tayi murmushin takaici.
"Babu Wanda yake buk'ata na mermu karki yaudari kanki, emperor yafi kowa son nabar nan gidan saboda matsala nake kawowa."ta girgiza kai tareda zama gefen gado tana share hawaye.
Mermu ta zauna gefenta.
"Doctor it's high time for you to know the whole truth about this family..."
"Bana buk'atan ji mermu just let me be."
Duk k'ok'arin da mermu tayi wajen ganin cewa miemie ta saurareta amma ta kiya, k'arshe tashi tayi tafita kamar yadda ta buk'ata.
*******
"Ka tabbata ka mayar da ita har gida."cewar murad da idanunsa suke a lumshe.
Sadisu ya dubeshi da fuskar tausayi tareda kallon study room d'in da Yake a wargaje komai yafita hayyacinsa.
"Ga check nan da iPad ka kai mata."yana kaiwa nan ya bud'e idanunsa dasukayi sauya kala suka koma wani iri yanayinsa ya isa ya nuna gaba d'aya he's devastated.
"Yalla6ai allah huci zuciyarka amma maiyasa ka yanke hukunci Wanda kaima kasan zai cutar dakai, kayi hak'uri."
Murad yayi murmushin yak'e.
"Shine abunda ya dace sadisu, I had to do this saboda lafiyarta yafiye mun komai a yanzu..."
Zai sake magana murad yayi saurin katseshi.
"Banason magana sadisu, kayi abunda nace."yana kaiwa nan ya mik'e yafice.
Sadisu ya girgiza kai cikeda tausayi kafun ya tattara ya gyara gun yad'auki check da iPad d'in.
******
"Gashi yalla6ai yace a baki."ya mik'awa miemie dake tsaye bakin mota shikuma yasa akwatin ta a boot.
Bin abun miemie tayi da kallo kanata bud'e wani d'an card tagani na safe journey abun yabata mamaki sannan da check da iPad.
"Gashi ka maida masa bana buk'ata."ta mik'a masa check d'in.
"But hakkinkine doctor."
"Bana buk'ata ManSadi."ta yi murmushi.
Sannan ta mik'a masa iPad din tace
"Bance ya biyani ba, you can also take it back to him."
Sai card din ta d'ago tayi murmushin dole tace.
"I accept this."tana kaiwa nan ta bud'e baya ta shiga.
Duk abunda ake a idon murad dake tsaye balcony na d'akinshi yana kallo, tana shiga yayi saurin barin gun.
Miemie dake zaune tana kallon sanda yabar gun taji wasu hawaye masu zafin gaske sun zubo mata.
Amatullah da zarah suma suna tsaye hawaye ya wanke musu fuska sai mai martaba da SG suna zaune cikin garden suna kallon komai.
ManSadi ne ya shiga tareda sa wa motar key yafice daga harabar gidan miemie na ma gidan kallon k'arshe.
******
_phewww! Promised fulfilled right? Should I take another brake😁_
_well... Miemie na dab da barin gombe shin suwa sukeso ta dawo ta k'arisa aekinta?_
******
Vote, comment. And share
VOUS LISEZ
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Roman d'amour"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...
