chapter 7

2.2K 154 0
                                        

IN DEDICATION TO MIEMIEBEE👄

"Baby bari yayan naki yazo sai a tambayeshi"

"Niba ma'alyaciya bane kamar ammal!"

"Miemie kibali fa baluwana mama zata bugeki!"

"Ina luwanka dani ae hajja na ne tace ajo dani nima amun!" Tafad'a tana k'ok'arin daga hannu zata dakesa yayi saurin matsawa.

 Mai aski kallonta yake yana mamakin ta, sa musa daru tayi da itafa sai an mata, birgima tahauyi tana rikici itama ance amata.

Mai aski ya d'auki scissors zaifara yankewa kafun ayi da clipper.Yanke wa yahauyi saida ya yanke duka gashin itakuwa sai hangame baki takeyi.Clipper'n ya daura kan tahau dariya, ammar ko ya sake baki yana kallon ikon allah Dan dayace pit to fa miemie zata mammakesa, bataga kan taba kasancewar tsayinta baikai mirror'n ba itadai tanajin dad'i akanta. Sanda aka gama askin tas tadub'i mai aski tace "Dad'i a shake min!"

Mai aski yayi dariya yace"Baby an gama babu abunda za'a aske!"
 
Tajuya ta kalli ammar"Ammal wai haka!"

Ammar mai zaiyi inba dariya ba,haushi yakama miemie"To meye kakemun daliya!" Tafad'a tana b'ata fuska.tadubi mai aski tace"A'gani naga madubi nafisa kyau ne yake jin haushi!" Mai aski kuwa yayi yadda tace yad'agata ya tsaidata kan kujera.

"Kutumelesun nan!" Ta rantamo ashar

"Ina gacina?" Ta tambaya tana shirin yin kuka, mai aski yasake baki yana kallonta"Baby ga gashin nan an aske!"
 
Kallon gashin tayi sannan ta kalli mai aski"Wallahi ka biyani gacina!"Tasanya ihu

"Nikam ka biyani ka biyani!!!Kuka takeyi tsakaninta da allah tana birgima "nikam ka biyani gacina ko na k'ira police station ya kamaka kuma na pa'awa hajja na"Hand'a da gand'a yasake yana kallonta.

Ammar sai dariya yakeyi, mik'ewa tayi ta taska mishi Mari shima yasanya ihu.

Mai aski yau yaga takanshi, mutane suka fara tara mishi ita a dole yabiyata gashinta. Ana cikin haka sadeeq yadawo.
  
"Subhanallahi! Gwuigwui meya sameki?  Ammar meya faru?" Yafad'a yana k'ok'arin dagata a k'asa tana tirjewa"Ya deeku kace ya biyani gacina!"

"Gashinki a in..."Baki ya sake ganin kan miemie anyi k'wak'wal dashi.Same time haushi,dariya, bakin ciki, takaici, nadama duk suka rufeshi, rasama abun fad'a yayi yana kallon me aski.Mai aski sai muzurai yakeyi tare da nadamar biye mata dayayi.
 
"What have you done James?" Ya tambaya furiously
 
"She was the one that insist believe me I didn't intend to...
 
"For goodness sake can't you see she's just a kid huh?"
 
"Is not my fault shaa, she was crying I have no option than to do what she insist besides I work for money!"Yafad'a cikin halin ko inkula.
 
Haushi yagama cika sadeeq, tunda yake miemie bata tab'a basa takaici irin nayau ba, yadube ta cikeda haushi yadaka mata tsawa."Will you shut the hell up and get up!" Abunda baita6a yiba.

Take taga yasauya mata yabata tsoro,tsit tayi tare da mik'ewa tana shesshek'a.

Wafce clipper'n yayi ya ajiya masa 1000 ko kula canji baiyiba yaja hannun ammar sukayi waje James ya tab'e baki yacigaba da abunda yakeyi.

Miemie dake tsaye tajuya ta kalli James tare da murgud'a mai baki"Allah ya isha mugu, uwaka!"

Baikula ta ba yaciga da abunda yakeyi,gurin kud'in tanufa ta d'auka tareda b'oyewa bayanta"Bala a baka ku'in ba 6alawo kawai"Gadan gadan zaiyiwo kanya, tsala ihu tana k'iran ya deeku.
  
Sadeeq dake k'ok'arin dawowa dubota yaji abunda tace, janyeta yayi tareda kar6e kud'in a hannunta ya ajiye.

"O ooo ya deeku bala abasa ba ya biyani gacina!"

Sadeeq daya gama k'uluwa yace"Kinsan allah gwuigwui idan bakiyi shiruba zan zaneki, c'mon wuce mutafi!"

Kuka tasa sosae harya juya tana kallonsa.Dawowa yayi ya Sanya mata hulanta cikeda haushi yaja hannunta suka fice.

 Baya baya takeyi suna gaba sadeeq na rik'e da hannun ammar, batare da sadeeq ya luraba miemie tajuya ta koma shagon.Mai aski yana shara,ya juya baya bai lura da shigowanta ba ta lalla6a kamar 6era ta kama hannunsa ta gantsara masa uban ciro saida yakusa jini tad'ago"Kuma allah ya isha!" Ta arce a guje.

Azabar da hannunsa keyi baisa yayi yunk'urin mata wani abuba.Duk acikin seconds da baifi 7 ba miemie tadawo.Sai ganin miemie yayi agabansa tana dariya tana sauk'e numfashi. Juyawa yayi bayansa baiga kowaba tabbacin itance.

 "Hehehe yah deeku na cucesa tunda na cijesa!"

"Kinyi meye?"

"Na lama mana!" Tafad'a tana tura baki.

"Bakyaji ko gwuigwui!" Yaja kunnenta kad'an cikin b'acin rai.Ihu tasa wane marinta yayi ga muryar kamar fasasshen ganga,har mutane sun juyo.Hannunta yaja dasauri.

******
 
"Yo ina su sadeequ suka tsaya ko borno sukaje yaci sun dawo yanzu kam!" Hajja taf'ada cikin fad'a tana duba agogo.

Rabi dake goge TV tayi dariya yace"Hajja k'ila suna hanya!"
 
"Uwar meye suka tsayayi awansu guda har da rabi da fita,Yadda rana tayi zafi 'yan biyu kurum nake tunani,musamman miemie da batason rana,nibansan meya kaini cewa sujeba..."Bata idasa ba tajiyo kukan miemie tundaga bakin gate,gashi dama murya ba kad'an ba dan tsakininta da allah takeyi.

Mik'ewa hajja tayi tana tambayar lafiya.Dagudu tafad'a jikin hajja tana kuka hajja duk ta rud'e tana tambayarta lafiya.
  
Sadeeq kallon kawai yake bin miemie dashi don salun alum suka dawo daga gate tafara wannar ihun.

"Me akayi mata sadeequ?" Hajja ta tambaya tana kallonsa.

Shiru yamata yakasa cewa komai."Dan gidanku ba tambayarka nakeba kayimin kunnen uwar shegu iyee! Mairona fad'amun waya ta6aki"
D'agowa tayi tanuna sadeeq da hannu tana tura baki tana shesshek'a.
  
Baki sadeeq ya rik'e yau abun takanshi ta fad'a.
 
"Uwar meh kayi mata iyee?"
  
"Hajja ba shine  yakaimu acki ba kuma mai acki yacilemun gacina kuma shine ya deeku ya dakeni!"
 
"Aski aka miki mairo?" Hajja ta zaro idanu waje.Cire hular tayi,meh zata gani! Kan miemie fayau babu gashi.
 
"Innalillahi! Meh nake gani abubakar? Da hankalinka kace ayiwa maryama aski?"....nan hajja tafara fad'a ta inda take shiga batanan take fitaba.Allah sarki bawan allah sadeeq shiru yayi yana kallonta.

"Hajja da kin tsaya kinji bayani kamar akwai magana bakin sadeeq da gangan bazai bari ayi mata aski ba!"cewar rabi
 
"Uwar meh zai gayamun bayan kinji abunda mairo tace,zata masa k'aryane?meh tasani iyee!  Mairo fad'amin abunda yafaru maza!"

Miemie ta k'ara shesshek'a tace."Hajja acki yace amana ya tafi!"
 
"Ayya takeyi!" Ammar ya fad'a.

 Miemie tad'ago"Ka lupa mana baki! Kaine meh ayya ae!"

  "Zo ammar!" Hajja ta yafico shi da hannu,matsowa yayi "Fad'amun maza!"

Cikin gwala6en hausan sa yamawa hajja bayani.Tunkan yayi rabi miemie a hankali ta janye jikinta a jikin hajja tayi bayan rabi.Sallallami hajja yafara.

"Yo sadeequ shine bazakamin bayani ba!"

"Hajja fad'a fa kika fara, you should've asked me first before jumping into conclusion!" Yafad'a sounding disappointed.
 
"Mairo zonan!"

  "O ooo!"ta make kafada

"Karki sake k'arya kina jina!" D'aga kai tayi.

 Haushi yagama cika sadeeq,shikenan fa hajja bazata hukun ta ta ba,ficewa yayi daga gidan abunsa.

_Sunday_

Ranar sadeeq yakoma ya d'aukosu daga gidan hajja, 5:30pm suka shigo Gidan.Hydar na taya faruk assignment,faruk na kwance kan rug, mama da ikko suna kitchen.Da gudo ta shigo falon tana ihu ta take k'afar hydar saikan ruwan cikin khaleel ta daka tsalle, wani ihu sukasa a tare Dan sun mugun tsorata da shigowarta khaleel ya rik'e cikinsa.
 
Mama da ikko har suna cin Karo garin fitowa.Miemie kuwa sai kyalkyalar dariya takeyi daidai lokacin sadeeq ya shigo rik'e da hannun ammar.
 
"Oyoyo mamana!" Tafad'a kan mama saura k'iris ta kifar da ita Dan komai na miemie da k'arfi takeyin sa.
  
"Bana hanaki wannan gudu da wasan banzan nan ba!" Tafad'a tana zare mata idanu.
  
Turmutsa fuska miemie tayi tana shirin yin kuka."Mama oyoyo fa nayi!!"
   
"Haka ake oyoyon a garinku!"
  
"Komawa gun hajja na danyi tunda ba a shona" tafad'a tana tura baki zatabar falon.

Babu wanda ya kulata,mama takoma kitchen abunta.

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now