chapter 36

1.7K 143 21
                                    

In dedication to
Miemiebee 👄

******
10:30pm

Zaune take sanye da pajamas baby pink gashin kanta duk yagama yamutsewa wani ya zubo mata fuska,ta nad'e k'afafu a tsakiyar gado tareda rafka uban tagumi bakinta a ture tak'ura wa iPad nata dake ajiye kan pillow a gabanta idanu kamar zata fashe da kuka.
Runtse Ido tayi tareda Jan tsaki,yanzu suka gama video call da maheer yai mata sallama dan a asibiti zai kwana, sake duba time tayi, yanzu tasan 'yan gidansu sun kwanta, Sarah ce ta fad'o mata rai, da sauri tajawo wayanta tareda dialing number'n Sarah,kusan sau biyar tana k'ira bata d'aukaba, tsaki takuma ja Karo na saba'in da uku, jawo bargo tayi tareda ture kayan data cire ta lullu6e kanta, runtse Ido tayi tanason bacci yazo amma inaa, wannan wani irin rayuwane akeyi anan gidan, tun zuwanta tafita ta zaga cikin gidan kusan sau bakwai amma bayan masu aeki bataga kowaba, ma'aikatan ma kansu a k'asa babu Wanda ya kalleta, tayi tambayoyi amma babu wanda zai kulata, a d'aki aka kawo mata abinci, harlokacin bata sake ganin mermu ba balle sud'anyi hira, itafa bata iya zama gu d'ayaba sa'annan bakinta baya iya shiru na minti talatin amma yau yaugata a gidan kurame, Wanda babu mai shiga hark'ar wani kowa sabgar gabansa yakeyi, tasaba gidansu tare suke cin abinci, suyi hira suyi kallo suyi wasa dukansu,take taji kewan gida ya kamata,amma nan tun k'arfe takwas taji gidan yayi tsit,tashi tayi zaune gabad'aya tagama hargitsa gashin kanta.
Mik'ewa tayi tsaye ta koma k'asan ta kwanta flat tareda d'aga k'afafunta sama tafara exercise,tayi wannan tayi wancan harta gaji,yanke shawaran fita tazaga cikin gidan tayi kozai d'an d'ebe mata kewa kafun bacci yazo, duba agogo tayi taga sha d'aya ta d'an gota,batareda tasa takalmi ba ta d'auki headphones nata ta rataya a wuyanta tareda d'aukan iPad nata a hannu tanufi k'ofa, tana dab da bud'ewa ta ta6a kanta taji babu d'ankwali harta basar zata fita ta tuna hud'uban mama, dasauri ta koma tad'auki hularta ta Sanya batareda ta gyara gashinba saita zama tamkar wata dodo gashin ya rufe mata fuska,murd'a handle na k'ofan tayi tareda lek'a hallway d'in, dim light ne babu haske sosae, babu ko alamun rai agun, ahankali tafito tana lek'e lek'e, tafiya tahauyi batare da tasan inda zatajeba, kunna wak'a tayi a kunnenta tana tafiya tana kad'a kai, kowani falo tagani saita Shiga, duk abunda ya burgeta kuwa saita d'auki hotonsa,take ta fara nishad'i tanajin dad'in tafiyanta, wani dogon corridor ta hango ta gefen damanta, bin hanya tayi tana lek'e lek'e, wani k'ofa tagani tagefe guda, mamaki tayi ganin a keb'anci da sauran d'akuna yake sa hannu tayi tareda bud'ewa a hankali tana lek'a kai, makeken kitchen ne a gun, sa hannu tayi tana laluman makunnin wuta taci sa'a kuwa ta samu tareda kunnawa take d'an dim. Light ya mamaye kitchen d'in dukda ba wani haske sosae bane.
"Wow!" Tafurta breathtakingly baki a bud'e
IPad nata ta d'ago tafara d'aukan selfies,ashe kitchen d'inma suna suka tara.
Babbane sosae kuma ya k'ayatu ba k'aramin burgeta yayiba gashi ko ina neat.
K'arisawa tayi tahau bud'e bud'en drawers bayan tagama kalle kallenta ta hangi magic warmer a gefe guda, Dama ance hali zanen dutse miemie bata fasa hali ba ta nufi warmer'n nan tareda bud'ewa zaro idanu tayi fuskarta d'auke da murmushi har hak'waran ta suka fito ganin chicken shawarma, take ta had'iye yawu kutt jin aroma tana kallo, wani mugun kwad'ayin ci takeji, harta sa hannu zata d'ago ta tuna bafa a gida take ba, cize yatsa tayi tana tunani, kullum mama saita kwa6eta kan d'aukan abunda ba'a bataba, tunowa da hud'uban mama tayi akan kwad'ayi, harta rufe zata juya saikuma ta fasa a hankali tace mama am sorry tareda cire headphones mata ta ajiye iPad a gefe kana ta bud'e, lumshe idanu tayi tana perceiving aroma d'in,sa hannu ta d'ago tahauci,saida tayi rabi tana k'ok'arin cusa wani a baki taji k'aran k'ofa,daskarewa tayi ita bata kai bakiba ita bata ajiyeba sai muzurai take.
"Mekike buk'ata Dr." Ta tsinkayi murya daga bayanta.
Jin mermu ce yasan ta sauk'e ajiyar zuciya bakin nan duk ya 6aci,da sauri ta ajiye tareda juyowa.
"Ohh mermu kece!"tafad'a sillily tana Sosa kai.
K'arisowa tayi ciki murmushi d'auke a fuskarta.
"Akwai abunda kike buk'ata ne, tund'azu kinata yawo..."
"Umm well umm nothing kawai bacci ne baizoba so kawai na deciding na fito nad'an zaga."
"I wonder yawon me kikeyi at this time of the night,allah yataimaka an yi saurin ganeki kuma ke bak'uwace da kinshiga mummunan matsala musamman ganin kinshigo kitchen kuma kusa da abincin PMB shiyasa akace na zo na duba no lafiya...akwai abunda kike buk'ata ne?" Tafad'a tana matsowa.
Tunda mermu tafara magana miemie ta k'walalo idanu waje, tunda take a rayuwarta bata ta6ajin ta rud'e akan Abu ba sai yau jin shawarman prince murad takusa cinyewa,haka kurum taji cikinta ya d'uri ruwa,da kuma ya akayi akasan tana yawo a cikin gidan Bacon tasan babu Wanda taci Karo dashi da alama kowa ya kwanta a lokacin Dan sha biyu saurane,yau ga abunda kwad'ayi yaja mata.
Kasancewar kitchen d'in dim light ne yasa mermu bataga bakin miemie ba,a d'an tsorace miemie tace
"Ya akayi kuka...
"Ya akayi mukasan kin fito ko?"mermu tafad'a tana 'yar dariya.
"Well,akwai CCTV camera a ko ina a palace d'innan except d'akuna ansa tsaro a gidannan sosae musamman hallway dan ganin abubuwan dake faruwa,ana kashe wuta tun k'arfe goma kinga dole ganinki yasa a zargi wani Abu,akwai securities dasuke gadi cikin dare,abunda yasa ba'a kunna alarm ba coz daganin yadda shigarki yake gakuma abubuwan hannunki yasa aka gane kece bak'uwar mai martaba,shiyasa akace na tambayeki koda abunda kike buk'ata." Tafad'a tana mata murmushi.
"Dama hajjo tace nashirya abincin PMB coz by 12:15am zai Iso palace yanzu haka suna hanya shigowa nan, so anytime hajjo zata iya shigowa dan duba abunda na shirya kafun ManSadi yakai mishi."mermu tafad'a tana neman asalin switch na wuta.
Miemie da cikinta yafara rawar shoki ta gwalalo idanu yau ta shiga taranta.
Mermu na kunna wuta tace
"Tunda babu abunda kike buk'ata yaki iya komawa idan kuma Abu yataso you can call me through landline coz fitowanki cikin dare zai iya jawo mini hatsari bab..."
Kasa k'arisa maganan tayi ganin bakin miemie dake tsaye tana muzurai gashi duk yagama rufe mata fuska saura kad'an mermu ta zura a guje,da mamaki take kallon ta.
Baki na rawa tace
"Dr. What...what have you done?"
Miemie tasa hannu a baki tana cizam yatsa tace.
"Umm. Am really so...sorry.I...I made...a very big mistake"tafad'a ruefully tana cin yatsa.
Mermu tayi shiru tana kallonta can tace.
"Dr. You should have told me kinason shawarma the chef would've made it for you, aunty jaleelah made this specially for PMB shiyasa hajjo tace ta serving masa immediately yana dawowa,yanzu what would I tell hajjo..." Tafad'a duk tagama gigicewa.
Ganin halin datashiga yasa miemie tausayinta,imani yafara shiganta dasauri tace.
"I'm terribly sorry mermu, l don't know what to say Dan banida wani hujjan kare kaina, karki damu I will explain it to hajjo,kuma yanzu zan sake wani,I'll make up for him..."tafad'a ruefully cikeda Dana sani.
Mermu zatayi magana sukaji k'aran k'ofa, dasauri suka juya a tsorace don and in wayeni idanunsu alamun marasa gaskiya unfortunately hajjo suka gani da tani a bayanta, sanye takeda jallabiya ta yafa k'aton gyale ya rufe mata jiki k'afarta da flat shoe.
Tana shigowa mamaki mermu tayi da tani suka sunkuyar dakai suna kallo k'asa.
"Sannu da fitowa ranki shi dad'e..."mermu tafad'a bakinta na rawa tanaiwa miemie alamar ta sauk'ar da kanta amma miemie ko gizau.
Da mamaki hajjo ke kallonsu, ganin miemie agun yasa ta had'a rai.
"Me kikeyi anan at this time? Meya samu bakinki?"fuskarta blankly
Batare da tunanin komaiba miemie tace
"Am very sorry your highne...
"Hajjo! You can call me hajjo!"ta gyara mata fuskarta expressionless
"Umm dama amm dama!"takasa fad'a ganin k'warjinin da ta mata.
"Ehm?"fuskarta alamun tambaya.
"Am sorry your high... Am hajjoo am dama dama naga shawarma ne a cikin warmer sai...ganinshi yawuna na tsinke without second thought naci ashe ashe na d'anki ne... Am very sorry."ta k'arishe tana runtse Ido.
Surprisingly hajjo ke kallonta
"You what?"tafad'a angrily
"I apologize no body is above mistake."
Hajjo tak'ura mata idanu tana nazarinta.
"Da alama ba'a gwada mini tarbiya da sanin yakamata ba a gidanku, ace a yanayinki da shekarunki zaki fito all the way from your room kizo har official kitchen a gidan da bakisan kowaba kiga abunda bakisan maishiba without second thought kid'auka kici, haka mahaifiyarki ta koya miki?"
"Your high... Am hajjo I apologize but please don't drag my mom to this, ninai laifi kuma nabada hak'uri baikaiga cin fuskar mahaifiyata ba coz uwa uwace."tafad'a boldly batare da tunanin komaib cikin jin zafin kushe mama datayi.
Kallonta hajjo take da mamaki tana nazarinta.
"Meya fito dake at this time?"
"I was bored shiyasa tafito yawo harna to nan" Tabata amsa
"Next time karki sake garajen fitowa war haka if you need something you can call through landline and you needs to walk on your manners before meeting me again."
Tanakaiwa nan tamaida kanta kan mermu kana tace.
"Make a cup of black coffee for him... Shikad'ai yake buk'ata, Sadi zaizo ya amsa anan."
"Angama ranki shi dad'e."
Tana kaiwa nan tamaida kallonta kan miemie tace.
"Next time wear something decent for you walk around the house...wannan bai kamace kiba."
Tanakaiwa nan tajuya tani tabi bayanta.
Ajiyar zuciya mermu tasauk'e kana tadubi miemie dakebin k'ofa da kallo.
"Alhamdulillahi,nasha zanbar gidan nan a gobe,dan hajjo batason 6acin ran PMB ko kad'an and I wonder yadda kike challenging d'inta, bata iya dogon zance dake."
"She's so mean!"shine abunda miemie tafad'a tareda zuwa gun washing hand basin ta wanke bakinta kana ta nufi gun fridge ta bud'e tazuri nutri milk a hannu.
Jiran mermu tayi har ta kamallah ManSadi yashigo ya amsa yahaura terrace dasauri.
Miemie ta dubi wani hanya dake gefenta tace.
"D'azu nazo wucewa na hangi glass wall but ban k'arisa gun ba coz da duhuwa, meyene a gurin?"
"Garden ne agurin Dr. Babbane sosae saboda ruwa yana tafiya a gurin sannan kuma akwai shuke shuke da dama,But nobody is allowed to go there except for PMB and his sisters,sud'inma idan yana gurin babu mai zuwa,idan yana cikin damuwa dakuwa gun yake wuni."tabata amsa a tak'aice.
"Really? Inaso na ga gurin!"cewar miemie sillily
"What? Bakya gujewa shiga Matsala."
"Please mermu lek'awa kurum nakeson yi."
"Okay saidai ki lek'a through the glass wall."
K'arisawa sukayi miemie ta lek'a gangarane da inda suke bakinta yak'i kulluwa sai dariya take tsantsar had'uwan gun,ga hasken wuta ya k'ara k'awata gurin, dama akwai guri irin haka a nigeria.

"K'arisawa sukayi miemie ta lek'a gangarane da inda suke bakinta yak'i kulluwa sai dariya take tsantsar had'uwan gun,ga hasken wuta ya k'ara k'awata gurin, dama akwai guri irin haka a nigeria

Ups! Gambar ini tidak mengikuti Pedoman Konten kami. Untuk melanjutkan publikasi, hapuslah gambar ini atau unggah gambar lain.

"Is this natural?"ta tambaya smilingly
"Nope artificial ne..." Constructing akayi saboda PMB mai martabane yasa ayi."
"Wow! So amazing mai martaba naji da d'ansan nan."
Murmushi kurum mermu tayi bata sake cewa komaiba.
Saida miemie tayi selfies masu isanta tagama kalle kallenta kana sukayi sallama da mermu bayan ta nanata mata duk abunda take buk'ata ta nemeta.
Hallway tabi bayan tamaida headphones nata tanajin wak'an little mix (power) hannunta d'aya rik'e da iPad d'aya rik'e da nutri milk, gashin nan har yanzu a zube a fuskarta sai tafiyar tan nan takeyi tana wurga k'afa.
Tafiya take santin wak'a na d'ebanta hartazo k'ofan d'akin, murd'a handle d'in tayi tabud'e, duhune a mamaye a d'akin, batareda tunaniba za kutsa kai,wani k'amshene ya dabaibaye mata hanci ga sanyin AC ya ya had'e da k'amshi, mamakine ya kamata tasan ta kunna AC amma wannan k'amshin ta ina yafito, tunawa tayi akwai flitter a d'akin yasa batayi tunanin komaiba, kasancewar ta haddace gun gado kawai tabi ta laluma ta ajiye iPad mata da nutri milk tahau kan bazareda ta kashe wak'ar kunnenta ba, laluma bargonta tafara son tasan ta bud'e bataji bargo ba, zaune ta mik'e ta laloma can kusan k'arshen gado tajawo ta lullu6a tareda lumshe idanu tanajin wak'ar Justin bieber (2U).

*****
I manage to drop this today, please cheer me up by pressing the star below; vote vote vote, comment as much as you can.

Guess whose room miemie entered?
Jeeddah loves y'all ❤❤❤❤

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang