In dedication to
Miemiebee 👄
"Kin tabbata babu abunda ya ta6a lafiyarki?"
"Ko saina tabbatar maka ne! Are you ready for a fight?" Tafad'a tana dunk'ule hannu.
Dariya sosae tabashi har yakusa hawaye.
"No noo! Ban shirya ba, muje abba na jiranmu!"
Jerawa sukayi suna tafiya, kafun maheer yayi taku biyu miemie tayi hud'u kamar wacce ake janta Dole maheer ya d'aga k'afa sosae dan ya kamota.
Mutane da dama gulmarsu sukeyi,wasu sunajin haushin yadda maheer ke matuk'ar kulawa da miemie dayadda yake biye mata suyita shirme da dariya sa6anin sauran, musamman mata ko sun mishi magana wani sa'in ba kulasu yakeyiba,bai cika sakar musu fuskaba har gwara maza, gashi wani farin jini allah ya mishi, mata dayawa sun nuna suna sonshi hakan ne ma yasa bai sakar musu fuska, Sam bayason zak'ewan dasukeyi akanshi.
Wasu cleaners biyu dake gefe suka fara gulma.
"Kaltum ni meye tsakanin Dr. Maheer da wannan mahaukaciyar?"
"Wace mahaukaciya?"
"Dr. Miemie mana, yo ae babu marabarta da marasa hankali,dubanta kawai in mutum yayi yasan sabuwar kamuce dukda a jiki kam batada makusa, duba ga irin shigarta da dabi'unta,sannan abun mamaki duk yadda Dr. Maheer yake had'add'e kuma miskili amma yarasa wacce zai kula sai ita, kiga irin sonda sister meelah ke mishi amma ko kallo bata isheshi ba,kullum wannar ta6a66iyar tana manne dashi,insuna tare kurum nake ganin dariyarshi"
"Ohuhu deejah! Ganemun hanya wai makaho yaso gulma,Waya gaya miki cewa soyayya suke, Dr. Miemie 'yar uwarsa tare suka tashi,shak'uwace kurum tsakaninsu,Ke a tunaninki Dr. Maheer zai iya tarayya da wannar ta6a66iyar ne,kinsan hakan ba mai yiyuwa bane, dan ni banga banbancinta da wani namijin ba, ae duk namijin da sister meelah tace tanaso ba k'aramin can6awa yayi ba dan yagama yin dace.
"Amma ke a ganinki yana kulatane, kiduba duk shisshigemasa da takeyi ko fa kallo bata ishesa ba,kiga yamun inba soyayya yake da Dr. Miemie ba babu abunda zaisa yana share sister meelah...
"Kedai bar zancen abunda bakida tabbas akai, yanzu dai muzuba Ido dan ni 'yar abi yarima a sha k'idace, ayine mugani mukuma baza a gari..."
"Hhhh shegiya kaltume bakida dama, kinsan ni 'yar kwashe labarice, nikekaiwa sister meelah updates kedai duk abunda ya faru kika gani sanar dani cikin gaggawa...
(Oh allah rabamu da munafukai).
Maheer da miemie kuwa sun tarar da abba a office d'insa bayan sun zauna
Abba yadubi miemie yace
"Maryam wani alfarma akazo nema nan asibitin kuma ke kad'ai zaki iya taimakawa."
Cikeda alamun tambaya take duban abba.
"Ni kad'ai?"
"K'warai kuwa!"
"Tayaya kenan abba?"cewar maheer yana mai dubanshi.
Abba ya numfasa
"D'azu wasu bak'i sukazo suka sameni ciki harda wazirin masarautar gombe, I was surprised when I saw them saboda banta6a tunanin ganinsu anan ba,kuma sun taho neman alfarma,sarkinsu ya samu matsala a k'afofinsa Wanda har baya iya motsasu na tsawon shekaru shida, nayi mamaki k'warai da jin hakan, i once heard about the incident but banta6a tunani zaikai warhaka bai samu lafiya ba dukda komai ikon allah ne,nayi tunani a lokacin in aka kaishi waje cikin watanni k'alilan zai iya ya warke gaba d'aya saboda dubaga kwararrun likitoci da kayan aeki dasuke dashi,banyi k'asa a gwuiwa ba wajen tambayar su shin anyi maganine bai warke ba ko kuma kwata ba'ayi wani abu a kaiba, abunda wazirin ya fad'a ne ya d'auremun na cewa sarkin shida kanshi yak'i yarda a fitar dashi,kwata kwata yak'i amsar kowa irin treatment kama daga na asibiti zuwa na gida, dakyar ya yarda aka bashi na wata d'aya daganan yak'i,ya avoiding exercise hakan yayi sanadiyyar nakasan shi,tundaga lokacin ya baiwa d'an uwansa rik'on k'warya na tsawon shekarun nan,yanzu kuma bansan dalili ba amma ayarda sukace sarkin da kansa yanemi samun sauk'i wanda hakan yasa sukazo nan and I promised to help them bisa yarjewarki dana iyayenki.
"Abba tayaya zan iya taimakawa kenan?"
"They're desperately in need of a physiotherapist!"
Duka suka zuba masa Ido,miemie tace.
"Abba kai meh zaka iya yi kenan dasukazo gunka nikuma taimakon meh zanyi?"
"Your services are called!"
Zaro idanu tayi waje.
"Ni kuma??"
"K'warai kuwa maryam kece kad'ai nake ganin zaki iya taimakawa kibada gudunmawarki wajen warkar dashi da ikon allah,a k'arshe zaki samu d'unbin lada wajen taimakon.
Karo na farko a rayuwar miemie dataji zata iya taimakawa kai tsaye wholeheartedly.
Abba yace
"You're my daughter maryam,babu banbanci tsakaninki da maheer a guna, kinsan uba bazai iya yanke hukuncin dabai yarda dashiba kan 'ya'yansa, bazan ta6a yarda kije inda zaki cutu ko ki wahala ba,taimako zakiyi kuma allah ne kad'ai zai iya biyanki..."
"Abba na sani! You don't have to say that, I'll definitely do whatever you asked me to,bazan baka kunyaba."
Maheer ya k'ara
"I trust her abba, she'll never failed us besides she's the most youngest and talented physiotherapist in the whole of this state..."
Abba yaji dad'i k'warai.
"Nagode maryam allah ya yimiki albarka amma a tunanina nayi ragon azancin yarje musu danayi batare da na nemi yarjewar babanku da mamanku ba..."
Maheer yace
"Ae lokaci bai k'ure ba abba, zaka iya yiwa baba magana dukda nasan he'll definitely agree to it inayaji bayaninka..."
"Absolutely!" Cewar miemie
Abba yayi jim kana yace
"Alright insha allah masa magana! Zaku iya tafiya,sainaji amincewar su zan nemesu."
DU LIEST GERADE
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romantik"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...
