chapter 66

2.3K 188 60
                                        

In dedication to
Miemiebee 👄

******
   Wasa gaske tun anasa ran ganin dawowan murad da miemie har k'arfe goman dare basu ba labarinsu, hankalin kowa inyayi dubu ya tashi musamman da aka nemi sadisu shima shiru babu labarinsa.
Zaune kowa yake a babban falon mai martaba anti zugum tareda wazeeri da iyalansa sai hakimi da matarsa hajia laelah.
Hajjo,zarah,amatullah da jaleelah sunci kuka har sun gaji.
Mai martaba kuwa gaba d'aya magana ma ya kasa dan jikinsa ne yayi mugun sanyi yana tsoron kar wani Abu yasamu murad kamar sauran 'yan uwansa, ga mariam itace babban damuwarsa ayanzu yanda yad'agota gaban iyayenta yake fatan yamaida ta lafiya.
"Ga irinta nan yaro Sam baijin maganan kowa da yana tareda securities da duk hakan bai faruba,gashi yakai kansa ga hatsari mu kuma yasamu cikin damuwa..."cewar hajia laelah tana tura dankwali tareda kauda kai.
Hajjo ta d'ago da jajayen idanunta ta dubeta tace.
"Su securities din sun isa su hana abunda allah ya riga ya tsarane? Insha allahu d'ana bai cikin hatsari zai dawo gida lafiya, furta alkhairi ko kayi shiru shiyafi dacewa a yanzu..."zarah tayi saurin dado kaf'ar hajjo hakan yasa tayi shiru.
Hajia kalthum dake gefe tace.
"Komadai menene tayi gaskiya, komai shiya jaaa, meyasa tun farko bai sanar da kowa inda zashi ba ya yayi6i karuwar likitan nan, k'ilama wani bushasharsu sukaje yi..."
"Kathum..."wazeeri ya tsawatar mata.
"Allah ya tsaresu da mugun baki..."cewar hajjo
  "When did you start caring for your children dahar zakiyiman rashin kunya iye?"cewar hajia laelah
Sai a sannan mai martaba ya d'ago ya dube hajjo da t kasa magana yace.
"Khadeejah ya isa haka...duk wannan cece kucen bai tasoba addu'arku shi sukafi buk'ata a yanzu..."
  Hakimi dayafi kowa nuna damuwarsa ya gyara murya yace.
"Ku kwantar da hankalinku murad da mariam ba yara bane duk inda sukaje da izinin allah zasu dawo, mudai muyita addu'a allah yasa lafiya..."
Hakimi yadubi hajjo yace
"Khadeejah murad ko mariam wani bai sanar dake inda zasu ba?"
Hajjo ta girgiza kai
"A"ah bappah hakimi, murad bai ta6a fita batare da ya sanar dani inda zashi ba sai yau... Mariam kuwa tunda tazo bata ta6a barin cikin gidannan ba..."tak'arishe hawaye na zuba.
"Koda kuwa akwai Wanda zai iya sani saidai sadisu,dan ba ko ina bane yake barin wani soldier ya bishi saidai in nasashi dole saboda lafiyansa, gashi shidin ma tunda safe ba'a sake d'uriyarsa ba."Cewar CS dake muzurai yana kallon hakimi.
Jalal d'aya gwada wayar murad for the hundredth time ya girgiza kai yace.
"At least da ansamu layinsa hankalinmu zai kwanta, wannan lamarin is out of hand I think yakamata asanar da corps..."
"Co... Corps? Kar ayi hanzari jalal insha allah zasu dawo..."cewar wazeeri
"Wazeeri jalal yayi gaskiya for how long zamuyita jiran dawowansu batare da an d'au mataki ba..."cewar SG da shima hankalinsa a tashe...
Hakimi ya gyara malum malum dinshi yace.
"Baza'ai hakaba,ya kamata a dakata tukunna, yanzu ana sanar da 'yan sanda labari zai bazu kamar hayak'i saikuma ya juye zuwa wani abun daban kasan sha'anin mutane, a dakata zuwa gobe idan ba'aga dawowarsu ba sai a d'au mataki...kuma koda ba'a jiba CS ne zasu fara bincike bamasan maganan nan ta fita."cewar hakimi tareda mik'ewa.
Duk abunnan dake faruwa mai martaba baice komai ba sai idanu dayake binsu dashi shi kad'ai yasan abunda ke ransa.
  Bayan fitan hakimi wazeeri yabi bayanshi suka fita tareda jalal...
Hajia laelah ta mik'e tana wani yatsina tayi gaba hajia kalthum itama tamik'e.
"Kukan ya isa haka tunda bashi zaisa ya dawoba sai ki tashi mutafi aeko..."taceda jaleelah
Jaleelah ta tura baki tareda sakin wani kuka
"Ni babu inda zani kiyi tafiyarki kawai..."
Bata sake magana ba sai wani kallo data watsa mata itako takauda kai...ficewa tayi hajjo tabisu da kallo tanajin zuciyarta na mata wani d'aci.
Zarah da amatu kuwa zugun sukayi suna jimami dan aganinsu babu wanda yakaisu damuwa.
   SG ne ya tura mai martaba zuwa d'akinsa a hankali kowa ya mik'e ya nufi makwancinsa...
Ranar babu Wanda yayi bacci munafukai suna murnar victory nasu while su hajjo sunakan buzunsu suna add'uar allah baiyana su murad cikin koshin lafiya.

********
  Duk wasu members na fadan gombe da king makers sun halarta falon mai martaba anti zugum.
Tun tashi sallar asuba'i mai martaba yayi k'iransu dukda hakimi baisoba yarasa dalilin dayasa tun jiya mai martaba yake acting very strange amma yadake bai nuna alamun damuwaba ko k'adan.
Abunda ya d'urewa hakimi kai hard a chief constable (
The head of the police force) da muk'arrabana sunzo.
Bayan ya isar da gaisuwa gun mai martaba da mutanen gurin akai masa nuni d'aya zauna.
Tsakanin hakimi da wazeeri kallon kallo ake wannan ya kalli wannan wannan ya kalli wannan allah sa mai Martaba murabus zaiyi.
Galadima dan dattijo dayafi kowa manyanta dan zai iyakai shekaru tamanin a duniya mai martaba yace.
"Ranka shi dad'e allah yak'ara maka girma, kataramun anan gashi kowa ya halarta har yanzu bakace komaiba..."
Mai martaba yasauk'e ajiyar zuciya kana yadubesu d'aya bayan d'aya, duk a gurin fiye da rabi sun girmeshi.
"Na taraku anan ne saboda na sanar da ku abunda ke faruwa acikin gidannan..."
Duka suka fara dubanshi wannan yakalli wannan har daga k'arshe suka tattara nutsuwarsu suka maida kansa.
"Nad'auke kai gameda abubuwan dasuke faruwa agidannan na tsawon lokaci...basaina fad'a ba kunsan komai tunda kan mutuwar 'ya'yana maza hud'u dakuma nakasar da nake ciki a yanzu..."
Kowa ya jinjina kai,hakimi da wazeeri suka had'a idanu...
"Banyi bincike ba tun fari saboda Wanda ina ganin hakan shine babban kuskuren da nayi,anyi amfani da nakasar danayi wajen musgunawa iyalaina tareda hanasu zaman lafiya da walwala duk na d'auke kai na amshi jarabawa ta hannunta bibbiyu saboda nayi imani mutuwa bata iya d'aukar kowa sai lokacinsa yayi...Na yarda daku dukan ku musamman bappah hakimi na yayana d'an uwana wazeeri, bana iya 6oyewa kowa komai a cikinku sannan bana iya yin komai batareda na nemi shawararku ba hakane?"
Duk sukayi shiru kowa na zuru zuru da idanu musamman hakimi da wazeeri da zufa ya fara karyo musu.
"Ko bani amsa?"ya buk'ata
"Hakane ranka shi dad'e allah yaja kwana..."suka fad'a a tare.
Mai maitaba ya sauk'e numfashi kana ya bisu da kallo d'aya bayan d'aya, in a low tone yace.
"Shin Na ta6a tauyewa wani hakkinsa cikinku? Shin na ta6a musgunawa waninku?"
Sukace amsa da a'ah
"Madallah... Meyasa ni kukeso ku tauyemun nawa hakkin? Meyasa kukeson musguna mun ku k'untata mun haryazama ajalina?"
Da mamaki koqa ke mamakin furucinsa,ya girgiza kai yace.
"Ina sane da duk abunda ke faruwa a cikin gidannan dasa hannun wasunku a ciki..."
Kowa sai muzurai yake yana kallon dan uwansa...
Hakimi har ya had'a zufa amma ya fusge,wazeeri sai zare idanu yake.
"Murad shi kad'ai gareni a yanzu shine magajina,ina rok'onku da girman Wanda ya halicce ku a sannu duk Wanda yakeda hannu a 6atan murad da Dr. Mariam ya fitar dasu tun kafun na d'auki kwakkwaran mataki akai..."
Tunda suke basu ta6a ganin mai martaba cikin wannan halin ba,komai nasa ya sauya lokaci guda tsantsar mulki da sarauta ne a tattare dashi yanzu, duk sun tsorita dayanayin da yake ciki yanzu.
  "Nasan da yawanku a yanzu kun d'auka murabus zanyi..."ya girgiza kai
"Sarautar kasannan da izinin allah jinina zaiba dan da shi nake tare... Allah ba azzalumin bayinsa bane dazaibar al'ummansa hannunta azzaluman dasukeson rushe abunda akayi shekara da shekaru ana ginawa....Abu d'aya nake buk'ata a yanzu, nan da minti uku inaso ya sanar dani inda 'ya'yana suke..."
  Tohfah nan hayanaya yatashi kowa sai zufa yake yana tofa albarkacin bakinsa...hakimi kuwa gaba d'aya a tsorace yake da ganin yadda babu sauk'i a tattare mai martaba sarauta ta motsa...gaba daya gurin an tsorita dashi.
Bayan giftawar minti biyar bakajin komai sai k'aran AC kowa yayi tsit.
Mai martaba yayi dan murmushi yadubi chief constable yace.
"CC inaga zan maida hannunka a yanzu... Na yarda dakaine shiyasa zanyi hakan, na baka izinin yin bincike mai tsauri kan kowa a cikin fadar nan harsai murad da mariam sun bayyana,this is an order..."ya yi magana cikin d'aga murya Wanda hakan ya matuk'ar girgiza duk wani rai dake zaune a gurin.
Wazeeri ya mik'e cikin k'unar rai yace.
"Haba yalla6ai ya za'a haka... Shin kakuwasan me kake cewa wato bakayada damu ba kamar yadda kafad'a a baya,ta yaya zamu cutar da kai, katuna nifa dan uwankane na jini koda za'ai bincike kan kowa baikama ayi akanmu da hakimi ba..."
Mai martaba yayi d'an murmushi
"Zan iya cewa d'an uwanka na zai iya k'inka fiye da bare,ko kamanta uwarmu na d'aya ba? Kuma nasan ka sarai... ban ware kowa cikinku ba sai a bincika koda kuwa hakimi ne... Dan nafisa kokonto kanku ku biyu..."
Hakimi ya mik'e cikin fushi yace
"Banyi tsammanin haka agareka ranka shi dad'e na d'auka ka d'aukeni matsayin uba kamar yadda na d'aukeka a d'an cikina taya kake tunanin zan aekata wannan aekin duk k'aunar murad danake baka ganiba har zaka d'aura kokontonka a kain..."
"Zuciya bata da k'ashi ko ka manta? Zuciya kowa da irin tasa saboda haka bazan iya fayyace abunda ke ranka ba."cewar mai martaba yana kallon cikin idunsa
Da sauri yakauda kai yana huci, lalai yau akwai abunda ke damun abdulazeez bai ta6a ganinsa hakaba.
"Bana buk'atar jayayya... Bincike ya sauk'a akan kowa cikinku... Afito mun da 'ya'yana ko na fito ta wani hanya daban."
Yanakaiwanan yayiwa sarkin gida hannu alamar yashiga dashi har zai juya saiga wata murya yayi sallama cikin fad'an hakan yasa shi juyowa duka suna kallonshi kowanne idanunsa a kansu sunai masa kallon mamaki.
k'arisawa yayi gaban mai martaba ta tsuguna tareda rik'o hannunsa.
Ahankali ya fara shafa kansa yanajin wani farin ciki a zuciyarsa na ganin tilon dansa.
"Murad kaine?"
"Nine abba...kayi hakuri na tayar muku aka da hankali."ya danyi murmushi.
  Zaiyi magana yayi saurin dakatar dashi
"Kwantar da hankali abba she's with me..."
  Nan fa aka dan fara hayaniya wasu suna farin cikin bayyanarshi.
Hakimi kuwa wata muguwar zuface tafara karyo masa duk sanyin AC'n dake d'akin bayaji, kansa gaba d'aya juyawa yake yakasa gaskata abunda idanunsa ke gani, murad din da aka tabbatar masa da cewar ya mutu har hoton gawansu yagani shine agabansa ko kuwa fatalwa...
  Bayan hayaniyar ya lafa wazeeri yace
"Ga irinta nan ae,ka zargi mutane akan abunda basuda masaniya akai..."
"Language bappah wazeeri..."cewar murad bayan ya d'aure fuska duka aka dubesa da mamaki baki bud'e.
"You have no right to talk to my father with this tone... He's the king of this palace not a commoner. So ka kama harshenka..."ya fad'a yana kallon cikin idanunsa.
Ahankali wazeeri ya sulale ya zauna mamaki bai gama sakeshi ba, kallon inda hakimi yake yayi halin daya Ganshi ciki yasa jikinsa yin mugun sanyi.
CC ya tambaya ko zai iya tafiya tunda murad ya bayyana.
"Ka d'an dakata saboda akwai masu maka rakiya."
Dam dam dam...zanso kuga idanun hakimi da wazeeri LOL.
  Da hanzari hakimi yamik'e yana gyara malum malum dinsa tareda dakewa yace.
"Alhamdulillahi tunda allah yasa ka dawo lafiya...inada uzurin da zanyi yanzu sai anjima..."
Da sauri murad ha tare gabansa tareda smirking yace.
"Wani uzuri ne yafi maka farincikin dawowata gida lafiya..."
Ya nad'e hannu a k'irji yana dubansa cikin ido.
"Bazaka tambaya ina nafito ba? Ko kuwa kana tunanin fatalwa ka gani a gabanka?"
Rai a 6ace hakimi ke kallon murad dake watsa masa wani mugun kallo.
"Banason shashancin banza,rashin kunyar taka yanzu kaina ta gangaro."
Popping baki yayi waje tareda girgiza kai yana murmushi ya rik'o hannun hakimi ya zaunar dashi kana yace.
"Allah ya huci zuciyarka, gani bayi murad dinka ne gabanka kuma baka nuna farincikin ganina ba kamar yadda kake nuna kana k'aunata fiyeda kowa..."
  Jin haka yasa ya koma ya zauna yana k'ok'arin daidaita nutsuwarsa.
Murmushi kurum murad yayi.

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now