chapter 48

1.5K 136 3
                                    

In dedication to
Miemiebee 👄

******
  Cikeda mamaki miemie ke kallonsa
"Kamar yaya abba?"ta tambaya curiosity.
Ya sauk'e numfashi kana kana yace.
"Gaskiyane mariam barinki gidan ya zama dole saboda tseratar da rayuwarki daga shiga hatsari... A gaskiya samun irinki sai an tona, na yaba da k'ok'arinki sosae wajen ganin kin kawo farinciki a cikin gidan nan ke mutunce wacce ta cancanci zama cikin al'umma saboda muddin kika cigaba da gudanar da aekin nan rayuwarki na iya salwanta kuma kinga mafarinshi jiya."
"But..."
"Bana buk'atan jin komai daga bakinki mariam, kamar yadda kikace kin d'aukeni tamkar mahaifi zanso na miki magana kiji cause this is more like umarni, kamar yadda na buk'ace da farko yanzu na janye,ki shirya gobe in allah ya kaimu zaki koma gun iyayenki."yafad'a cikeda tausaya wa kansa tareda shirin dannan button dan tafiya da sauri miemie ta k'irashi tsayawa yayi batareda ya juyo ba.
  A hankali miemie ta tako zuwa gabansa ta tsuguna tad'aura hannunta kan k'ofofinshi.
"Kamar yadda kafad'a da farko sawa kayi a d'aukoni daga gaban iyayeni saboda samun lafiyarka, abba karkayi tunani dan biyana da akayine nake nan gidan ko d'aya,abba kudi basu bane a gabana banida burin daya wuce cetun al'umma na k'udurta a raina da izinin allah na zama silar warkewarka kuma kuwani cikakken mutum yana k'aunar ace ya cika burin alkhairi domin samun ladan mahaliccin mu sannan yakan kasance cikin bak'in idan har k'udurinsa bai cikaba, meyasa kai da kanka kakeson hanani aekin samun lada? Meyasa bakaso na samu ladan al'umma?"
Zaiyi magana tayi saurin katseshi.
"Kamar yadda kafad'a kai kamar uba kake a gurina nima kamar 'ya nake a gurinka,kuma kowace 'ya tana burin taimakawa iyayenta ta kowani hanya no matter the circumstances saidai in bankai matsayin ba,kasani a matsayin Murad, Zarah da Amatullah abba kana ganin su bazasu risking rayuwarsu wajen ceton taka ba? Inada ikon Samar maka lafiya meyasa kake k'ok'arin hanani saboda wani dalilin da babu Wanda ya isa ya maka sai Allah, abba so kake allah ya hukuntani da laifin sa6a alk'wari, ko kamanta akwai inda allah yake cewa cikin suratul Isra'ila aya ta 224 inda Allah (SWA)  ke cewa _kuma ku cika alk'awari, lalle alk'awari abun tambayane a gareni_ abba ko kamanta na d'auka maka alk'warin kasancewa daku komai rintse harsai allah ya baka lafiya..."hawaye ya gangaro mata.
"Banaso nakasance  cikin Wanda allah zaiyiwa hukunci ranar gobe k'iyama saboda wannan laifin kuma nasa a raina babu Wanda ya isa yamun abunda allah bai munba."ta share hawayenta tareda k'ak'alo murmushi.
"Abba babu inda zanje nabar ubana cikin wannan halin."tana kaiwa nan tamik'e tanufi hanyar fita daidai lokacin murad ke shigowa, kallo d'aya ta mishi ta ra6a ta gefensa ta wuce.

_The next day…_

Da walwala da fara'a kamar kullum miemie ta tashi,abunda ya mugun bata mamaki yau babu walwala fuskarsu Zarah duk wace hanyar da data had'asu kaucewa suke, a dining room ne hankalinta ya tashi ganin yau babu murmushi fuskar mai martaba koda ta gaisheshi ciki ciki ya amsa, jiki ba lakka ta zauna tareda kallon murad inda yayi tamkat baisan da mutum a gunba, kowa yak'i bari su had'a Ido sannan babu mai cewa fit in fact komai yakoma kamar farkon zuwanta, jiki a sanyaye tashiga breakfast dukda bawani abun kirki ta iya ciba, kowa ya watse batareda ya kalleta ba sai mai martaba.
Mik'ewa tayi da nufi turashi zuwa filin exercise yayi saurin dakatar da ita, yau sarauta ya motsa.
"Karki wahalar da kanki Doctor dan bana buk'ata."
Murya a raunane tace.
"Saboda meyasa abba? Am your Doctor."
"That was then, yanzu i've no business with you, saboda you don't longer exists in this palace, kiyi gaggawar barin gidan shine buk'ata ta in ba hakaba zansa a fitar dake."yana kaiwa nan ya kunna engine na wheelchair nashi yayi gaba.
Daskarewa miemie tayi agun tana mamakin kalamun mai martaba da sauyawansa lokaci d'aya.
Cikin azama tafice da nufin zuwa shashin hajjo sukayi kici6is da mermu a hanya.
"Doctor what's wrong?"
Miemie tayi murmushi
"Yaushe kika dawo?"
"Yanzu dawota nazo sanar da hajjo... Is anything wrong?"ta tambaya.
"Not at all kawai inaso muyi wata 'yar magana da hajjo."
"Bari na sanar...
"Noo jeki kawai zan shiga da kaina."
Zatayi magana miemie takatseta tareda murmushi.
"Don't worry mermu, am used to everything in this palace, just go."
Bata saurari abunda mermu data ceba tayi shigewarta ciki, a parlor ta hangi hajjo kishingid'e ga fruits gefenta fuskarnan tata kamar kullum q dishe.
Sallama miemie tayi hajjo ta d'ago kai tareda amsawa ciki ciki.
Zata k'ariso hajjo tayi saurin dakatar da ita.
"Stay still I didn't asked you to come in, what are you here for?"ta buk'ata hankalinta naga TV.
Miemie tayi gyaran murya tareda cewa.
"Magana nakeson muyi."
"Kuma waya gayamiki ana magana dani ba tareda AP ba."
"Am sorry but it's urgent please do me this favour."tafad'a pleadingly abunda miemie bata ta6a yiba.
Hajjo ta watso mata kallo tareda d'auke kai.
"May I come in?"miemie ta buk'ata.
Da hannu tayi mata alama ta shigo, miemie ta sauk'e ajiyar zuciya tareda k'arisowa ta zauna a k'asa d'an nesa da ita.
"Karki 6atamun lokaci minti biyu na baki."cewar hajjo.
  Miemie ta girgiza kai kana tafara.
"Dama akan mai martaba ne."
Hajjo ta d'ago a dake tana kallonta.
"Sai akayi yaya?"tafad'a bayan takai water melon baki.
Miemie ta d'an matso kusa da hajjo a hankali tafara magana.
"Narasa abunda ya samu abba daga jiya zuwa yau, i've never seen him in this mode ever since I came into this palace, komai dana sani game dashi yau babu,yak'i na masa magani yau kuma before I could speak he chased me out sab..."
"K'ararsa kika kawo mun kenan?"hajjo ra katseta a dak'ile tana cin tufa.
Sake biki miemie tayi tana kallonta.
"Uhum?"ta buk'ata bayan ta ajiye abun hannunta ta tashi zaune.
Miemie ji tayi zuciyarta tafara tafarfasa, meyasa hajjo ke mata haka, runtsa Ido tayi tanason kauda 6acin ran kana ta bud'e Ido tareda d'an murmushi.
"Nasan fushi yake dani amma Inaso dan allah ki masa magana ki fahimtar dashi karya damu da lafiyata babu Wanda ya isa yamun abunda allah bai rubuta ba,kuma as far as ina gidan nan da taimakon allah saina Samar masa lafiya..."
"Dakata."hajjo tatseta tareda d'ago mata hannu.
"You're a doctor aren't you?"ta buk'ata.
"Yes I am why?"
Hajjo takalleta na d'an dak'iku kana tace.
"Ko wani likita yasan yadda za gudanar da aekinsa doctor basai ansa wani cikaba, you're brought into this house to cure the king right?"
Nodding kai miemie tayi a hankali.
"Okay... If you can't handle your job yourself then banga amfanin ki ananba, kitafi kamar yadda ya buk'ata inkuma kece bakyaso ki kuka da kanki amma gargad'ina na k'arshe karna sake ganinki anan da wannan maganan, your two minutes are over now get out."tafad'a tana nuna mata hanya.
Miemie ta kalleta kwalla yafara taruwa a idonta ta mik'e ahankali tanufi k'ofa rai kafun hajjo ta katseta.
"Barin ki gidan nan shine kwanciyar hankalin kowa."
A hankali miemie tajuyo hawaye ya zubo ta dubi hajjo
"A nawa tunanin aure shine abunda yafi komai muhimmanci a duniya,ma'aurata ansansu da rufawa juna asiri dakuma tsayawa juna ta kowani hanya but you proved me wrong hajjo,as a daughter bazanyi k'asa a gwuiwa ba wajen taimakon abba, idan baki taimakamun ba nasan allah zai taimakamun, kiyi hak'uri in na 6ata miki rai..."tana kaiwa nan batareda ta waiwayi hajjo ba ta fice abunta tayi d'akin zarah.
   A hanlali tabud'e ta hangi zarah zaune kan gado gaba d'aya ta Lula duniyar tunani hawaye na zuba a idanunta.
Jiki a sanyaye ta nufeta harta k'arisa kusa da ita ta sauna.
"Zarah..."ta k'isa sunanta.
Ahankali zarah ta kallota, miemie na shirin magana zarah tayi saurin mik'ewa ta nufi k'ofar fita batareda ta saurare ta ba,binta tayi dakallo gaba d'aya jikinta ya gama sanyi batada wata mafita, kowa ya fita hark'arta a gidan rasa gun wa zataje ahankali zuciyarta ta raya mata.
"Emperor."ta mik'e tsaye.
"I think emperor will help me."
Tanufi k'ofa ta tuna da baya gidan gaba d'aya, duba agogo tayi kusan sha biyu na rana, ficewa tayi tanufi d'akinta da anriga an fitar da macijin.
Mermu tashigo ta sameta ganin miemie tana cikin damuwa tafara bugan cikinta, miemie tayi murmushi.
"Mermu ince ke kika cemun rik'e sirri nada kyau, kinga na koyi rik'e sirrina karki damu I'll be fine."
Jin abunda miemie tafad'a yasa mermu yin shiru tareda ficewa miemie tabita da kallo tayi murmushi.

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora