In dedication to
Miemiebee👄
Al'amuran miemie na matuk'ar damun mama, ace yarinya shekarta goma sha uku harda d'auri amma babu hankali, idan tayi wani kwab'a sai mutum ya kusa kuka, kwata kwata bata iya magana ba wane daga duwawu ya fito ba a baki ba, idan tana yiwa babba magana zaka d'auka rashin kunyane amma ba haka bane rashin iya magana ne tsaba,bata duban girman mutum take ya6a masa magana, uwa uba abunda yafi damun mama shine d'abi'un ta, idan tana abu wane namiji, kwata kwata wasan banza da tsalle tsalle yafi k'arfinta,ko wajen murya idan tana magana yadda kasan fashasshen ganga,da gaske take bud'e murya, tafiya kuwa in suka jera da ammar kafun yayi taku biyu tayi goma, kwata kwata kominta a hargitse take yinsa saidai Alhamdulillahi bata wasa da karatu both Islamic da boko cos mama a tsaye take.
Mama ce tanufi dakin miemie kaimata wasu Kaya datasa aka dinka mata, atamfa kala uku sai materials kala biyu,dan yanzu kam tsayawa sosae zatayi dan ganin miemie ta canza.As usual yauma kamar kullum tundaga bakin k'ofa tafara cin karo da kaya,unifoam na islamiya ya tarar dana boko duk ta watsar dasu,school bag nata harta da sandals nata a tsakiyar d'akin ta watsar.
Kwance take ta babbaza k'afa tareda hangame baki tana baccin asara, gabaki d'aya kayan guga ne cike kan gadon da tunda aka shigo mata dasu sunanan yadda suke saima d'aura k'afafu datayi akai,gabaki d'aya sun fita hayyacinsu dan mama tabhana ikko yimata komai acewarta ta fara girma tayi komai da kanta,ga books nata data gama assignment duk suna kai.
K'arisawa tayi cikin d'akin tana girgiza kai cikeda bakin ciki,d'aga kai tayi tadubi agogo 7:07pm tayi imani miemie batayi magrib ba ga isha ta gabato.
Zuwa tayi bakin gadon ta ajeye kayan hannunta tana k'iran sunanta cikeda haushi."Miemie! Miemie!!"Ina yadda kasan gawa bakinnan a wangale ko motsi batayi Allah ya taima keta bata yawun bacci.Tapping cheek nata tafara tana Kiran sunanta.
"Uhummm!" Tasake gyara kwanciya tareda juya mata baya ta wangale kafafu.wani haushi ne yakama mama batasan lokacin da ta tak'ark'ara ta zuba mata naushi a gadon baya ba.Wani gigitaccen ihu miemie tasa tana neman hanyan gudu dan ta mugun firgita ta,wani uban tsalle ta daka saida takusan kayar da mama."Wayyo Allah mamana!" Hannu mama tasa ta ruk'ota da zaunar.
Sauke numfashi ta fara don dama setan k'ofa tayi zata arce. Rik'e k'ugu mama tayi tana kallonta rai a b'aci.
"Kai! Maa wallahi you really scared the hell out of me!" Tafad'a distressfully tana sauk'e numfashi tareda mik'a.juyawa tayi tana kallon mama Wanda har a lokacin kallonta take cikeda b'acin rai."A'ah maa ya kin tsaya kamar statue? Any probs wani abune ya faru?" Tafad'a zata gyara kwaciya.
Haushine ya dad'a kama mama "Kika kuskura kika kwanta zan mugun sa6a miki! Ko ance miki nashigo mahaukacin dakin nan dan nazo nayita kallonki ne!"Da sauri ta gyara zamanta tana gunaguni
"OMG! What is it again?"Ran mama in yayi dubu ya 6aci, kasa magana tayi tana kallonta
"Kalli agogo!" Tafad'a a tak'aici.
Miemie ta d'aga ido takalla "7:11pm! What's wrong with the time maa?"
"Ubanki ne!" Tabata amsa cikin bacin rai.
Miemie ta 6ata fuska tana tura baki."There you go again maa, what have I done this time around?"
"Da lafiyarki kuwa miemie? can't you at least once kiyiwa kanki fad'a, kwata kwata ke bakya aeki da hankali, tell me what exactly is wrong with you?"
Kallo miemie tabi mama dashi tana tura baki"Gaskiya maa must you always have a reason to scold me? n...."
"Will you shut up before I slap the hell out of you!" Tafad'a tamkar zata bugeta, da Sauri miemie ta matsa."I asked you to look at the time but still common sense naki bai baki abunda yakama bako! C'mon wuce kiyi alwala joor!"
"Ohhh! Ashe banyi sallah ba Haushi ya kama mama anya wannar kanta d'aya kuwa.
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romance"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...