chapter 46

1.7K 146 5
                                        

In dedication to
Miemiebee👄

******
   Ajiye laptop d'in tayi a k'ofar d'akin ta juya da zummar barin gun taji an bud'e k'ofar,batareda ta juyo ta kallesa ba ta fara tafiya.
"Doctor."ta tsinkayi muryarshi.
Tsayawa tayi batareda ta juyo ba, ahankali takejin takunsa har ya tsaya daidai bayanta rik'eda laptop din daya ta ajiye.
"Am sorry."ya furta a hankali saitin kunnenta.
Da sauri ta juyo da saura k'iris suci gware kallon mamaki take masa, ba ita kadaiba su zarah ma kallon mamaki suke masa.
Bakinta nason furta abu amma ta kasa saboda kafeta da Ido dayayi.
"Thanks."
Kafun tace wani ya mik'a mata wayanta tasa hannu ta amsa kana ya dubi Zarah.
"Take her to your room."
Ta amsa da toh baikuma magana ba ya juya ya bar gun.

******
  Tana tsakiyar bacci taji alamun ana tashinta, a hankali ta bud'e Ido tare da gyara zama cikeda mamaki ta dubi zarah dake kallonta fuskarta ba yabo ba fallasa.
Duba agogo miemie tayi kusan sha biyu da wani Abu.
"Lafiya?"miemie ta tambayeta suspiciously.
"Amm dama ara mun phone d'in ki zakiya I wanna make a call."tafad'a tana kallonta.
Batareda ta kuma magana ba ta d'auka ta mik'a mata, da mamakinta Zarah ta amsa cikin sauri tareda sakar mata murmushin jin dad'i.
"Nagode sosae Doctor."
"Miemie. You can call me miemie."ta fad'a smilingly.
Kai kurum Zarah ta d'aga tana murmushi.
Mamaki yakama miemie dan tunda tazo bata ta6a ganin hak'oran zarah ba sai yau ko meye dalili oho, zata gyara kwanciyar ta zarah tayi saurin rik'o hannun miemie cikin damuwa.
"Amm miemie dan Allah ina neman wata alfarma."
Questionable look miemie ke mata.
"Me kenan?"
"Please karki fad'awa kowa kin ara mun waya musamman agaban su hajjo dan kasheni zatayi dan allah ya zama tsakanin mu kawai."tafad'a cikin sanyin murya.
  Da mamaki miemie ke kallonta.
"Okay I won't tell anyone."tafad'a bayan ta mata murmushi.
"Promise?"ta kuma fad'a cikin yanayin damuwa.
"I promise."
  Godiya tayi wa miemie cikeda farin ciki kafun tamik'e tayi kan couch fuskarta d'auke da fara'a.
Mamaki ya gama cika miemie,da gani zarah data kaita shekaru komeye dalilin dayasa hajjo tahanata rik'e waya oho,ta6e baki kurum tareda gyara kwanciyar ta idanunta kan zarah.
  Kusan minti biyar da bata wayan daga fara'a fuskarta ya fara komawa na damuwa,duk abunda take miemie na kallon ta tana nazarinta.
Can kuma ta sa wayar a kunne kamar Marar gaskiya tafara magana.
"Hello munaya."
Daga can akayi magana ta runtsa Ido cikin damuwa.
"Zarah ce."bayan ta fad'i haka da sauri ta mik'e ta shige closet miemie tabita da kallo, Jan comforter tayi abunda ta ta6e baki,tun tana k'irga mintunan da Zarah ta d'eba har bacci ya fara surarta.
  Cikin baccinta tafara jin kamar shesshekan kuka a kunnenta, a hankali ta juya ta hangi Zarah saman couch da wayar a hannunta tana hawaye.
Da sauri miemie ta mik'e tanufi inda take tareda zama a gefenta worriedly tace.
"Meya faru? Did a relative died?"
Girgiza kai Zarah tayi tareda kauda kai.
"Then why are you crying?"miemie ta kuma tambaya.
"Miemie please let me be, ki koma bacci kawai."Zarah tafad'a in a teary voice.
Miemie ta kalleta kamar ta shareta dan ita ba mutum bace mai yawan shiga sabgar wani,komai yake damuka bata baruanta dakai saidai damuwar ta kasheka dan bazata ta6a tambaya ba amma a yau ganin halin da zarah ke ciki yasa tanason sanin matsalarta kodan ganin wayarta ne yaja komai, d'azu tana murna yanzu kuma murnar ya koma kuka,dafa kafad'ar tayi tace.
"I insist Zarah, I won't let you be until kin sanar wani abunda ke damunki."
Da sauri zarah ta ture hannun miemie daga kafadarta tajuya ta kalleta cikin hasala da idanunta dasuka sauya zuwa ja tace
"It's none of your business miemie ki kyaleni nace babu ruwanki da damuwata."ta juyar da kai gefe.
  Miemie ji tayi kamar ta fisgota ta filleta da Mari, ko Sarah dasuka shak'u bata ta6a d'aga mata murya ba, har yaushe dan tanason sanin halin da take ciki zata na mata Iyaye, runtsa Ido tayi tana nanata innalillahi wa inna ilaihir raji'un saboda 6acin ran ya gushe, bud'e idanu tayi ta kallo zarah data k'ara sautin kukanta, ji tayi tausayin ta ya yaye 6acin ran datake ji har abun ya bata mamaki, wai itace yanzu take damuwa da matsalolin wasu har haka.
Mik'ewa tayi tsaye tana kallon zarah kana tayi murmushi tace.
"Fine. Tunda bazaki fad'a ba I think I'd have to go and call everyone, meyiyuwa idan kika gansu zaki iya fad'a musu abunda ke damunki,kuma zan sanar dasu gaskiyar amsar wayata da kikayi."tanakaiwa nan ta juya da zummar barin d'aki taji zarah ta cafko hannunta cikin sauri.
  "Meye?"miemie ta fad'a bayan ta tamke fuska.
"Dan ya rasulullah ki rufamun asiri..."tafad'a hawaye na zubuwa.
"Not until you tell me everything."miemie ta fad'a bayan ta kafeta da Ido.
  Nodding kai tayi da sauri.
Bayan sun zauna ta dubi miemie with teary eyes.
  "Miemie tun da nake a rayuwa ta never once da mahaifiyata ta zauna taji matsalolina,hajjo uwatace amma bata ta6a
Zama taji damuwata ba saidai ta zartar mun da hukuncin dataga dama kuma babu halin musanta ta, tun ina k'aramata banida ra'ayin kaina sai abunda hajjo ta yankemun kama daga makaranta har zuwa sauran al'amuran rayuwa ta.Banida 'yan uwa mata manya da zasuji matsalolina har subani shawarwari,duk sauran yayyena mazani kuma ba komai bane ake sanar dasu saboda matsalar mace sai mace."
Miemie tayi shiru tana nazarin kalamunta _ba komai bane a ke sanar da namiji saboda matsalar mace sai mace_ ita yah maheer yafi sanin komai game da ita, bata fad'awa mama abunda take gayawa maheer.
"Sauran mazan sabgogin gabansu kawai sukeyi,yah Affan kullum suna tare da abba, yah Fahad na gudanar da al'amuran incomes na gidan nan,yah saleem bamai shiga cikin 'yan uwa bane,yah murad kwata kwata ba a garin nan yake zamaba sai yah safwan ne kurum me lura da duk wani matsololinmu har yake zama damu mu fad'i masa damuwarmu saboda shi kad'ai ke iya tankwasa hajjo,gashi allah ya d'aukeshi lokacin da mukafi buk'atanshi,mai martaba bai samun zama damu saboda al'amuran yau da kullum,gashi shima halin da tsinci kanshi."tafad'a cikin shessheka.
Miemie ta rik'o hannayenta cikeda tausayinta.
"Miemie kud'i ko mulki ba komai bane inhar baka tareda farin ciki, farin ciki shike ja gaba a rayuwar d'an Adam, kuma farincikina duk yana tattare da kamal saboda shiya kawomun haske a lokacin da duniya ta mun bak'i k'irin, natashi cikin rashin kula ta mahaifiya, sannan cikin lokaci k'ank'an allah ya d'auki ran 'yan uwana hud'u sannan abba ya samu nakasa, komai ya juye mana lokaci guda..."tanakaiwa nan ta fashe da kuka.
Kwallane ya taru a idanun miemie a hankali takai hannu tana sharewa miemie hawaye.
"Kamal shine farin cikina a yanzu Wanda yake yayemun duk wata damuwa da nake da ita amma hajjo nason rabani dashi."tana dakata.
"Meyasa?"miemie ta tambaya.
"Son zuciya..."Zarah ta bata amsa bayan ta share hawayenta.
"Son zuciya kuma?"
"Kwarai kuwa, hajjo batason kamal saboda son zuciyarta shiyasa take son had'ani aure da Jamal."
"Waye Jamal?"
"Yayan jaleelah."
"Meye aibun kamal din da hajjo batasonshi."
"Saboda ba d'an gidan kowa bane, maraya ne baida uba mahaifiya kurum gareshi sai k'anwarsa Munaya, abba shi ya d'auki nauyin karatunsa har zuwa jami'a anan ne yasamu scholarship a Cyprus,mun shak'u sosae miemie bazan iya rayuwa babu kamal ba."tafashe da kuka tareda rungume miemie.
Bayanta ta shiga shafawa tanajin hawaye na zuba a kuncinta al'amuran gidan nan na bata tsoro da kuma mamaki, a hankali ta d'agota tarefa share mata hawaye.
"Cry no more Zarah, insha allah komai zai dawo daidai."
Murmushin takaici Zarah tayi tareda girgiza kai.
"Banajin komai zai dawo daidai miemie, hajjo bazata ta6a sauya ra'ayinta ba, kuma duk abunda tace Abba bai mata musu,hajjo ta rabani da karatuna saboda wannan dalilin, ta rabani da duk wata hanyar da zanna had'uwa da kamal gashi abun ya implicating amatullah, saboda ni an hanata zuwa karatu kuma babu yadda muka iya,zancen da nake miki yanzu Munaya tace kamal baidawo gida ba tun komawarsa almost 8months sannan ya disconnecting duk wata hanyar da za'a sameshi, kuma nasan duk hajjo ce."hawaye ya zubo mata.
Miemie ta kalleta cikeda tausayi, take ta tuno gida da 'yan uwanta, duk wani gata da kulawa tasamu gurin iyaye da yayunta,komai take buk'ata tana samu,ga wasu kudi mulki da matsayi baisa sun samu farin cikin daya kamata ba.
"Zarah look at me."
D'agowa tayi ta dubeta.
  "Daina kuka ki dangana lamarin ki ga allah kuma kiyi addu'ar ya zabar miki mafi alkhairi, sannan alk'awari na d'aukar miki saina samar miki farin cikin da kika rasa,it's a promise."
Zarah tayi murmushi.
"That's not possible miemie,zaifi kyau ki share kawai dan zaki jawa kanki matsala ne,nariga nasan rayuwata ta kusa zuwa k'arshe dan da rayuwa cikin wannan yanayin na gwammace mutuwata,hajjo tayi nisan da batajin k'ira komai tasa a gaba bata fasawa saita cimma,miemie kina ganin akwai wani sauran hope bacin hajjo tasan halin yah jamal kuma takeson had'a zuri'a dashi? Ina danganta hakan da tsana coz ban ta6a ganin uwar dakeson kai 'yarta ga halaka ba,atimes ina kokonton anya hajjo ita ta haifemu..."
  Da sauri miemie ta dakatar da ita ta hanyar toshe mata baki.
  "Zarah uwa uwace komai wuya kada ki k'ara fad'an haka saboda babu yadda za'ayi uwa tak'i 'ya'yan data Haifa a cikinta, kuma biyayya ga iyaye wajibine matsawar bata sa6a ma dokar Allah ba, komai tamuku kada kuji haushinta saboda yin haka zaku d'ibe zunubi gun Allah, kinsan ance abunda babba ya tango yaro ko dutsen dala ya hau bazai hangoba, na yarda hajjo na muku ba daidai ba amma kun ta6a tambayarta meyesa take muku haka?"
Zarah ta girgiza kai a hankali.
"Wautar dakukayi kenan tun fari, zarah koda hajjo bata zama daku taji matsololinki yanzu kun girma kuma kunada hakki kan iyayenku meyasa ku bazaku tambayeta meyesa take muku hakaba meyiyuwa akwai wani dalilinta nayin hakan,babu wata uwa dazata so kai 'ya 'yanta ga halaka zarah,kiyi tunani akai."
Shiru tayi tana nazarin kalamun miemie ganin halinda tashiga miemie tad'anyi murmushi takamo hannun zarah.
"Alk'wari na d'auka saina daidaita komai tsakaninku da hajjo."
"Ba Abu bane mai sauki miemie."
"Nasani trust me kedai kawai ki bane had'in kai, insha allahu hajjo zata bayyana muku asalin sonku datakeyi, maganan kamal kuma ki mantashi a yanzu dai gaba kad'an."
  Rungume miemie zarah tayi tana hawaye.
"Nagode sosae miemie."
Murmushi kurum tayi tana share mata hawaye.
"Yanzu damuwa ta k'are kada ki nuna akwai abunda ya faru, kiyi fara'a sosae saboda walwalarki kad'ai zai taimaka mun."
D'aga kai kurum tayi kafun suka kwanta kowa da abunda yake sak'awa a ranshi.

******
   Washegari da suka tashi miemie tayi mamakin ganin walwalar da zarah keyi, bayan sunyi wanka zarah ta Sanya Swiss lace Riga da skirt daya amsheta tayi kyau sosae ta zauna ta sharara kwalliya, duk abunda take miemie na kallonta dama haka zarah take me surutu da fara'a ashe damuwa ce ya sauyata har take ganinta miskiliya wacce batada mutunci.
"Meya faru miemie?"Zarah ta tambaya tana kallon miemie ta mirror.
Murmushi miemie tayi ta matso tad'an jingina jikinta da da jikin madubin.
"So duk wad'annan tarkacen a fuska ake makawa?"miemie ta tambaya tana d'aga concealer.
Da mamaki zarah ke kallonta kafun ta kwashe da dariya.
"Don't tell me... Miemie bakisan concealer ba."
"Ohh sunanshi kenan? Ni ina zansani to tunda ba kwalliyar nakeba, kuma kunada aeki dazaku zauna ku kwashi awanni kuna fente fente."tafad'a tana ta6e baki.
  Dariya sasae zarah tayi kana tace.
"Kinada natural beauty ne miemie a hakan kima kinada kyau shiyasa bakyaso but believe me kwalliya na mugun gyara mutum..."
"To ae kema kinada natural beauty."
"But ae ance in kanada kyau ka k'ara da wanka saikafi had'uwa ko na gwada miki ne."
Miemie ta zaro Ido.
"Wa? Ni rabani bazan iya da wannan...
Kafun ta k'arisa zarah ta mik'e tareda jawota ta zaunar kan stool, miemie zata mik'e tasake maidar da ita.
"Ki nutsu please na gwada miki ki gani, simple make up zan miki."tafad'a ta d'ago foundation.
"A ina zaki sa wannan?"miemie ta zaro idanu.
"Shhh... Banason surutu oya rufe idonki."
A Dole tasa miemie ta nutsu zarah ta mata simple makeup Wanda ya mugun amsarta ku imagining ya miemie data zama.
"bud'e idonki."zarah tace.
Saida miemie ta k'urawa kanta idanu sannan tasan itace,bata ta6a tunanin tanada wannan kyaun ba.
"Kin ganki kuwa?"zarah ta fad'a smilingly.
Murmushi miemie tayi tana ganin sanda zarah ke d'aura mata d'an kwalin daguwar rigar dake jikinta, sosae zarah tayi mamakin gashin miemie ga kyau dukda bayashan gyara sosae.
  Da ta mik'e tsaye sosae tayi mugun kyau kallon kanta tayi a madubi tana murmushi.
  Hoto zarah ta d'auketa a waya suna dariya, bayan zarah ta zauna d'aura d'ankwali suka ji knocking.
Zarah ta mik'e data miemie tayi saurin cewa.
"Zauna barina duba."kana ta nufi k'ofar gaba d'aya har d'an kwalin yafara takurata,batareda ta duba ta peephole ba ta bud'e.

******
Vote, comment. And share

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now