In dedication to
Miemiebee 👄******
Gaban miemie ne yabada dam,a rikice bakinta ya furta
"What?"
"Yes nasanshi but I can't really remember where..."
Restlessly miemie tasake damk'e hannunsu Wanda sanadiyar haka ya d'ago ya dubeta da sauri, a hankali la66an bakinta ya furta.
"Think emperor..."
Juyawa yayi ya kalli 'yan cikin motar, ganin babu mai kallon inda suke ya zaro wayarsa a aljihu ya saita daidai inda mutumin ke biyan kudi ya snapping, duk abunda yake miemie na kallonsa baki bud'e kamar munafuka tace
"What are you doing?"
Baikulata ba ya cigaba da abunda yake, turawa sadisu yayi yana neman karin bayani.
Ko minti d'aya baiyiba sadi ya turo masa
_"ubalili sale; he was one of the main palace guard but how comes he's here? He was nowhere be found ever since aunt mareeyah's incident..."_
Ohh dama anan yasanshi, _was_ yana nufin not anymore kenan yanzu baya yiwa palace aeki,sannan tun incident din aunt mareeyah ba'a sake ganinshi ba me haka yake nufi?
"Something Is definitely fishy."ya fad'a a hankali
Confusingly miemie ke kallonsa, karbar phone din tayi ta karanta dasauri tad'ago ta dubeshi.
"I don't trust that guy emperor am sure he has something to do with aunt mareeya's disappearance..."
"That's what am thinking...hakan na tabbatar dacewa yasan inda take, we'd have to follow his footsteps..."
Duk da yasan it's dangerous but yadda suka disguising kansu allah sa baizai ganeshi ba, duban miemie yadda Wanda gaba daya sai muzurai takeyi worriedly tace.
"Let's get out of this car ASAP kafun ya ganeka...that might get us into trouble especially kai...zamu iya binsa ta wani mota"
kusan seconds biyar yana kallonta kana ahankali bakinsa ya motsa
"Calm down Duckie, trust me he won't be able to recognize me..."
Still kallonsa take da alamar har yanzu atsorace take.
"Insha allah he wouldn't get to recognize either of us, let's keep on acting remember you're larai and I'm..."
"Audu..."ta k'arisa tana yar dariya hakan yasa yadan murmusa har dimple nasa ya fito yasa hannu yana gyara artificial beard dayasa.
Ana cikin haka musa ya iso gurinsu tareda lek'o kansa cikin motar yana watsawa miemie mugun kallo itama tana mayar masa.
"To larai kike kowa, sai gyarawa passenger ya zauna."
Zatayi magana murad yayi saurin hanata ta hanyan matse hannunta,wato miemie tazama a tsakiyarsu jikinta ya gogi na d'ayan.
Harzai zauna murad yayi saurin yiwa miemie alamar data koma jikin window tako koma shi ya zauna a tsakiya, da mamaki miemie ke kallonsa yawani gimtse fuska tareda gyara rawanin kansa rabin fuskarsa a rufe.
Bayan mutumin ya zauna har musa ya rufe k'ofar ya dubi murad tareda masa sallama yana mik'a masa hannu.
Ahankali murad ya mik'a masa hannu sukayi musabaha yana gyara hannun rigarsa kar agogon hannunsa which is worth 500 thousand ya fito, amma dukda haka saida mutumin ya d'ago fuskarsa yana kallon murad curiously sanadiyar laushin cikin hannunsa, gakuma kamshin turaren dayaji,ganin haka murad yayi saurin cire hannunsa tareda ce masa sannu da fulatanci.
Murmushi yamasa alamar yagane, maida kallonsa yayi kan miemie inda kanta naga window tana kallon yan talla da marok'a cikeda tausayawa mutane kowa naharkar gabansa.
Canjin d'arin hannunta ta mik'a wa wani gurgu tareda masa murmushi ya amsa yana godiya.
Duk abunda take idanunta murad a kanta saida ta juyo yayi saurin kauda kansa gefe yasha kunu.
Daidai lokacin da motar ta tashi kenan murad ya runtsa Ido tareda yamutsa fuska dan komai sabo ya zamar masa.
Tunda suka d'au hanya wani zazza6I zazza6I yafara dirarwa murad ga kansa dake sarawa, miemie kuwa kanta naga window sai kalle kallen cikin gari take tana mamakin yadda gombe tafi bauchi sau dubu dan cigabansu daban ne ga tsafta dabin dokoki,kuma kowa harkar gabansa yake while murad ko runtsa idonsa yayi har a lokacin hannun miemie na cikin nasa.
Sun wuce roadblocks da dama suna wucewa batareda an cajesu ba,mutumin nan kuwa earpiece tareda rufe idanu ya jinginar da kansa,masu hira k'asa k'asa nayi ciki kuwa harda na palace inda suke jajanta abubuwan dake faruwa kuma ta murad ma yafi yawa,shidai kawai jinsu yake zuciyarsa na k'una,miemie ta kallo inda yake taga har a lokacin idanunsa rufe tacikin glasses din,wani tausayin sane yakamata ta runtsa Ido cikeda takaici gashi driver yasa wata shegiyar wak'ok'in hausa wanda hakan ba k'aramin k'arawa murad ciwon kai yayi ba,hatta ga miemie sai yatsine fuska take tamkar tayi kuka,har suka wuce kaltungo kusan k'arfe bakwai na safe,alokacin sosae zazza6i ya rufe murad jikinsa ya d'au zafi.
Jin zafin hannunsa yasa miemie d'agowa tadubeshi cikin sauri...
Hannun datakai kan goshinsa ne yasa shi cire glasses din ya bud'e idanuwansa dasuka sauya kala yana ya sauk'esu a kanta daga yanayin fuskarta zakasan halin data shiga na damuwa.
"Are you sick?"la66an bakinta ya furta batareda murya yafito ba.
Dan murmushi yayi tareda girgiza mata kai ahankali.
"Am fine..."ya mayar mata ya fatar baki.
"Your temperature is very high..."tafad'a cikeda damuwa sosae.
Bata San sanda tace
"Driver wait..."da sauri ta runtsa Ido tareda cije harshe saboda kwa6an datayi.
Murad ko zaro Ido dubanta.
Jin abunda tace yasa mutane duka aka juyo ana kallonsu harda mutumin dake gefensu da sauri miemie ta wayance da cewa.
"Direba ka shaya do allah zan seyi abu a sago inbanci ba mutua zanyi..."ta murda harshenta tana rik'e ciki.
Jin abunda tace yasa mutanen juyawa suna maganganu da mita har a lokacin mutumin gefensu na kallonta, murad ko so yake ya tambayi miemie uwar me zatayi a waje har take neman tona musu asiri,irritatedly yafara magana da fulatanci Wanda babu abunda miemie tagane sai Ido datake binsa dashi shiko cewa yake.
"Larai kincika fitina aradu,saida nace miki kiyi zamanki ba lafiya kikeda ba kin nace sai kinzo gashi tun yanzu kinfara fitintunun banza da hofi,kwarankwatsa wani abu yasamu jaririna nida kene..."ya k'arishe tareda gimtse fuska Wanda a maganar tashi babu abunda ta fahimta sai murmushi kawai datayi shiko yayine saboda wancan mutumin yabar kallonsu.
Duk abunda suke idanunsa nanan kansu har driver ya tsaya wani kauye ya parking gaba kadan da wasu shaguna.
Zai fita tayi saurin girgiza masa kai alamar ya zauna.
"Kibarni zan shiyo kayana kuma kika biyoni aradu kasheki zanyi."tafad'a tareda murguda baki wanda hakan bakaramin dariya yabasa ba yayi saurin gimtsewa.
Itakuwa ganin kar idan yabita mutumin nan ya zargi wani abu yasa tayi hakan and she really needs to get something,bud'e mata k'ofar akayi dan nunawa tayi bata iyaba.
Fita tayi tareda hamdala tana fatan tasamu abunda take nema.
Ahankali ta k'arisa bakin shagunan nan tana baza idanu, takoci sa'a akwai chemist hamdala tayi tareda k'arisawa gurin.
Panadol ta amsa dukda tasan balallai bane murad yasha, kana taje na provision tanason amsar faro but tana shakkar kar a zargi wani Abu dan tasan ko mutua zatayi murad bazai ta6a amsar pure water ba.
Rasa abunyi tayi can idea ya fad'o mata, faro ta kar6a tareda turawa cikin kuddin kayan hannunta had'eda maganin, gurin wata mai arawa tace ta amsa awaran Hamsin ganin awaran ma kad'ai zuciyarta ta fara tashi but dole tayi hakan saboda gudun kar afara suspecting d'insu.
Bayan ta koma gurin motar mutane har sun fara masifar tana 6ata musu lokaci,LOL zanso kuga yadda ake shiganta.
Tana zama ta d'ago ledar awaranta tana yak'e baki.
Ganin abunda ke hannunta murad yayi saurin rufe Ido tana yamutsa fuska, dama tasan za'a rina.
Idanunta ya rufe tsam tarik'e numfashi tareda gutsuran d'aya a baki ta had'iye da sauri.
Da mamaki murad ke kallonta daga yanayin yadda takeyi yagane a dole takeyi, saiwani yatsina yake kamar shiyake ci,dariya ne cunkuse a cikinsa.
Miemie kusa a hannunsa ta basa lafiyayyen mutsina,zai bud'e baki tayi saurin cusa masa awarar a baki a zuciyarta tana dariyar mugunta.
Babu yadda ya iya dole ya had'iye zuciyarsa na juyawa, wani mugun kallo ya watsa mata cikin dabara tai masa gwalo.
Ruwan dake cikin kayanta ta nuna masa, hannu yasa zai d'auka tayi saurin buge hannun tana murmushin mugunta tareda girgiza kai.
Puppy face yamata kamar wani yaro tabashi ruwan tayi saurin ciro masa magani alamar yafara sha.
Kallonta yakeyi ba gaggautawa sai a sannan yagane dalilin dayasa duk tayi hakan,dama fitarta saboda shi ne sannnan tasan baison magana and she's trying to force him ta wannan hanyar.
Shikansa baisan sanda hannunsa yakai kan maganin data 6alla masa ba ya amsa,da kanta ta bud'e masa ruwan ta mik'a masa ya amsa.
Ahankali ya sakar mata murmushi bakinsa ya furta.
"Thanks" daidai jinta.
Harga allah sun ma manta wani mutum dake gefensu,shikuwa duk idanunsa a kansu.******
Zazza6in murad yalafa itakuwa miemie tayi dabarar yarda sauran awaran kan, tundaga lokacin babu Wanda yasake cewa komai a cikinsu harsuka wuce savannah.
Daidai lokacin motarsu ta samu matsala gashi dungurmin jeji ne bayan minti talatin da tsayuwarsu.
Kowa ya fita amotar banda murad da miemie Wanda yayi dana sanin meyasa sukayi hakan tun farko gashi ranar kamar hadin baki babu motoci sosae kan hanya.
Ganin babu kowa cikin motar miemie tace.
"What are gonna do emperor?"
"Don't know...and Wannan motar babu alamun gyaruwarta yanzu and am sick of all this act stuff."
Ciro wayarsa Wanda ya tabbatar a lokacin sadisu ya gaji nemansa, yana kunnawa kuwa k'iran sadi na shigowa.
"Hello yalla6ai..."
Kafun yasake magana murad ya katsesa.
"Am sick of all this sadi...come with a car ASAP and you've to drive fast banason jira..."
Miemie idanunta ya hango kamar wani na la6e, so take tanuna masa but sai magana yakeda sadi yanai masa bayanin inda suke.
"Am coming..."kafun yace wani Abu tayi wuf tafice daga motar.
Daidai inda mutumin kan yake waje tak'arisa d'an nesa dashi kad'an inda bazai gantaba ta boye bayan wani bishiya saiji tayi yana cewa.
"Allah k'ara maka martaba Tabbas su nagani tun a Tasha na gane yareemah murad ne macen ne dai bansan ita wacece ba,tun a can na had'a plan da drivern yayi kamar motar tasamu matsala a inda babu Wanda zai iya kawo masa d'auki..."bayan dan shiru ya kwashe da dariya.
"Yalla6ai Kabamu minti goma zuwa sha biyar saidai akai muku gawar murad dan yanzu yarana sunakan hanya baifi minti biyar su k'araso inda mukeba...insha Allah baza'a samu matsala ba"
Ae kafun ya k'arisa magana miemie tajuya da mugun sauri hankalinta in yayi dubu ya tashi.
Kallon gurin tayi taga gurin duwatsu ne da bishiyoyi gashi sunyi nesa da sojoji, wato dama ya ganosu tuntuni sannan ya hada baki driver saboda a kashe murad.
Isarta bakin motar har murad ya fito, haki tafara tanason sanar dashi abunda ke farua shiko ganinta haka yasa ya k'ariso yanason tambayarta.
"Emperor there's a problem..."
"What?"ya tambaya curiously
"wancan guy din ya ganeka tun a gombe,he heard what we were saying earlier kaganshi can he's making a call over there...they're planning to kill you right here"ta nuna masa inda mutumin yake gaba daya jikinta na rawa.
"We need to get out of here ASAP..."
Kafun tayi wani yunkuri ya jawo hannunta da sauri, batareda kowa ya luraba suka shiga cikin jejin da mugun gudu.
Saida sukayi tafiya mai mugun nisa suka Wani bishiya, Janta yayi ya zaunar da ita gaba d'aya sai haki take k'ishin ruwa kamar zata shid'e.
D'ago wayarsa yayi babu network gaba d'aya.
Tsaki yaja Karo na talatin ya dubi miemie yace.
"They can trace us easily..."
Cire rawanin kansa yayi tareda rabawa biyu ya tsuguna gabanta yajawo k'afarta ya d'aura tsakiyar takalminta na both kafan tanason tayi magana amma ta kasa.
Saida ya d'aura nashi yad'ago ya dubeta.
"Am sorry Duckie... But yakamata mu Kara gaba kad'an kila mu samu ruwa"
D'aga masa kai tayi kurum ya jawo hannunta suka fara tafiya, bayan minti talatin da tafiyar ya hango wani guri inda ruwa yake gudu sosae...zaunar da ita yayi inda tagama galabaita yadubeta Karo na farko cikeda tausayinta a idonshi dan ya tabbatar rabonta da ruwa tun jiya...goran data rik'o hannunta ya amsa yace
"Am coming..."batareda ya saurari amsartaba ya juya zuwa gurin wannan ruwan.
Bayan yasha wahalar k'arisawa gurin tareda d'ebo ruwan a goran.
Juyawan dazaiyi inda take yaga wayam babu ita.
Goge idanunsa yayi ya bud'e amma babu miemie, waigewaige yahauyi amma duk a banza babu miemie babu labarinta.
*****
Vote, comment. And share
STAI LEGGENDO
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Storie d'amore"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...