chapter 54

1.7K 147 10
                                    

In dedication to
Miemiebee 👄

******
Gaba d'aya jikinta kyarma yake tana cikeda tausayin kanta,ji tayi gaba d'aya duniyar tai mata zafi batada wani sauran farinciki, shikenan rayuwarta batada wani sauran amfani tunda ta rasa farin cikinta, tayi mugun wauta data bari son maheer ya mata mugun kamu, koda yake so babu ruwanshi, sai yau ra tabbatar da ita wawuyace data kasa yarda da maheer da miemie soyayya suke,maheer shine farin cikinta gashi yana neman su6uce mata, kallonsa kad'ai sata farinciki yake shine ma dalilinta na zuwa rashin ganinsa a asibiti wunin yau kawai ta gwada kiran layinsa yafi a k'irga bai dagaba hakan yasa hankalinta ya tashi ta fake da zata gaida ummi shine mummynta ta bata aeka ga kuma abunda tazo ta tarar Wanda yafi komai d'aga mata hankali, hawaye ne masu zafin suka gangaro kan fuskarta, tayi nisa cikin duniyarta har batasan ummi tagama wayarba saiji tayi ta k'ira sunanta tayi saurin share hawayen.
"Lafiya jameela? Kukan me kike wani abune ya faru?"ummi ta tambaya cikeda damuwa.
Murmushin yak'e tayi ta girgiza kai.
"Ba kuka nakeba ummi abune ya shiga idona yama fita..."tafara goge idon kamar da gaske.
ummi ta kalleta nadan dak'ik'u kana tamata sannu bayan man taita janta da hira amma kwata kwata hankalinta bai gun yanaga maheer,kusan ko yaushe tazo gidan tana had'uwa dashi amma yau ko alamansa babu duk da ayanzu tanason hana zuciyarta son ganinshi amma ta kasa kuma tanajin nauyin tambayar ummi inda yake ummi ta katse mata tunani.
"Ko zaki shiga ki duba yayan naki tun jiya baiji dad'i ba..."
Gaba d'aya hi tayi zazza6I na neman rufeta saitaji dama ita ciwon ya kama ba shiba.
"Subhanallahi...ya jikin nashi hope da sauk'i?"
"Alhamdulillahi za'ace dan bai jima da samun bacci ba tun safe Muke Abu d'aya yak'i akaishi asibiti sannan yaki cin abinci balle shan magani dakyar nasamu yasha tea d'azu nan ma saida na kusa neman miemie sannan na d'aura masa ruwa saboda yasamu k'arfin miki yanzu dai ya samu bacci lamarin maheer na damuna yana abu tamkar yaro k'arami ace mutum Sam baison magani..."ta girgiza kai cikeda takaici.
"Allah yabasa lafiya."shine kurum abunda ta iya cewa.
Da farko tak'i zuwa dan tana tunanin idan idonsa biyu haduwarsu bazatayi kyau ba dan kashi yafita daraja a gunsa, saida ummi tayi kafun ta yarda kamar 6arauniya tabud'e k'ofar d'akin bayan tayi sallama, lumshe Ido tayi jin kamshen turarensa ya naushe hancinta ahankali tabi d'akin dakallo komai tsaf tsaf har idanunta suka sauk'a kanshi.
Kwance yake yana bacci gaba d'aya yau kawai ya zabge kamar bashiba, kyakkyawar fuskarsa ya Kara haske bakinsa a bushe, wani tausayinsa ne hade da sonsa suka taso mata ahankali ta k'arasa bakin gadon hawaye suka cika mata Ido, ruwan da ummi tasa masa ya kare, bayan ta cire masane ta zauna a kasa daidai saitin fuskarsa tana kallonsa tana hawaye cikeda tausayin kanta, rashin cin abincinsa yafi komai dagamata hankali dan murmushi taxi ganin ya dukunkune gu d'aya kamar wani yaro karami,mik'ewa tayi tareda gyara masa comforter kafun taxi waje bayan tasoba.
Kitchen tanufa inda ummi ke shirin nema masa Abu mai sauk'i ta zai iyaci idan ya farka, amsa tayi daga hannu ummi bayan ta insisting zata tayata, Abu mai sauk'i ta dafa daidai marar lafiya duk abunda take ummi na kallonta cikeda sha'awa dan harga allah tanason jameelah.
Bayan ta gama tashirya komai ta tararda ummi falo tana waya bayan tagama ta dubeta.
"Sannu da aeki jameelah, allah yayi albarka..."
"Ba komai ummi, ni zan wuce..."ta jawo mayafinta
"Aah d'aga yanzu kuma..."
"Eh wallahi gari ya fara rufawa..."
"Kijiki da wani zance Nan ba gida bane?"
Dan murmushi tayi batace Komai ba.
"Kafun ki wuce ki gaisa da yayan naki mana, nasan yanzukam ya farka."
Batayi musuba ta taya ummi d'aukar warmers na abinci tabi bayanta.
Zaune yake kan sallaya ya idar da sallah, ya sauya kayan jikinsa alamar wanka yayi, jiransa sukayi harya idar da add'uarsa, buyewa bayan ummi meelah taxi dan bataso ya ganta balle annurin fuskarsa ta d'auki.
"Ummina shine ko ki tasheni nayi sallah..."ya zauna gefenta tareda kwantar da kansa kan kafad'arta.
"Afuwan... Ya kufayin jikin?"
"Alhamdulillahi na samu sauki..."
"Masha Allah bazan tabbatar da hakan ba sai kaci abinci..."
Yamutsa fuska yayi ya juya zai kwanta, a dole ummi tasa zauna ta mik'a masa plate.
"Maza ci ina kallonka, inba hakaba d'ure zan maka..."tafad'a ba alamar wasa tattare da ita.
Meelah dake bayanta tad'anyi dariya sai a sannan ya lura da ita, wani mugun harara ya banka mata alamar bana wasa dake.
"Zaka daina harararta ko yaya... Ka gode allah daba ele tamaka ba."
kauda kai yayi ta had'e baki.
"Yah jikin yah maheer?"
"Da sauki..."ya amsa a dak'ile kafun yakai spoon d'in farko ya lumshe Ido, dukda baida appetite tsintar kansa yayi da cin abincin sosae ummi na zolayarsa.Meelah kuwa ta kafesa da idanu tana wani sussunne kai shiko ko kallon inda take baiyiba.
Saida ya gama yace
"Nagode ummina..."
"Thanks to meelah data girka maka gashi kaci sosae..."
Yanajin haka yayi tsit tareda kauda kai itakuwa kanta k'asa ummi ta dubeta.
"Taimaka ki ballawa wa yayanki magani ina zuwa..."tamik'e tanufi k'ofa tanacewa
"Ki tabbata yasha..."
Bayan fitan ta ta mik'e tanufi saman side drawer inda taga tablets d'in tahau ballewa kana ta tsiyaya ruwa
Bayan ta gama tadubeshi tareda mik'a masa ko kallota baiyiba ya tattara hankalinsa kan wayarsa baimasan da mutum a gunba.
Tsaye tayi itama ganin bai kulata ba.
Daidai fuskarsa takai ya buge hannun magungunan suka watse,cikeda takaicin abunda yayi take kallonsa,tayi saurin maida hawayenta dan karya gani.
"Get out."ya umurta
"I won't..."tabashi amsa kai tsaye.
Da mamaki yake kallonta itakuwa tajuya tareda sake 6alle wasu, shikuwa martanin da ta maida masa ne yabasa mamaki da meelah bahaka takeba dukda Sasha mata irin haka bata ta6a tamkawa ba sai yau.
Baisan sanda ta gama ballewa ba sai ji yayi ta toshe masa hanci, da sauri ya bud'e bakinsa tayi saurin cusa masa magunguna ta kifa masa cup a baki, babu yadda ya iya ya had'ewa kafun ta sakar masa hanci.
Hayayyako mata masifa zai fara ta katseta.
"Next time don't play with your medications please...Get well Soon."tanakaiwa nan ta d'auki plates tafice batare da ta dubeshi ba.
Sake baki yayi yabita da idanu kamar wani soko, kwafa yayi alamar zasu gamu.

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Onde histórias criam vida. Descubra agora