chapter 74

1.8K 164 30
                                        

In dedication to
Miemiebee 👄

******
"What?"miemie ta furta cikin kid'ima.
"Yeah you've to be back ASAP acewarta tana buk'atan ganinki kafun ta mutu,kinsan rigimar tsohuwar nam."cewar yah faruk
"Mene ke damunta?"
"Hawan jininta ne ya tashi...sai ciwon jiki datake fama dashi amma yanzu yadawo normal saidai fa ta nace sai kinzo dan acewarta mutuace takusa zua."
"Oo hajjah,ta iya rud'a mutane,tell her I'll be back soon...Allah ya bata lafiya."
Sallama sukayi miemie na jinjina rigimar hajjah...a lissafinta saura kwana biyar ta koma but ciwon hajjah yasa tanason tafiya a gobe.

*****
Tamusu bayanin hajjah ba lafiya tanason lafiya a washegari, abba ya fahimce ta kuma yasan tana cike da kewan gida, wata uku ba wasa ba shiyasa yace tashirya a washegari za'a maidata gida, zarah da amatu zasu rakata daga can su wuce abuja gidan kanwar hajjo, zarah zata wuce Cyprus while amatu zata fara zuwa baze.
Da daddare miemie na shirya kayanta zarah na tayata while jaleelah ta baje sai chatting takeyi.
Amatu ce tace
"Adda zarah yaya I alal yace kisameshi a garden."
Kamar bada ita ake ba.
Miemie da jaleelah suka dubeta tawani kauda kai.
"Tomato jekice tana zua."cewar miemie.
Zarah ta d'ago ta dubi miemie a hasale
"Babu inda zani karma ta6ata kafarta."
"Why do you've so much hatred for my brother zarah?"jaleelah ta ajiye phone tana kallonta.
"Cause I hate him...I hate him dayayi sanadiyar rabani da kamal, tell me jaleelah ya zakiji idan an ranaki da masoyinki?"
Shiru tayi batace komaiba cause tafara experiencing a baya amma yanzu batada wani prob tunda miemie'n zata koma sannan ya yarda zai aureta.
"Zarah ya jalal ya canza..."
"I know but I hate him thesame."
Jan bakinta tayi tareda yin gum.
Miemie tadubeta tace.
"Don't misundastand him zarah...jalal is now a changed person, bawai nace ki soshi ba am hoping hatred din dakike mishi ya ragu cause he's your brother, jininki ne shi... Please go bakisan abunda ke tafe dashi ba,ba'a fidda rai da rabo k'ila kamal shine mijinki ko kuma jalal shine alkhairi a gareki...kedai kiyiwa kanki fatan alkhairi."
"Ni inaga kamal din nan ba sonki yakeba, never once daya nemi inda kike..."jaleelah takar6a.
"That time hajjo ce ta tilastashi ya rabo dani."
"Bayaga nan fa...yanzu present
Muke ba past ba,Ko ban fad'a miki hajjo har gidansu taje tabaiwa mahaifiyarsa hak'uri ba, at least he could have call you idan yana sonki... Zarah you have to wake up cause ke kike sonshi shi ba sonki yakeba...stick that into your head..."tana kaiwa nan tafice abunta.
Zarah ta bita da kallo rai a 6ace.Miemie ta mika mata mayafi.
"Gashi kisameshi."
Ba musu ta amsa tareda ficewa.

******
Bayansa ta hango daga wutan d'aya haska gurin,yana zaune kan bench da alama waya yake.
Had'e rai tayi dam Sam ko kallonsa batason yi.
Yana tsaka da magana yaga mutum tsaye a kansa ta juya masa baya hannunwanta hard'e saman k'irjinta, sai abun ya bashi dariya ya katse wayar yana dubanta ta gama rainashi.
"Fatee..."bata amsa ba sannan bata juyo ba.
"Why didn't you answer any of my calls?"ya tambaya sounding serious.
"Banga damaba saboda bamuda abunda zamuce da juna."
"Nidana k'ira ae nasan abunda zan fad'a anyway ba abunda yasa nayi k'iranki ba kenan."
"Nafika matsuwa na sani cause am tired of standing here."
"Really... Why don't you just sit down cause nima na gaji da ganinki tsaye a kaina."
"Ohooo...I think I would have to leave."
Tajuya kenan yace
"Abunda kikaga dama bazan takuraki ki tsaya... But inamai tabbatar miki kika tafi kinyiwa kanki kuma dole nid'in zaki aura...gwara tun wuri ki dawo hankali ki adana sauran rainin naki mu nemar wa kanmu solution."
Jin haka da sauri tadawo hartana cin tuntu6e ta zauna tana facing d'inshi.
Murmushi yayi yana kallon fuskarta data 6ata sai taimishi kyau.
"I love you Fatima, but I won't force you to marry me cause nasan bakya sona you love someone else..."
D'agowa tayi tana dubanshi yadda yayi maganan saiya bata tausayi.
Murmushin yak'e yayi kana ya cigaba.
"I truly love you and I want the best for you, your happiness shiyafimun komai, abba yasake magana kan auranmu but I choose to ask for your opinion dukda nasan amsar d'ayane you hate me shiyasa nayi deciding fasa auranki..."ya had'iye Abu mai d'aci kana yace.
"Kamal is the one you love right?"
Bata bashi amsaba illa kallonsa kurum datake da mugun tausayinsa, ita kanta tasan jalal na sonta sosae tun tana karama.
"Na kawo miki kamal fatee...turn around and see your happiness."yanakaiwa nan ya tashi yabar gun.
Bayansa tabi da kallo kamar sokuwa kana a hankali ta mik'e tareda juyawa bayanta, wa zata gani.
"KAMAL."Ta furta a hankali tanason tabbatar da abunda ta gani.
Tsaye yake hannunsa zure a aljihu yana mata murmushi, ba laifi black beauty ne ya had'u, banga laifin zarah ba datake sonshi.
Da gudu ta k'arisa tareda tsayawa gabanshi tana lek'e fuskarshi dan tabbatar da shi d'in ne.
"Zarah..."jin muryarsa ya tabbatar mata da shi d'in ne, tarasa wanne d'aya zatayi kuka ko dariya, sai kuma tafara dukan k'irjinsa da hannunta.
"Where the hell have you been, do you know how much I missed you..."saikuma tasa kuka tana bugunsa.
Cafke hannunta yayi yana kallon fuskarta kana yace
"Zarah listen to me..."
"I don't need any explanation cause it'll make me more angry...let's forget everything tunda muna tare a yanzu."
Sauk'e numfashi yayi kana yace.
"Zarah I've something to tell you."
Tattara hankalinta tayi ganin yadda ya sauya fuska zuwa damuwa.
"Zarah you misunderstood our relationship."
Blankly take kallonsa.
"What are you trying to say."ta tambaya bakinta na rawa.
Kutt ya had'iye yawu yace.
"Zarah I...I..."
"You what?"ta tambaya a tsorace
"I never loved you...I thought we're best friends da zamu ringa sharing both our sorrows and happiness together but you fall for me in the process...I tried to explain it to you but regarding situation din dakike ciki a lokacin nayi shiru... Please forgive me but munaya is the one I love nasan bakisan ita cousin sister na bane...aurenmu nan da wata d'aya insha Allah... Am sorry."
Frozen tayi a tsaya zuciyarta na mugun harbawa...shin mafarki take ko a zahiri.
"Am sorry zarah..."
"Go away..."ta furta a hankali hawaye ya zubu.
"Z...
"Get out of my sight..."ta fad'a da k'arfi
Jiki ba Lakka ya juya zaibar gurin yaji tafurta.
"Don't you ever show your face to me again..."tana kaiwa nan ta juya da gudu tabarshi agun.

Jalal dake tsaye daidai entrance d'in yayi zugum kalan tausayi tareda zuba hannu a aljihu yana kallon compoun d'in, ganin zarah tanufo da gudu tana kuka yasashi nufanta.
Ji yayi ta fad'a k'irjinshi tareda kankameshi tana kuka iya k'arfin da Allah ya bata.
"Ya jalal, jaleelah was right kamal never loved me, he never loved me I was the one fooling myself."tafad'a cikin muryar kuka.
Ji yayi tamkar yaje ya shak'e kamal ya nad'a masa na jaki kan abunda yayiwa zarah...
"That bastard..."ya yunk'ura tareda d'agata zaije tayi saurin taroshi tareda girgiza mai kai tana hawaye.
"Let him be..."
Mannata yayi da kirjinsa yana comforting d'inta."
"Shhh... He'll pay for what he did to you zarah... I thought bringing him over here zaisaki farin ciki instead it broke your heart... Am so sorry..."
Dakyar ya iya lallashinta kana
A ranste yace "Be sad as you wish Zarah,Cry as much as you need, Suffer from the heartbreak, and then come to me."
Bayan nan yaja hannunta zuwa cikin gida gun miemie cause She's the only person that can calm her.
Dakyar miemie tasa tayi shiru yareda alkawarin erasing memories din da sukayi da kamal.
Miemie kam itakadai tasan abunda takeji a zuciyarta... Manta murad ba k'aramin Abu bane but she really have to try.

_THE NEXT DAY..._

hajjo ta rik'o hannunta miemie idanunta na dab da kwalla dake sake mata godiya dasa albarka,da da halin dazatace miemie karta tafi da tayi, shakuwar su lokaci guda amma tanajin sonta kamar soyyayyar d'a da uwa, dukansu saida suka zubar da hawaye.
Da kyar miemie fa amshi kyautar da hajjo tamata na gold jewelry (set) Wanda ta gada gun mamarta.
Abba ma dauria da mulki ne kurum suka hanashi zubda hawaye dan sosae yakejin zafin tafiyanta a zuciyarshi.
Yazaunar da zarah dan jin tabakinta gameda auren su da jalal tanaso ko bataso.
Mamakine ya kama kowa data amsa zata aureshi,kowa yayi farin ciki shiko baki har kunne yasamu Wanda yakeso...anyi alkawarin daura aure dazaran ta kammala karatunta nan da shekara d'aya tareda nasu murad da jaleelah.
Har gun shiga mota aka rakosu, guards da maidens din gidan duk sun fara kewar miemie dan ita kowa natane, jaleelah ma sunyi kyakkyawan bankwana da ita kafun suka d'au hanya da driver sai sadisu sake gaba su miemie a baya.
Babu Wanda ta sanar da dawowanta a ranar surprise takeson basu, farin ciki wane an tsumbulata a aljanna haka takeji, she can't wait to see her family a hankali tace
"BAUCHI STATE HERE I COME."

*_BAUCHI..._*

Abeedah na hango zaune da tulelen cikinta dan wata bakwai kan kujera a kitchen tana yanka vegetables, ammah dake tsaye rik'eda Teddy bear sai kukan fitina take bata kulata ba.
"Kinsan Allah idan baki rufamun baki ba zan mugun sa6a miki..."
Jin haka yasa tasake wangame baki dan tasan mummyn nata dakyar take iya tashi.
"Waya ta6amun manga cubu na..."cewar mama dake shigowa
Da gudu ammah ta fad'a jikinta
"Mummy ne."
"Meye mummy tayi manga?"
"Fitina ne kurum mama...wai saina bawa teddynta nono..."
Meye mama zatayi inba dariya ba
"Ke ina nonon naki dazaki kaiwa mummynki tabata."
"Nawa ba ato bane irin na mummy..."tafad'a tana tura baki
"To kibari idan kikayi saikina bata ko."
"O..ooo anty mumu na zata bata ae...mummy tafison unborn baby akan ni."
"Waya fad'a miki haka?"
"Anty mumu...wai ni mai big head"
"Idan ta sake cemiki big head kice mata gado kikayi kinji?"cewar ammar dake shigowa
Mama tadan buga keyanshi...
"Zaka koya mata rashin kunya ko?"
K'ara yadan sake yana dariya.
"Yau tun safe zancen anty mumu ake a gidannan."cewar abeedah
Dakyar ta mik'e mama ta tallafa mata.
"Kidinga hutawa Fatima... Bani nan aekin ya isa haka ikko zata k'arisa."
"Mama tun safe banyi komaiba sai yanzu...am bored shiyasa nake dan motsa jiki."
"A motsa dakyau saboda a sun6ulu baby mai kuzari irina..."duka suka tsinkayi muryar miemie daga bakin k'ofar kitchen d'in.
A tare suka sake baki suna kallonta,ammah ce da gudu ta rungumeta miemie ta d'agata sama
"Miss you big head."kana ta sauk'eta.
Ta rungumi mama da farin ciki ya hanata magana fuskarta ce zata tabbatar ma da hakan.
"I missssed you soooo much mamana."
"Miss you too miemie... Allah na gode maka daka dawomun da d'iyata gareni lafiya."
Kana abeedah ta rungumeta suna dariya
"Gwuigwui ja baya wanna makalkala haka karkisa a haifarmun bakwanni ba shiri."cewar yah deeku.
Fad'awa jikinsa tayi tana dariya.
Ammar yace
"UHHH...why are you back?"
"Ko zaka maidani ne... Wama ya maka magana."
"Lil coke and fanta...kunfara ko?"cewar yah khaleel
Zata bud'e baki faruk yace
"Mumu kinbar bak'i a waje fa."
"Auuu..."

*****
Comment,vote. And share

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt