SAUYIN RAYUWA!👩
Written by
H_jeeddher
In dedication to
Miemiebee👄
*****
Da asuba abeedah ta tashi,gaba d'aya jikinta ciwo kasancewar bata saba kwanciyar k'asaba,mik'ewa dakyar tadubi gado inda miemie ke kwance,gaba d'aya ta kwaye bed sheet d'in ta wangale k'afafu tareda hangame baki tana zuba gwarti, wandon pajamas natane ya rufa asiri don gaba d'aya kwanciyar batayiba.
Ta6e baki tayi ta girgiza kai,ko gigin tashinta batayi saboda gudun masifa,fad'awa toilet tayi ta d'aura alwala tafito,duban miemie saura k'iris tafad'o k'asa garin birgima,da kamar zata barta wani zuciyar yayi saurin kwa6arta,ba halinta bane mugunta musamman ma Idan tayi la'akari da har yanzu miemie yarinyace,tana bata shekaru yakamata ta rik'e girmanta komai zatayi mata yakamata tayi mata uzuri.
Zuwa tayi gaban gadon tana tunanin ta tasheta ko kuma, tunawa tayi da idan tatashita bala'i zataja wa kanta yasa ta yanke shawarar gyara mata kwanciyar kawai,k'ok'arin gyarata tahau yi dakyar.
Jin ana ta6ata cikin bacci ta tak'ark'ari ta narkawa abeedah gulli a ciki batare da tasaniba,dasauri tasaketa tareda da dafe cikinta,saida tayi minti biyu kafun taji dama dama.
Miemie sake gyara kwanciya tayi tacigaba da gwarti, dakyar abeedah ta tashi ta d'aura zani kan night gown nata tahau sallah,bayan ta idar tajawo wayarta ta karanta suratul yasin kamar kullum tayi daily du'as nata,saida gari yafara haske tamik'e kan rug inda ta kwana,miemie kam anata sana'a.
*****
Cikin bacci tafarajin k'idan favorite girl na Justin Bieber yacika mata dodon kunne,tsaki taja tana tsinewa mai k'iran ta wannan lokacin.
Bud'e Ido tayi taga d'akin yayi haske alamar gari ya waye,mik'ewa zaune tayi batare da takaranto addu'an tashi daga bacci ba, goge yawun baccinta tayi da rigarta,lek'e lek'e tafara taga babu abeedah a d'akin,bata damuba saboda abeedan kwando shara tamaidata,jawo wayar tayi taga missed call na Sarah hud'u.
"To meyene wannar kuma!" Tsaki tayi kafun ta danna mata k'ira ko immediately tad'auka.
"Hea what is it? Why are you calling me this early,bashi kike bina har four missed calls?" Ta fad'a irritatedly cikin muryarta kamar k'aran drum.
"What? Early? It's pass 10 already! Don't tell me you're still on bed!" Tafad'a surprisingly
"To meye? Ina ruanki?"
"Maida wuk'ar! I've got something to tell you!"
"Meyene?" Tafad'a kamar zata fasa wayan.
Murmushi Sarah tayi Dan tasan halin miemie,hak'urinta yayi yawa, dawatace da tuni tayi zuciya ta katse wayan amma Sarah bata fushi, dayaya suka zama friends,bawai friends d'in kut da kut ba, Dan miemie ammar,muneer da sageer sune best friends nata, Sarah itace mace ta farko da miemie ke kulawa harsuyi abubua tare,sam miemie bata d'aukar abubuwa gun Sarah irinsu kwalliya da Sauransu,haka zalika Sarah bata biyewa miemie suyi wasan banza, kowa lifestyle nashi daban haka suke zama,kamar wahainiya take,yanzu tasan haushinta takeji saboda ta katse mata bacci.
"Guess what?"
"Mtsw you know I hate guessing!"
"Oh Allah! Can't you try and guess even for once!"
"I said am not interested in all this guessing stuff just go straight to the point will you?"
"Oh miemie guess mana...
"Oh goodness aradun Allah I'll hang up! Wannan ae iskanci ne nama fasa ji..."
"are you angry already...
"Kutumar ubaaa! Tambaya kikeyi bar...
"OK OK now will you calmly listen to me please..."tafad'a jokingly
"Mtsww... Bana jinki!"
Dariya Sarah tayi
"Our jamb result has been released finally!"tafad'a at last joyfully
"Mtwwwww...banason munafurci mak'aryaciya..
"Have I ever lie to you before...?"
"Nasani ko kin fara yau."
"I ain't lying if you don't believe me you can check your email! I've checked mine already"
"Are you serious?" Ta tamabaya astonishingly
"Of course I'm! I scored 215."
"Like seriously?"
"Go see for your eyes!" Ding ta katse wayan.
Mugun tsalle ta daka takoma k'asa hankalinta gaba d'aya naga phone nata,Allah ya taimaka screen nata dukda fashewarsa yana dannuwa itama Tasha alwashin saita fasawa abeedah tata.
Idonta zuru zuru kan waya,na ammar tafara dubawa daga yasamu 234 wani ihu tasaka tanata tsalle,saida ta gama tsalle tsallenta ta duba tata,ihu tasa duk saida gidan ya amsa she can't believe she scored 240.
Da mugun gudu tayi falo duk yawun bacci a bakinta kanta kuwa buzu buzu gaba d'aya wata iri.
KAMU SEDANG MEMBACA
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romansa"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...
