chapter 8

2.3K 166 5
                                        

IN DEDICATION TO MIEMIEBEE👄

  Thousands of years ago, one man was chosen by the divinity to be a prophet of peace and destined to be the founder of a new religion. He was the great prophet Muhammad SAW, the man who give birth to ISLAM and who was given a sacred knowledge of QUR'AN on a sacred month better known as RAMADAN ★★★
   may the festival of lights be the harbinger of joy and a prosperity, as the holy occasion of RAMADAN is here and the atmosphere is filled with the spirit of mirth and love, here is hoping this festival of beauty brings your way, bright sparkles of contentment, that stay with we all through the days ahead ★★★

********

"Zo nan mamana!" Ikko ta ware mata hannu,make kafad'a tayi tana murgud'a baki

Ups! Gambar ini tidak mengikuti Pedoman Konten kami. Untuk melanjutkan publikasi, hapuslah gambar ini atau unggah gambar lain.

"Zo nan mamana!" Ikko ta ware mata hannu,make kafad'a tayi tana murgud'a baki.

Da gudu ammar yaje ya fad'a jikinta, ganin ammar jikin ikko taje gadan gadan ta janye ammar tare da tunkud'asa gefe ta rungume ikko.

Fad'uwa ammar yayi tare da fasa ihu.
Da sauri ikko ta kawarda miemie suka d'aga ammar itada sadeeq.Mamace tafito tana tambayar lafiya.

"Tura ammar tayi!" Cewar faruk Mama tayi mata wani kallo kana tace
 
"Miemie kifita idona! Kina sake rashin hankali anan zan iya bugunki!!"Wage baki tayi zata fara kuka.

"Kina 6aremun baki anan yanzu zan miki shegen duka!" Mama tafad'a tayi shigewarta kitchen itada ikko
  
Faruk ne yayi dariya yana cewe"Ammar kaikuma kadinga bari mace na dukanka son ranta kana 6are baki!!"
  
Ammar yana kallon miemie yace"Ya faluk k'alfi take dashi uukana takeyi sosae!"

"Inta bugeka ka Rama!" Cewar hydar.
 
"Saiku gayamun tayaya zai rama bacin kuma ba barinku takeyi ba! Acikinku waye bata duka?" Cewar sadeeq

"Wallahi nidai bata isaba, kyaleta kurum nakeyi Dan k'arama ce da badan hakaba ae saita kwana asibiti" khaleel ya fad'a.

Zuwa tayi zata naushe sa yayi saurin rik'o hannunta, again kokuwan kwacewa hularta ta zame, malu d'inta ya bayyana.
  
A tare dukansu suka fashe da dariya banda sadeeq, dama hajja tace karya sake wani yai mata dariya.
  
Gadan gadan tayi gun faruk dayafi kowa dariya tahau ruwan cikinsa takamasa da dambe.Hydar ya fincikota tako kwad'a masa Mari tana huci.Khaleel kwance yana dafe da cikinsa da miemie ta nausa.Nan take kowa tasamu dukansa takeyi.

"Mama anya miemie ita d'ayace?" Cewar khaleel

Sadeeq dake janyeta yace "Kaikuma kama bakinka ko na mangareshi, karka sake kafara maganan banza anan!" Yafad'a tare da d'agata.

"Yarinya fingel da ita sai shegen uban k'arfi, wallahi kika sake tab'ani sauna 6allaki!!"

"Bishmillah!" Tafada tana murgud'a baki tana harara.

"Mik'ota nan sadeeq!"cewar mama data d'auko tsintsiyar kwakwa.
 
"Mama kiyi hak.... "

"Zaka mik'ota ko saina had'a dakai!"
 
Kanma ya sauk'eta miemie ta dira, kan k'iftawar bismillah an nemeta a falon an an rasa.
  
"Ku kuma kunsan halinta babu wanda ta ragarwa, saikuyita biye mata kuna tsokanarta!" Cewar ikko.

*****
   
  
Washegari ta kama monday, as usual k'arfe shida ikko tashiga ta da twins, dama ammar take fara d'agawa saboda yanada sauk'in tashi, bayan tamishi wanka tazo ta daga miemie Dan sai ankashe minti talatin kafun ta tashi.
   
"Mamana tashi kiyi wanka akwai makaranta!" Tafad'a tana d'agata.

K'wace jikinta tayi "O oo balan jeba!"

"Tashi ko saina k'ira mama!"Dasauri ta mik'e tace "a'ah na tachi!"

  *****
Bayan anmata wanka an shiryasu suka nifi gun breakfast, kowa cikin shirinsa banda sadeeq daya gama a shekarar.

"A'ahhh su gwuigwui an girma, ba rikici yau kenan? Sadeeq yafad'a yana mamakin bata kukan kin son zuwa makaranta.

"Ae ya deeku bana kukan banja, daliya akemun in nayi!"
  
"Yauwa Good girl haka akeso!"

"Tanchu bad boy!" Tabasa amsa tafara humming national anthem.

Dariya faruk yayi "Yo su an iya national anthem! Kwananku nawane da shiga makarantar?"
 
"Kai kafiye neman tsokana,sannan kasan hakinta sarai!"

Miemie ta gefen ido take kallon kowannen su.
 
Hydar ko kulasu baiyiba dan 'yan miskilancin sun motsa.
 
"You guys should be fast its getting to 7:30" cewar mama dake fitowa daga kitchen

 
Khaleel yace "yaa sadeeq yau ma kai zaka kaimu?"
  
"Aah baba driver zai kaiku yana jiranku a waje!"
    
Kowa ya mik'e suka shiga side din baba don masa sallama.

Da gudu ta fad'a kan baba tana dariya"Mama na kintashi lafiya?"
  
"Lafiya!"
 
"Babana kaifa?" Shima ya amsa
Miemie tace "Baba anshie mushayi colour!"
 
"Mama na kullum ne sai an siya colour?" Yafad'a yana kallonta.
 
"Umm ummm ehmm ruler akashe mushaya!"

 Baba yayi dariya Dan kullum a duniyar Allah in zasu tafi makaranta to fa saitace ance su sayi kaza.
  
"Miemie ayya, baba ayya takeyi!" Cewar ammar.
 
Miemie ta harareshi "Kaje fisari lokacin da aka fa'a!"
 
Nan fa musu yafara kaurewa
Baba yadubi hydar yace."D'auko 500 a d'aki!"
 
"Baba miemie k'arya takeyi....
 
"Shhhh! Ya isa"

Bayan hydar yadawo yace"Saika confirming kasiya musu!"
 
"Toh baba"

Ya dubesu duka yace "Allah muku albarka adawo lafiya"
 
Bayan fitowarsu mama tace "Miemie come and finish your breakfast! Faruk d'aukar mata Jakarta!"
 
"Mama kullum fa haka takeyi saboda ace na d'aga mata!" Yafad'a yana tura baki.

"Ae kaine babba sai kaci girman koh!"Tana fad'a tashige kitchen. Hararar miemie yake tayi.Basu Ankara ba miemie tad'auki tea ta kwara masa a jikin uniform.Ihu yasa ga azabar zafi.

miemie ta murguda baki yace"Kur kashake harara na!"Ganin mama tafito yasa tamik'e dagudu tayi waje gun sauran tana dariya.
  
Agurguje mama tasauyawa faruk unifoam dan sun makara yanata Allah Allah yafita yaci k'aniyarta,mama tace
 
"Karka ta6ata faruk,saurin hannu na jawo raini, barta zata dawo tagamu dani, anfison babba yadinga hak'uri kaji?!
 
"Toh mama!"

*****

12:30 sadeeq yaje d'auko twins kasancewar suna Riga saura'n tashi.Yauma kamar kullum tundaga bakin gate yake hango yara sun taru suna kallo, ko ba'a fad'a masaba yasan miemie ce ke dambe.
 
Yana kutsa kai kuwa yaganta taci d'amara da d'an guntun higabinta malu d'inta ya bayyana yara sai dariya suke mata,ammar na a gefe ta tula masa jakarta da lunch box nata.
 
Wani teacher ne ke k'ok'arin rabasu miemie na tirjewa,duk tayiwa yaron dukan tsiya, cikin zafin nama sadeeq ya janyeta tareda d'agata sama
ya turata mota tareda kullewa.
 
Dawowa yayi yana baiwa teachern hak'uri, Dan kullum da kalan fad'an dayake tararwa. Abunda yasa ba'a d'ukar mataki yawancin yaranne ke tsokanarta itakuwa ta musu dukan tsiya. Hannun ammar ya kama suka shige mota.
   
Haka rayuwa ta kasance musu kullum masifa da rigimar miemie k'aruwa take, bata tsoron kowa bata shakkar kowa Dukda tsawatarwa da mama ke mata, idan tayi wani abun wani namiji, abunda miemie keyi sauran basayi, komanta da k'arfe takeyinsa ga shegen wasan banza da b'arna,komanta na rashin hankali takeyi.

*****
   Time passes on, miemie da ammar sunkai 10 years suna jss1,abubuwa dayawa sun faru wanda aciki harda bunk'asan arzik'in baba, sadeeq yagama degree nasa na architecture a ABU,hydar na 200L Quantity Survey a ATBU, sai khaleel dake Ss3 faruk na Ss1.
  
A halayen miemie babu abunda ya sauya, tadai rage fad'a da yayunta sai ammar marainin wayonta shid'inma yanzu ba barinta yakeyiba saidai su daka juna, kwata kwata bata Abu kamar mace, komai irinta maza takeyi,daga yanayin shigarta Dan bata shiri da manyan kaya, wando shine abun sawanta, mama tayi fad'an, tayi dukan, tayi lalla6an amma miemie Sam tak'i koda kuwa tasa minti 20 bayayi ajikinta zata fara murk'ususu ita zafi ya takurata, k'arshe da mama ta matsa mata takai k'ararta gun hajja itako tace abar yarinya ae gaba da kanta zataso kayan mata, kwalliya miemie batayi ko kwalli nan bata sawa, kullum fuskarta fatau, d'an kunne sanda mama takafa mata takunkumi akai tukunna tafara sa manne, tafiyar miemie sai mutum ya kusa kuka, ko namiji albarka, tafiya take kamar zata fire kwata kwata bata Abu a hankali, muryarta kuwa wane an buga ganga, Sam bata iya magana a hankali ba, gashin kantane kurum ke banbanta ta da maza, halayen miemie na mugun damun mama, nikuwa nace mama don't blame her LIFE WITH BOYS!

******
Jeeddah♥

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang