chapter 97

1.3K 124 2
                                    

In dedication to
Miemiebee 👄

******

   Maheer baitaba sanin menene asalin soyayya ba sai akan meelah...sai a sannan yagane ba soyayya yayiwa miemie ba shakuwace tsantsa... Meelah ta fahimtar dashi menene asalin so... Yanzu yanajinta aransa sosae fiyeda yadda yayiwa miemie...tana basa kulawa sosae da tsaftaccaciyar soyayya Wanda ayanzu yakeji bazai iya rayuwa ba itaba... Komai yadawo masa daidai... Ayanzu ya warke garau bayajin ciwon komai... Meelah tazame masa farinciki,abokiyar fadansa, abokiyar shawararsa Sa kuma abokiyar zamansa in Allah yadda.

Har alokacin baida tunanin dawowa Nigeria yariga yayiwa kansa alkawari bazai ta6a dowowa ba sai miemie tayi aure...duk halinda miemie take ciki yasani dukwani labari yanaji daga bakinsu muneer da Abba. Sosae yayi missing kowa musamman hydar da miemie saidai babu yadda ya iya dadin abun duk yanajin komai game dasu.

Muneer yasanar da Abba komai gameda maheer da meelah Wanda ba karamin dadi yajiba...yanzu dansa zai samu farin ciki shima... Tattaki yayi zuwa wurin mahaifin meelah ya sanar dashi halin da ake ciki... Dafarko ya firgita jin maheer said a Abba ya warware masa zare da abawa... Yakuma roki alfarmar karya sanar da kowa tukunna... Yayiwa matarsa bayani ta gamsu itama dama tuncan sunsan irin sonda meelah keyiwa maheer... Sun amince kuma sun bada goyon baya dari bisa dari.

Batare da 6ata lokaci ba baban meelah ya sanar da uncle din meelah nacan a daura musu aure acan... Randa aka sanar da maheer wane ya zuba ruwa a kasa yasha Dan farin ciki Ji yayi he's the happiest man on earth gaba daya.

Duk wasu al'adu na aure anwa meelah hatta lefe da taimakon ita mahaifiyan meelah... Maheer ya sanar da Abba bazai dawo yanzu ba kuma ya gamsu hakan yasa ya tura masa CV dinsa da duk important abubuwansa.

Baisha wahalan neman aeki ba saboda yanada kwali Mai kyau matsayin neurologist... Kuma yayi karatu makaranta Mai kyau. Sun daukeshi tareda bashi muhalli babban gida da motoci biyu....

Andaura aurensu da meelah exactly cikansa wata uku a India...sosae suke zuba soyayya Ga yarda da amince tsakaninsu... Da wani kula da juna da suke.

Duk wani farin ciki maheer yana samu agun meelah... Ita mace ce tamkar ya duba acikin kashe dari da wuya a samu kashe goma irinta... Ga fahimta uwa uba hakura... Ta share duk wani burbudin soyayyar miemie a zuciyarsa saidai har alokacin wannan affection din nanan saboda miemie dabance a gunsa...

Watansu takwas da aure ta haifi kyakkyawan Santa kasancewar ta haifi 7month...saida akasashi a incubator na 3weeks kafun yagama kwari... Abba, baba da maman meelah duka sunzo... Kasancewar tanada Yan uwa anan bata samun matsa at least akwai nagida a kusa.

Yaron yaci sunan Aleeyu Haidar Wanda dama alkawarine tsakaninsa shida amininsa in Allah yabasu yaya maza zasuci sunan juna.

Hydar na shekara biyu abba ya kirasa ya shaida masa anzo neman auren miemie... Jim kadan yayi yana nazari haka kawai yaji baiji dadi aransa ba saidai ya danne ya tambaya no suwayene Dan yana addu'ar Allah sa murad ne Dan yasan koshi kansa baiya yiwa miemie sonda murad ke mata.

Luckily abba yace masa murad ne ba karamin dadi yajiba yabada amincewarsa dari bisa dari tareda musu addu'ar zaman lafiya.

_Nigeria_

Lokacinda mai martaba yazo nemawa murad auren miemie agaban baba da abba...bayan tafiyarsa baba yadubi abba yace.

"Alhaji menace gameda wannan alamari...kaine uba agareta na baka wuka da nama duk hukuncin Daka yanke kan Marian daidai ne."

Abba ya numfashi yace "aganina mufara tambayar ra"ayin yarinya intaji tagani to kar azo ayi abun Dana sani."

"Kayya alhaji... Idan mukabi tata bazatayi aureba... Kaga shekaru gaba suke ba bayaba musamman ita datake ya mace... Shekaru ashirin da hudu harda dauri ace batayi aureba... Bazamu zuba mata idanu tana abunda taga damaba mu zamu yanke hukunci akanta dukda itadin mai biyayyace bazataki abunda muka za6a mata ba..."

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Место, где живут истории. Откройте их для себя