chapter 84

2.1K 177 44
                                    

  In dedication to
  miemiebee👄
 

******
  Daga jikin abba miemie ta yunkura fadi da Sauri ya tallabota da alamar sumace, zaman dirshan hydar yayi a kasa dan kukan ma kasa zuwa yayi, sadeeq ne ya rikeshi tareda dagashi sukayi waje.
Iya tashin hankali babu Wanda basu ganiba, a takaice sanda aka baiwa miemie da meelah gado, babu Wanda baiji mutuwan maheer ajikinsa ba koda kuwa makiyine ballantana bai dashi, ko ina saida abada shaidar yabo akansa, babu Wanda baiji mutuwarsa ba kamaga yan uwa, gurin aiki,yan unguwa da sauran abokan arziki, yayi zaman mutunci da kowa a ko'ina ansonshi saidai mutuwa tayi yankan kauna, mahalliccimu daya fisu sonshi ya daukeshi saidai muce Allah yayi masa rahama.
  Daga hidiman biki ya rikida ha koma gidan makoki dama tuncan ahade ake yan uwa nanan,an tsaida jana'izarsa karfe goma na safe.
  Gida akayo dashi daga asibitin saboda a shiryasa, shashin mahaifinsa aka wuce dashi direct, abban da kansa ya bukaci zaiyiwa dansa wanka ya shiryashi, bayan komai ya kammala akayi kiran ummi tazo tamasa addu'a.
  Da kuka sosae mama tasamu ta janyeta gaban gawan bayan tagama yimasa addu'a, har a kullum maheer cikin shan albarkanta yake, ko sau daya maheer bai ta6a bata mata raiba, yarone mai biyayya,kawaici,hakuri da sanin ya kamata, aka jera maza dubu da wuya asamu goma kwarara masu halin danta,ako ina zata iya bada shaidar haka.
  Kallo daya zakaiwa hydar kasan yana jikin tashin hankalin rashin dan uwa kuma amininsa,shakuwarsu bazai faduba, duk dauriya irinta hydar shima kasa daurewa yayi saida yaimasa kuka dukda yayi kokarin hana hakan faruwa, hakan ta kasance ga mama dan ko kadan maheer baida banbanci da su sadeeq.Har a lokacin miemie bata hayyacinta.
  Jana'izar maheer yatara mutane da dama saboda kyawawan halinsa, mutane na nesa da kusa kowa addu'an samun rahama suke masa, har mutanen da basu sanshiba musamman idan sukaji ranar daurin aurensa ya fad'i,ko ina kaje saidai abaka shaidar kyawawan halinsa ba dai kaji an kushesa ba.
Bayan angama sallatansa akai kaishi gidansa na gaskiya, gidan da dole kowa saiya je,dakyar aka janye hydar gaban kabarin maheer, Allah kasa mucika da imani.
  Tunda meelah ta farfado take kuka kamar ranta zai fita, saida babanta yai mata nasiha mai ratsa jiki gameda kukanda manage baiso saidai addu'a, sannan kuma yarda da kaddara da kuma karbarta hannu bibbiyu alkhairi da kuma sharrinsa... Wanda yafita son maheer ya daukeshi ta rungumi kaddara sannan tabishi da addu'a wannan kukan duk bashida amfani, dakyar akasamu tayi shiru.

*****
Tunda miemie ta bud'e ido take kallon mutane, idanunta a bushe takasa koda magana sannan taki kula kowa saibinsu da Ido, gaba daya tadawo mutum mutumi itadai numfashin kurum take amma komai na jikinta baya functioning,tanajin abunda zaka fada amma sam kwakwalwarta bata dauka.
  Kwananta Hudu cikin wannan halin,batacin abinci bata wanka bare sallah,hakan na matukar damun mutanen gidan,duk yadda sukaso tayi kuka abun ya gagara,kowa yayi iyakan kokarinsa amma inaaa,mutane da yawa sunzo mata ta'aziya saidai ta zuba musu idanu.Kowa ya tausaya mata halinda take ciki,alokaci guda Abu ya taru ya musu yawa kuma koda yaushe mutuwar maheer a sabo yake musu, dakyar da akasamu hydar ya dawo daidai dan yanzu ana zama karban gaisuwa dashi sabanin da saidai ya kulle kansa a daki.mai martaba yazo ta'aziyya kuma ya isa gurin miemie, kallo daya yamata ya dauke kai danya cigaba zuciyarsa zata iya karyewa dan wani mugun tausayinta ne ya kwararo mishi.
  Kwanan zarah uku ta wuce badan tasoba saidai babu yadda ta iya, taso tazauna da miemie a wannan though time amma ba hali a dole ta wuce syprus, ya saura daga sarah sai addah abeedah ne Wanda suke zama da ita ana kusa.
Ayau kwana biyar cif cif da rasuwar maheer, da misalin karfe hudu na yamma hydar yashiga dakin da miemie take daga ita sai Sarah.
  Tasata a gaba sai dura mata tea take ansa mata tsumma kamar baby dan ko bude baki batayi, da spoon take amfami wajen feeding dinta dan a kwanakin nan daga kunu sai tea ake iya bata.
Hydar ya jima tsaye kansu cikeda mugun tausayin kanwarsa, yasan shikansa baiji rashin maheer kamar yadda miemie tayiba, shakuwarsu ta zarta misali sannan ya hadu da batun aure, maheer yayi nisa ya tafi inda bazai ta6a dawowa ba, dolene suyi hakuri su saba da rashinsa dan ya musu nisa.
"Bani hijabinta."yaceda Sarah
Da kansa ya karba yasa mata tareda dagata Sarah ta taimaka masa suka sa mata takalmi.
Hannunta yaja tashiga binsa tiryan tiryan,basu tsaya ko'inaba sai cikin gidansu maheer, har a lokacin da mutane yan gaisuwa hakan yasa sukabi ta baya da taimakon muneer.
Tun shigowansu gidan yanayin miemie ya sauya, sai waige waige take kamar mai neman wani abu, sanda suka tsaya kofar dakin maheer daga inda hydar yake yana iya jiyo bugun zuciyan miemie.
  Sa key yayi ya bude yajata ciki, kamshin maheer ne yafara yimusu sallama, har tsakiyar dakin ya zaunar da ita akasa shima ya zauna yana fuskantarta.
"Miemie kinsan inda muke?"
Batareda ya jira amsarta ba dan yasan ba bayarwa zatayiba ya cigaba.
"This is maheer's room... His own room Wanda bazaikuma shigosa ba har duniya ta nad'e"
Yana lura da yadda take clinching fist dinta hakan ya tabbatar masa da tanajin abunda yake fad'a.
"Maheer is gone why don't you just admit it...he's never coming back... Ever."yadan dakata tareda share hawayensa.
"Duk mai rai mamacine wataran muma zamubar dunian nan, lokacinsa yayi shiyasa Allah'n daya fimu sonsa ya dauke abunsa... What you're doing to yourself is unbearable to us,you're practically killing yourself inside why don't you just cry your heart out. Take the pain out of your heart... Cry.."
Yamike da sauri saboda shima kukanne keson taso masa
"There's a verse in the qur"an that says 'And spend in the way of Allah and do not throw {yourself} with your {own} hands into destruction'. "
Yana kaiwanan ya fice abunsa.
Duk abunda hydar yafada taji, tunda sukasa kafa cikin gidanna kwakwalwarta ya fara functioning, so take tayi kukan amma ta kasa.
A hankali ta mike daga inda take zaune ta isa gurin bedside drawer'nsa tadauko wani frame na hotonsu shida ita tana kallo, kurawa hoton idanu tayi tun tana 18years sukayi pic din a waya...
  Take moments dinsu yashiga yawo akanta, muryarsa, murmushinsa, dariyarsa ya fara dawo mata, ga wayarsa, system da Sauran important abubuwansa hatta kayan daya sa yana kan gado, a hankali hawaye yafara zuba a idanunta, kuka tashigayi a gaggautawa tanayi ta maganganu kamar zautacciya.Wadannan sudden behaviors din dayayita nuna mata kamar Wanda yasan zai mutu especially maganar daya fada mata ranar daya bata diamond ring din hannunta.
_I might die before you so always keep it with you_ a lokacin tanuna masa bataso saidai yayi murmushi kurum yabata hakuri, sannan a gurin mother's Eve kalmar daya fada mata kenan na karshe acikin lafiyarsa _Always stay hopeful cause we never know what tomorrow may bring._ sai a yanzu ta fahimci man mafarkin datayi.
  Kuka tayishi da hawaye na karewa da nata ya kare a ranar, a toilet dinsa tayi alwala tazo ta Rama sallolin da ake binta tareda yiwa maheer addu'o'in da batasamu tayisuba, anan dakin tazauna har dare inda ummi tashigo tana bata baki daganan itama ta 6arke danata sukayi tayi babu mai mai lallashin wani, sanda sukayi mai isarsu sukayi shiru.

******
_AFTER FEW WEEKS_
  A yanzu maheer yayi kwanaki arba'in da rasuwa, rayuwa ta sauyawa yan gidan bakaman daba,very lively. Basa zama tare kamar yadda da suke a zauna gu daya ayi wasa da dariya,kowannensu a dakinsa yake wuni babu walwala kamar da,musamman miemie ita sauyawar nata har tsoro yake baiwa mutane,talkative miemie ta koma kamar kurma, funny, silly and carefree miemie takoma wata iri, saita wuni bayan gaisuwa bazatace da kowa komaiba, wuni take a daki cur, kominta a ciki takeyi.Gidan ya koma kamar makabarta.
Bayan dawowan hajjo musamman tayi tattaki tazo yimusu ta'aziyya, saida ta zubda hawaye ganin yadda miemie takoma, taso tafiya da ita saidai miemie'n taki,badan tasoba takoma.
Yan uwanta sunyi kokari wajen ganin ta koma kamar da amma inaa, hydar yai mata kyautar motarsa datake so,khaleel na yawan zuwa yana janta da tsokana, faruk na yawan bata labarin yan matansa, ammar da muneer na zama su tuna mata yarintarsu, yaa deeku na yawan fita da ita saidai har yanzu babu sauyi.
  Gidansu maheer kuwa ummi ta rungumi mutuwar maheer tadawo rayuwarta kamar nada, dukda kullum saita tunoshi amma take daure zuciyarta, muneer shi kadai ya rage gareta.
  A Dole mama tasa miemie tafito parlor, bayan ta hada man yaranta tana tunanin ko hakan zaisa Sudan sake, jifa jifa suke magana nan ma yaa deeku ne keja dan ganin yan uwan nasa sun sake, khaleel yafi kowa surutu yabiyewa sadeeq suna Jan kowannensu da hira.
Kowa yana magana banda miemie data tsura idanunta gu daya, ta tafi duniyarta can ta daban.
  Ammah ce tazauna kan cinyarta hakan yasa tadawo daga tunanin data fada.
"Anty mumu...kindawo kurmane?"
Bata bata amsaba illa zura mata idanu datayi.
"Where's uncle maheer.... I haven't been seeing him these days."tafada ahankali
Duka hankalin yan parlon ya koma kansu... Ammah tafara kuka tace
"Uncle maheer ne kurum yake sake dariya...please daddy call him."tajuya tana kallon sadeeq
"I want to see her smile...and I also wanna see him... I miss him."tafara kuka sosae.
Miemie ta rungumeta a jikinta tana hawaye.
"Stop crying ammah dear...shhh."
  Faruk ne ya amsheta hannun miemie yayi gaba da ita.

Baba da ya gaji da irin wannan rayuwar dasukeyi ya tarasu tareda musu wa'azi, Yakuma fahimtar dasu ba'a fushi da al'amarin ubangiji, komai yafaru suyi tawakkali.
A ranar yasa hydar ya dauki matarsa suka koma abuja, ammar ya koma school shida muneer, yaa sadeeq shi kadai Yakoma yabar adda abeedah ta haihu anan, faruk ma Yakoma Lagos,yasaura daga miemie sai khaleel da yace sai next week.

   _jeeddah_

Vote, comment. And share

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora