In dedication to
Miemiebee👄Abba da kansa yaje har gida yayi wa baba bayanin komai, sosae ya gamsu da bayanansa amma a zahirin gaskiya bayason tafiyan miemie,baison tayi nisa gida saboda sanin halayenta da yayi,ya rayuwarta zata kasance bayan ta tsinci kanta inda batada kowa hartayi watanni uku, dama wani gidane daban ba babban gida data Tara mutane iriri wanda yawanci hassada da kyashin juna yayi yawa, da ba gidan sarauta bane da sauk'i amma gidan sarki guda,yana tsoron rigimar da 6aran6aramar miemie, a gida ya aka k'are bare takaiga gidan sarauta inda ba'a d'aukar raini musamman babbar masarauta irin ta gombe,daga jin bayanin abba yasan duk yadda akayi akwai sark'ak'iya cikin lamarin amma saiyayi Sauri ya kawar da tunanin,dafarko baijin zai ita yarda amma daga yayi dayayi nazari sosae,abinda miemie zatajeyi taimakone Wanda silar hakama ta ceci rayukan al'umma da dama, yasan muddin miemie tasa abu a giba hankalinta bai ta6a kwanciya saita cimma shi, abin alfaharine a gareshi ace 'yarsa tana samun d'unbin lada a gurin allah saboda taimakon mutane da takeyi,tsoronsa d'aya gidan sarauta na cunkushe da abubuwa da dama,mugaye, algungumai sun yi yawa cikinta, a yadda yaji bayanin abba yafara d'ago wasu abubuwan d'aure kai,saurin barin tunanin yayi saboda zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya, bazaiso kauce aekin lada saboda waso tunanai Wanda baida tabbaci akansu ba, zai yiwu hasashensa ne kawai,bisa dogon nazarin dayayi har aransa ya aminta miemie taje tayi taimako dan Allah, amma sai ya tabbatar yaja mata kunne sosae saboda sanin halinta na shisshigi dashiga abunda bai shafeta ba.
"Haba alhaji! Maryam 'yarka ce kaima, duk abunda ka yanke nasan daidai ne basai kanemi yardana ba,indai maryam d'in ta amince babu matsala..." Cewar baba
"Ban tari numfashinka ba, amma a nawa tunani ya dace na sanar daku, bakowa bani zaibari 'yarsa taje inda batada kowa sannan kuma ta gamu da mutane iri daban daban musamman gidan sarauta, koda kuwa ka amince k'anwata fa, kasan uwa batason abunda zaijanye d'iyarta daga gareta musamman zuwa guri irin haka,a nawa tunanin ya dace kuyi shawara da ita tukunna."
Baba ya zaunar da mama ya fad'a mata abunda ake ciki, shiru tayi takasa magana saboda kanta gaba d'aya ya k'ulle, zataso 'yarta tayi taimako amma sanin halin 'yar yasa jikinta yayi sanyi tana tsoron abunda zaije ya dawo,da wanine daban cikin 'ya'yanta da gudu zata yarda amma banda miemie,sanin rawar kai sa shisshigin tsiyarta zaisa ta iya jawo musu matsala.
Baba yasubi mama yadda tayi shiru tana tunani,hannunta ya kamo cikin nasa yana kallon fuskarta.
"Maman sadeeq"ya k'ira sunanta.
Cikeda damuwa ta d'ago tana dubansa Yad'anyi murmushi.
"Nasan a ranki kinaso maryam ta taimakawa al'umma sosae musamman mai martaba dayake buk'atan taimako a wannan lokacin, amma kina tsoron abunda zaije ya dawo saboda sanin d'abi'unta Sam baiyi kama da irin nasuba,sannan kasancewar babban gidane kina shakkar kar maryam ta janyo wata fitina garin nemo k'iba a samu rama..."
Shiru tayi tana kallonsa idanunta alamar damuwa sosae.Tanajin dad'in yadda mijinta ke karantar halin datake ciki lokaci guda kuma yake k'ok'arin kawar mata da shi komawa wace irice, sosae take alhafari dashi kuma a kullum take godewa allah daya batashi a matsayin miji, addu'arta kullum miemie tasamu miji mai hali irin na mahaifinta koma fiye da haka amma miemie batada wannan lokacin.
"Nima nayi wannan tunanin zainab, amma dana zauna nayi nazari sosae akan haka sai nafara tunani,kiduba tsakanin gombe,bauchi,plateau da sauran jahohin dake kusa, akwai physiotherapist bila adadin, mehyasa sa suka tsallake sauran sukazo kan d'iyarmu,Allah ne masani,shiya tsara komai kuma shiyasan abunda yake nufi da hakan, saina fara sawa anya tafiyar miemie ba alkhairi bace? Wannan Allah ne ya shirya saboda inaji a jikina Maryam zata zama abin alfari ga kowa, inaji a jikina gaba silar taimako zata San abunda ke mata ciwo, baya ga wannan kiyi tunani rayuwa nawa zata ceto dalilin taimakon mutum d'aya,bakya ganin zuwanta can zaisa tasan abunda rayuwa ke ciki zainab gidan sarauta ya wuce sanin kowa,babu wanda yasan gaibu cikinmu,bazamu predicting abunda bamuda tabbas ba shin zata bamu kunya ko a'a, abunda batayishi lokacinda take jami'a ba banjin zatayishi yanzu, duk da nasan tana misbehaving but never once nayi failing exams ko aka suspending nata, duk rashin hankalin da takeyi bata ta6a kauce hanyar allah ba, I believe in her addu'an mu take buk'ata, mu rok'a mata kariya da tsari wurin allah, sannan mu kwa6eta karta shiga abunda bai shafeta ba, ta focusing kan abunda ya kaita harta kammala ta dawo... "
Tabbas abunda baba ya dad's gaskiyane, basuda tabbas d'in ko miemie zatayi abunda suke tunani, abun alfaharine a garesu ace yau jininsu ya taimaki wani.
" yadda take 'yata haka itama 'yarki ce, bazan tilas ta akan tajeba as far as ranki bai so ba,you're a mother in hankalinki bai kwanta ba shikenan dama tuncan haka allah ya tsara...
Da Sauri mama ta tasa hannunta kan bakinshi tana murmushi.
"Banida jayayya akan duk abunda ka yanke baban sadeeq,yadda banida ikon kaine haka banida ikon maryam,kaine komai namu haka zalika duk hukuncin daka yanke shine nawa,farin cikinka shine nawa farin cikin haka zalika damuwarka damuwa tace, nida miemie duk mallakinka ne banjin har abada zan iya jayayya kan abunda ka yanke, bayanin dakayi yasa hankalina ya kwanta, banda sauran damuwa baban sadeeq, na amince d'ari bisa d'are, kuma I believe addu'armu shi zai kare mana ita..."
Jawota jikinsa yayi yana k'ara jin sonta a ranshi, yana alfahari da ita.
"Nagode da fahimta na dakikayi zainab, bazamuyi nadamar yarda da hakan ba insha allah..."
"Amma a ganina ya dace hajjah tasani saboda bazamu yanke hukunci ba tareda da yardarta ba!"
"Ashaf! Hakane fa, ina sonki sosae ke alherice, inawa 'ya'yan mu fatan samun Mata ta gari irinki mai tsayuwa wa mijinta a kowani hali, zainab ina k'aunarki sosae."
Da Sauri mama ta cusa kanta a k'irjinsa a dole kunya shikuwa sai dariya yake.(Oh allah tsofi ba'a bar soyayya ba,su mama wai kunya,an ajiye gard'a gard'an samarai amma anakan min kunya LOL).*****
Hajja ta yarda itama bayan dogon nazari akai, kwana biyu tsakani aka gama shiye shiryen komai na tafiyan miemie,daga masarautar za'a turo mota kasancewar tafiyan awa biyuce daga bauchi zuwa gombe.
Washegarin da miemie zata tafi suna hangar dawowa daga gidan hajjah itada maheer, ahanya yayi shiru gaba d'aya jikinsa a sanyaye baisan meyasa ba, miemie nata zuba tanata murnar washegari zata ganta a palace, ina shi hankalinsa baya kanta, driving kurum yakeyi amma a zahiri hankalinshi yayi wani gun, jiyayi an tura kafad'arshi da k'arfi saura k'iris steering ya kauce masa dasauri ya taka burki har said a miemie da tsorita batasan lokacinda ta tukwuikuyo jikinsa ba.
Cak komai na jikinsa ya tsaya yakasa k'wakk'waran motsi yana kallonta, miemie kuwa a jikinta dan ita a duniya batada wani feelings itadai gatanan nedai kawai.
"Chapdi jam! Tunanin meh kake inata zuba kayimun banza, aradun allah k'iris ya rage ka zubar damu."
Still yananan kamar statue yazuba mata na mujiya ko kyaftawa bayayi.
Miemie kuwa kumatunsa takama da k'arfi taja saida yad'an Saki k'ara.
"Wai nikam my paladin what's bothering you, I've been talking and talking non stop but I dont think you heard a single word a said!" Tafad'a mockingly tareda jan seat baya ta d'aura k'afafuwanta kan pegging box.
Still kallonta yakeyi yanaji kamar yajawota jikinsa ko zai rage masa abunda yakeji a zuciya,haka kawai yakejin bayso tayi nesa dashi, he wants her near him, he just cant resist been without her, why is he feeling something strange about for,fiye da shekaru goma yakejin abunnan gameda miemie, hydar yasha fahimtar dashi akan hakan amma yana denying,acikin kwana biyun nan feelings d'in dad'a girma yake he can't deny it anymore, ya yarda he's deeply and madly in love with miemie kuma he likes everything about her, duk wani wauta da shirme datakeyi yana so,komai bata daga magana,tafiya da komai about her yanaso, he just love her the way she is, he so much loves her...he wants her, he want to cherish her and make her feel like a real princess, he wants to show her how much he love her wanted to be with her, he wants to confess his true feelings for her but he doesn't have the courage why? duk sanda yayi niyya kasawa yakeyi,tsoro yakeyi ya zata d'auka dan shi baijin miemie tasan wani abu waishi so,gashi zata yi nisa dashi, jiyake kamar sun rabu kenan har abada,da farko yayi murna kan abunda miemie zatajeyi but banda yanzu, jiyake kamar zata barshi, yau yad'au alwashin sanar da ita takoma halin yaya but ya rasa ta wani hanya, abunda yake tunani kenan tuntuni,kallonta ya cigaba dayi.
"Wai nikam meyene? Why are you staring at me like this paladin..." Tafad'a cikin gargadan muryarta.
Cikin sanyin murya Wanda yake nuna tsananin Sonta a ranshi yace.
"Princess are you happy to leave me here all by myself?"
"Why'd I not be happy,aradu murna nake zanje gombe gobe you know what? Kawai inaso naga yadda palace d'in yake, yadda mutanen ciki ke rayuwa,kai komaima dake ciki and lastly Inason cin nasara a abunda zanjeyi." Tafad'a tana dariya.
Shiru yayi yana nazarinta, can yaji tace
"Kaifa ga yah hydar da me... Auu!" Dasauri tayi shiru
Baice komaiba ya sauke handbreak suka fara tafiya, instead of taga sun nufi gida saitaga sun canza hanya.
"Ina kuma zamu?"
"Are you scared already?"
"Nooo! You know I won't be scared of anything as far as you're with me..."
Murmushine ya su6uce masa tareda kallonta ganin hankalinta nakan wayarta yasa yajuya.
Restaurant suka nufa, bayan sun iso yayi parking cikin premises d'in, d'agoa tayi tadubi gun tareda sake haki tana hura hanci alamar mamaki.
"My paladin what are we doing here?" Tafad'a tana sauk'e kafarta daga saman pegging box
"I guess you haven't eaten anything since morning and it's 7:30pm already..."
"Chap! Waya gayama Nid'in ne zankai war haka ban gabza abinci ba, aradu naci tuwo a kitchen gidan hajjah harda fura nasha..."
"Princess yaushe kika fara rowa? Tukunna ma when did you Start eating without me ehn?" Ya k'ura mata ido
"Yo Toh naga kai d'an gayune bakacika son tuwo ba, nikuma duk inda akwai tuwo tofa an wuce gun don shikad'ai ne nake masa kallon abinci, tukunna ma ba gida zamuje ba?" Tafad'a tana ware masa idanu tareda Sosa saman hanci.
Kallonta yake yarasa abun cewa, ganin tambayar datake kwararowa baisan sanda yace.
"I want to tell you something very important..."
"Important?"
"Yeah... And ko bakyason cin abinci anan... Wait! Anya kin ta6a cin abinci a restro?"
"Eh mana! Zuwana kaduna, chai! Walloh yah deeku asarar kud'i kawai mukabar abinci a gida ya d'aukemu nida adda abeedah..."
Dakatar da ita yayi..
"And yes! We promised to go on a date remember? So here we are c'mon shine namu..."
"Ayho! Dama haka ake date d'in?"
Murmushi yayi yace.
"Rik'e sauran zamu k'arisa anjima fito."
Kan ya zaga ya bud'e mata ta fito abunta tana mik'a sai sannan na k'arewa kayan jikinta kallon.
Kamar kullum halem pants da top sai jacket a sama ta yafa gyalen akai.
"Shall we!" Yamik'a mata hannu tarik'e suka shiga.Comment
Vote
And shareOneLove ♥

KAMU SEDANG MEMBACA
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romansa"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...