SAUYIN RAYUWA! 👩
written by H. Jeeddher
In dedication to
miemiebee👄
*****
Tundaga nesa miemie ke hango motar dake gabansu,sosae ta k'urawa motar ido ko kyaftawa batason yi,bawai prado ne bata ta6a ganiba aa baba ita take hawa,hasalima yadda take tafiya da yadda ake wasa akan titin da ita,shiya fara janyo hankalinta,sosae drivern ke jujjuya motar yana canza hanya, saizaishiga kwana inyasa signal saiya fasa,da alama bashi direction ake,dan daganin yadda yakeja kasan a rud'e yake,sannan bai bari a overtaking,tuntana Jan tsoka hartafara zage zage,ba ita kad'aiba sadeeq ma yafara jin haushi abeedah kuwa nata Ido, yadda matuk'in ke abunda yaga dama saikace titin ubanshi,kowama akan hanyan yafara k'uluwa,so kawai suke suga waye a cikinta.
Harzata wuce entrance d'in jifatu already sadeeq yasa signal, ganin motar sukayi ta taka burki sai kuuu, saura k'iris sadeeq ya bugi bayan motar sai ya kauce da sauri instead sai ya bugi temporary'n mai fruits gijibbb allah ya taimaka babu mai wucewa takan shoulder, dasauri mutane suka tattaso ganin abunda ya faru.
Immediately duka suka firfito jikin abeedah sai 6ari yakeyi, miemie kuwa tsabar rashin hankali dariya tafara ganin yadda mutane suka rurrud'e, saidai abunda mai motar yayi ya mugun k'ular da ita.
Sadeeq ya glancing kan motar data causing komai, gani yayi ta tsaya, mutane suka fara caaaa kamar Wanda yasuje su rude motar da duka, amma a zahiri gaskiya babu Wanda yayi gigin zuwa kusa da motar saboda ganin plt number'n ta dagani babban mutumne cikinta,hak'uri suka shiga baiwa sadeeq daga maicewa allah wadai,saimai cewa ae dama haka masu hannu da shuni suke sai sutake mutum yadda suka ga dama sannan sukasa bada hak'uri,jinsu suke sunfi kowa amma abun badagan take ba,sai masu cewa yabarsu da allah,murmushi kurum yayi yanuna musu ba komai yagode wa allah tunda abun bai rutsa da rai ba,hannu yayiwa abeedah da miemie alamar su shiga ciki,haushine ya turnuk'e miemie wannan ma ae iskancine,sai da aka kwashi minti biyu sadeeq harya sallami wad'anda yayi wa asara yana k'ok'arin shiga mota.
Bud'e k'ofar driver akayi wani d'an dattijo yafito dagani driver ne rik'eda kud'i a hannunshi.
K'arisowa yayi cikin Sauri ya dakatar da sadeeq dake shirin sawa motar key.
Ganin dattijone yasa sadeeq ganin girmanshi baikamata yayi masa wulak'anci ba,koba komai zai iya haifanshi, fitowa yayi fuskarsa ba yabo ba fallasa.
Dattijon yadubeshi yace
"D'an allah malam kayi hak'uri kuskure aka samu...laifina ne yalla6ai baiso hakanba..."
Dasauri sadeeq ya dakatar dashi
"Babu komai karka damu baba haka allah ya k'addara..."yana kaiwanan yajuya dasauri dattijon yace
"Yaro ga wannan yalla6ai yace arage asara..."
"Yalla6ai yace Arage asara!" Sadeeq ya maimaita a ranshi,daga dukka alamu shi yalla6ai d'inne yajawo shigafi k'arfin yafito yabada hak'uri saidai ya turo kud'i, angaya mishi shi matsiyaci ne, kokuwa kud'i suna kashe matsalar komai,duk asarar daya janyo yana ganin kud'in daya turo shizai sasanta komai sannan ya sanyaya zuciyansu, juyowan dazaiyi danufin cewa yamaida masa baya buk'ata saigani yayi miemie tasa hannu ta wafce kud'in a hannun dattijon.
Ido duka suka bita dashi suna mamaki, sadeeq k'ok'ari yake ya dakatar da ita Dan yanzu miemie zata iya janjamo musu fitinar da babu wanda zai iya kashewa sai Allah, amma ina tariga tayi nisa zuciya ya kwasheta, tafiya take wane namiji saiwani bank'are k'irji take.sosae mutane ke binta da kallo suna mamakinta, masu waya harsunfara sana'a wato d'aukar video.
Idonta rufe gadan gadan tayi kan motar, bata ganin komai gabanta, burinta kawai ta cimma mutumin nan, batare da tunanin komaiba tanufi owners' corner tare da bud'e k'ofan, masifan datayi niyan yi yatsaya cak ta tsura mishi idanu tareda daskarewa agun
kyakkyawan Saurayi sanye da suit gaba d'aya all in black,Idonsa sanye da sunglasses yana danna iPad,fuskarsa Sam babu alamar fara'a,jin bud'e k'ofar da akayi yasa ya d'ago a hankali yaga mai garajen nan.
K'amshin turarensa ne yafara dukan hancinta, take ta lumshe idanu tareda bud'ewa,tunda allah ya halicceta a zahiri bata ta6a ganin mai kyau irinsa ba, fari ne tas Wanda kanaganinsa kaga jinin Fulani, he's indeed a very attractive man,gashin kansa jet black ne ya kwanta luf luf, d'agowa yayi cikeda isa yadube tareda cire glasses nasa rai a mugun 6ace, shid'ewa miemie takusayi ganin oily grey eyes ne dashi unlike nasauran mutanen data sani,su ba k'anana ba su ba manyaba,eyebrows nashi wane anyi carving,idonta ya gangara kan hancin shi Wanda yake a mik'e yayi suiting cute face nashi kana ta gangara kan lips nashi, ya ilahi! Lips nashi reddish kamar Wanda yasa lipstick.k'ura masa idanu tayi ko kyaftawa babu.
ESTÁS LEYENDO
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romance"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...
