chapter 70

1.5K 141 5
                                        

In dedication to
Miemiebee 👄

_I know it's been a long time, did you count it? Was it weeks already? But am really busy that I can't get to update when I've to.SORRY GUYS…_

******
  Around 4:30pm tafito ratayi da backpack d'inta zuwa treating d'in abba, garden ta nufa dan tasan by that time can zata sameshi, kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin damuwa dan daja jiya zuwa yau ta fad'a, idanunta sunyi luhu luhu fuskarta fayau.
  Dab entrance na garden d'in ta hango   fuskar murad da jalal opposite abba  akan bench while abba nakan wheelchair yana facing nasu,ganin murad agun yasa tai saurin juyawa batare da ya lura da ita ba hankalinsa naga abba,cak sakamakon jin muryar abba ya watsowa su murad tambaya,k'irjintane  yafara matsanaiciyar bugawa tareda juyowa da sauri tana kallon bakin murad don jin amsar da zai bayar.
Jalal ne yafara magana yace.
"Abba na Riga na manta komai saboda nayi imani duk abunda yafaru da bawa muk'addari ne daga Allah, tabbas iyayena sun aekata munanan zunubai kuma ina nema musu yafiya gurin ubangiji, ko kadan abunda yafaru bazaisa na loosing hope akan komai ba, maganar zarah kuwa ina sonta saidai bazanso a tursasa mata ta aureni ba kamar da,saidai ina so abata za6i duk abunda ta yanke I'll be fine with it..."ya k'arishe cikeda k'arfin hali.
Abba yayi murmushi yace
"Allah ya maka albarka jalaluddeen allah ya sa mu dace murad ina sauraronka,kadaiji abunda d'an uwanka ya yanke,me ka yanke gameda aurenka da jaleelah?"
  Sauk'e numfashi yayi tareda runtsa idanu, tabbas idan yace bazai auri jaleelah ba yayi butulci tunda da fari ya amsa,yakuma san tana matuk'ar sonshi,idan yace bazai aureta ba she'll be heartbroken,damuwa zai k'aru mata akan Wanda take ciki yanzu,jaleelah is more like a sister to him yadda bazaiso a cuci zarah ba haka bazaiso jaleelah ta shiga damuwa dalilinsa ba.
"I'll get to married to jaleelah In Sha Allah..."
  Shiru abba yayi nad'an wani lokaci kana ya sauk'e numfashi kana yasa musu albarka duka.
  Miemie dake tsaye jikinta yafara rawa zuciyarta yayi nauyi hadi da bugawa kanta na sarawa har wani dishi dishi take gani she just want to be alone and cry her heart out...da sauri ta juya zata bargun.
  "Doctor..."jin an ambaci sunanta yasata juyowa idanunta yahad'u dana murad da sauri ta kauda nata
Jalal ya k'ira sunanta for the second time yana mata murmushi Daurewa tayi ta faking smile tana kallonsa, kauda kai murad yayi daga kallonta.
"Why're you standing there? K'ariso mana."
Kamar wacca kwai ya fashewa a ciki tafara takawa zuwa inda suke batare da ta had'a Ido da kowaba dan kallo d'aya zakai mata ka gane akwai damuwa tattare da ita.
"Were you about to leave?"Jalal ya sake watso mata tambaya smilingly.
"Y.. Yeah naga kamar kuna kamar magana ne bai dace na katse muku ba."ta bashi amsa tana maida masa murmushin.
  "Yanzu muke shirin tafiya..."
Dan kallon murad tayi hankalinsa na bisa wayarsa ko kallo bata isheshi ba, tasan dama za'a rina.
  Tana kallon sanda ya mik'e yabargun without sparing a glance at her jalal kuwa sai janta da surutu yake dayaga hankalinta bai d'auka ya dubi abba da hankalinsa gaba d'aya ke kan miemie yana nazarinta yai masa sallama ya wuce.
  Maida kallonta tayi ga abba ta sakar masa murmushi
"Sannu da hutawa abba..."
D'aga mata kai kurum yayi, Sam yau babu surutun gaba d'aya komai da sanyi take, juyo da backpack din tayi zata bud'e muryarsa ya dakatar da ita.
"Mariam zauna inada magana dake."
Dakatawa tayi gabanta ya fad'i tana fargabar abunda zai fito daga bakinsa tana addu'ar Allah sa karyamata tambayar da hajjo tai mata d'azu.
  "Meke damunki?"lumshe idanu tayi tareda k'ak'alo murmushi tabashi amsar da ta baiwa hajjo
"Babu komai..."
"Bansanki da k'arya ba mariam,ko akwai abunda akai miki?"
Ta girgiza kai
"Babu komai abba...am just missing my family."tayi k'arya though half was true.
Jinjina kai yayi yasan tabbas tayi kewan gida wata biyu da satukaba wasa bane, tabbas babu wanda keson tabar gidan but yazama wajibi amma yayi imani ba abunda ke damuntq ba kenan saidai bai son tsawwala binkici tana buk'atar lokaci
"Kishirya nan da kwana biyar insha Allah za'a maidaki gida."
Wani 6angare na zuciyarta dad'i yaji while wanin na bak'in ciki,she cant wait to see her family saitaji tad'an sake kad'an.

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now