chapter 29

1.7K 122 5
                                    

IN dedication to
Miemiebee

*****
Life matches on,komai yacigaba da lafiya yau dad'i gobe ba dad'i,babu ranar allah da zai wuce batare da Miemie ta tuna mutumin nan ba, wani sa'in har mafarkinsa take daga zaran ta farka tayita masifa ita kad'ai har mama tafara tsoro ko gamo tayi,kowa a gidan yasan da zancen sa,tun suna jinta har abun yafara basu haushi,intana zage zagenta babu mai kulata,maheer yafi kowa jin labarin mafarkin arrogant jerk datakeyi,ta rink'a zuba mita da masifa wane shine yai mata laifin, shikuwa yayita bata hak'uri had'e da bata labaru kozaisa ta manta amma sai abunda ya k'aru, wani sa'in hirarsu karan kaf akan zancen ne, ta rink'a predicting abubuwan dazata masa gaba in Allah yasa sun had'u,inta Ganshi saita mishi abunda har ya mutu bazai mantaba, tun maheer na biye mata har abun ya soma bashi haushi, daga ta fara zuba zancen zaimata sallama ya kashe,inyakuma k'ira still da zancen zata tareshi, tun yana hak'uri har hak'uri yafara gazawa,yakasa mata magana saboda kwata kwata baison 6acin ranta, ganin washi kurum take masa hira cikin lumana tafad'i abubuwan dake ranta,barinta yayi saboda yana ganin hakan ne kawai hanyar dazaisa ta huce ahankali zata manta da komai intana fitar da abunda ke ranta,kullum bq hali a zauna guri d'aya sai ta kawo zancen AJ da kalar tsanar data mishi,,Sosae ta ishe kowa, saida mama ta taka mata burki kafun abun ya lafa tarage zancen.
Haka rayuwa tacigaba da gudana a halayen miemie babu abunda ya ragu saima k'aruwa da yayi,sosae girma ya bayyana a jikinta amma kwata kwata babu kimtsi, jin kanta take tamkar namiji,mama tayi iya k'ok'arinta amma miemie ta sharantar, duka, nasiha duk babu Wanda ke shigarta,gaba d'aya bata abu kamar mace,wasan banza da iface iface bata kunyar yi a gaban kowa,babu abunda tafi tsana irin soyayya da kallon fina finansu abarta da kallon action film da wrestling,wak'ok'in JB kurum take iyaji duk da mafi yawancinsu ma soyayyane,tad'auki abun a shirme da 6ata lokaci, daga zaran taji maganar aure saita lailayo ashar tace auren ma yaci ubansa,mama kullum addu'ar shiriya take mata allah sa nan gaba tasan gaskiya tanakuma gane meyake mata ciwo a matsayinta na 'ya mace,wanda baisantaba yahad'u da ita rana d'aya zaice tanada ciwon hauka, football da hawa doki sune hobbies nata.
Admission nasu yafito duka sun samu a unimaid,ammar yasamu mechanical engineering, miemie tasamu physiotherapy, muneer veterinary medicine Sarah kuma bsc nursing.
Ko kad'an mama bataso tafiyar miemie makaranta a nesa ba saidan tanace ita physiotherapy take so, kasancewar a arewa a uni biu akeyi daga buk sai unimaid,tafiso tazauna kusa da ita yadda zata kula da tarbiyarta dakyau, ya aka k'are a gida balle kuma tayi nesa,sosae tanuna rashin amincewarta,miemie kuwa ta nace itafa sai taje ita physiotherapy take so,baba ma baisoba amma babu yadda ya iya, yaro inba'a barshi ya karanta abunda yakeso ba toh bazaita6a maida hankali akan abunda baisoba,saida hajjah tasa baki kafun suka yadda bisa amincewar zata babu zaman hotel sai gidan Babban yayansu mama wato yah ameenu (cousin ya girma hannun babansu),hankalin mama bai kwanta ba ganin bawani shiri suke da uwargidan sa ba,bazasu ta6a shiryawa da miemie ba ,ta Riga ta k'wace ragamar gidan sai abunda taga dama takeyi shikuwa bayida say,hakan ne yasa zumuncinsu yaja baya dukda d'an uwansu ne amaryarsa ce mutumiyar kirki, 'ya'yansa biyu kuma suka k'anana kasancewar uwargidan bata ta6a haihuwa ba.
Dakyar ta amince bayan gargad'in da nasihan dataiwa miemie sosae ,ganin tare da Sarah zasu tafi tad'anji sanyi, tayaba da halayenta ko ba komai zatasa miemie a d'an wasu hanya.
Saidai mamar Sarah bata amince kan tazauna gidan da miemie zata zaunaba aganinta d'awainiya za'a d'aura musu, gwanda ta zauna a hostel tunda basuda kowa acan,mama ta nuna mata ba komai ae duka yiwa kaine, zaifi dacewa su zauna gu d'aya tunda yanzu an zama d'aya.
Bayan auren sadeeq da abeedah da sati biyu suka fara shirin tafiya makaranta, ita kanta miemie taji wani iri saboda bata ta6a nesa da gida ba, ko ina zataje tare da mama take zuwa.
Washegarin da zasu tafi mama tashigo d'akin rik'e da kaya nik'i nik'i a hannunta.
Miemie na cuccusa kaya cikin akwati batare da nad'i ba.
Tana ganin mama da sauri ta rufe tana washe baki dan tasan abunda tayi.
Mama tadubeta ta girgiza kai kana ta matsar dakayan dake watse kan gadon ta zauna tare da dubanta.
"Maryam!"tak'ira sunanta.
"Na'am maa!"
"Zauna anan!"tanuna mata gefenta.
Zuwa tayi ta zauna kamar mutumiyar arzik'i tana muzurai.
Mama tayi murmushi ganin yadda ta nutsu lokaci guda,she never thought miemie would be this emotional.
"Kinfara kewata ne already?" Mama ta tambaya tana murmushi.
"Chap! Aradun allah maa jinake kamar nayi fuffuke naganni a borno,missing d'inki ae sainaje can nafara banda yanzu tukunna."tafad'a tanacin farce.
Buge hannun mama tayi dasauri ta sauk'e hannun danta Manta shaf a gaban mama take.
"Still dai nasihar zanmiki miemie, please karki bani kunya,maintain your status and act like a goodlady, karki manta da inda kika fito, kiyi abunda yakaiki can, miemie dan allah karki shiga abunda bai shafekiba,can yatara mutane da dama k'abilu daban daban, ina rok'on ki da girman allah karki bamu kunya,allah ya muku albarka ya taimaka."
"Shine magana maaa! Albarka da addu'a shiza kuta hank'adamu dashi, allah yamana albarka, amma maaa bazan miki alk'awarin abu d'ayaba, aradun allah duk Wanda ya shiga hanci na I wont hesitate to face him/her out!"
Mama tabita da kallo speechless.
"Miemie please maintain your language kina jina, haka zakina magana wa lecturer's?" Mama fad'a rai a 6ace.
"Sorry maaa! Na sleeper's of tongue!"(LOL inji Jenifer).
Girgiza kai mama tayi
"Allah ya shirya! I repeat karnaji karnagani ankawo min k'aranki kinyi kaza, kizauna da kowa lafiya musamman gidan da zaki zauna, karki sake kiraina kowa, kiyi abunda yakaiki kina jina."
"Yes maa! Angama."
Kallon da mama ta watsa mata yasa tayi saurin cewa
"Insha allah! Na gyara!"
D'an guntun tsaki mama taja ta jawo akwatin da miemie tagama tukwuikuyawa.
Ciro kayayyakin mama tayi, duka babu atamfa ko d'aya duk gayyan mahaukatan kayan datake yawan sawane, cire rabi tayi ta replacing nasu da kayan datashigo dasu Wanda mafi yawansu dogayen riguna ne, tana kallon miemie na tunzura baki ta shareta.
"Saura naji bakya sawa nida kene!"
Kauda kai tayi tana k'uk'uni duk gayyan zafine da takura.
Gani tayi mama ta d'auko braziers guda bakwai kala kala da sauran underwears.
Waro Ido miemie ta zaro tana kallon su
"Maa meye wannan? Mezanyi da wannan kayan 'yan iskan?"
mama tadubeta cikeda takaicin
"Nima 'yar iskace kenan?"
"Nibance,naku ae manyane wad'ann...
Mama ta katseta dan bazata iya wannan kayan takaicin ba.
"It's high time daya kamata kifara sa brazier, sa half vest ya isa haka sai sa'i da lokaci!"tafad'a tanasawa aciki.
Miemie tabi abun da Ido
"Maa dududu nawa nonon nawa yake! Kallafa kigani."tafad'a tana k'ok'arin d'aga rigar pajamas nata.
"Kika d'agamun riga saina mangareki, banida idanu ne, inbakisaba kanki kikayiwa sai ya fara ta6a k'asa ae!" Mama tafad'a irritatedly
"Maa da hajjah bata sawa meyasa Nata bai ta6a k'asaba."
"Kinci gidanku, gidanku nace stupid,allah sa karki sa saina mugun sa6a miki."
Tanakaiwa nan tatashi tafita, miemie tad'aga sama tana juyawa, ta6e baki tayi ta maida.
Aranar saida ta fad'awa maheer mama tabata brazier,ita wani nonon take dashi, shiru yayi tare da kashe wayan dan kunya ne ya gama rufesa, lallai miemie da sauranta, akwai aeki jaa a gaba.
Washegari yah khaleel ne zai kaisu, da yah deeku ne but antafi honeymoon a Paris saidai sunyi sallama ta waya.
Ammar da muneer tamkar zasuyi kuka miemie kam ko a gyalenta,sai dariya takeyi.
Faruk ya dubeta
"Allah miemie anji kunya, ace mutum zaibar gida na data hudu sai dariya yake yana tsalle."
"To kai meya dameka ya faruk, kaine zaka tafi koni iyee."
"Lil fanta bada ammar kike magana bafa!"khaleel ya tsawatar mata.
Rik'e kunnenta tayi
"Cowie yah paluk d'ina, I'll miss y'all"
Tasa kukan k'arya.
"Maana ummina hajjana, ikko na yah paluk harma da bandirawo I'll miss y'all like sosae sosae.baba bayanan zamu tafi,ni nama fasa zuwa makarantar."
Ummi harda jawota jikinta tana lallashi miemie kuwa sai sussune kai take.
Suna shiga mota ta washe baki.
"Oho dai nayi na k'arya kardai ace banyiba."
D'aga musu hannu sukatita yi harsuka fice daga gidan.
Gidansu Sarah suka nufa suka d'auketa daganan suka d'au hanya, kowani road block aka tsaya sai miemie sunsha hannu da sojoji kuma ta caka musu magana tana k'iransu marok'an zamani tarufe bakinku da mints na naira 20,khaleel yayi fad'an harya gaji amma bata dainaba, awani gu ne aka kusa sasu tsallen kwad'o saidai khaleel ya rank'washeta kafun suka samu sa'ida.
BQ ammar da muneer suka sauk'a, miemie da Sarah aka sauk'esu side d'in anty amarya dan nantace tanaso bazataje gun 'yan 6akin hall ba babu kunya tafad'a agaban uncle usman, shima yasan halin miemie dan haka yasa amaryarsa anty muneerah takaisu side nata aka basu d'aki.
Anty salah itace uwargidan taso baiwa su miemie hard time a gidan but miemie turns out to be more evil than her, duk wani hanya idan tabi ta musguna musu sai k'aik'ayi ya koma kan mashe k'iya, haka tun tanayi harta hak'ura dan miemie tawuce tunaninta, agabanta zata zageta babu abunda take iya cewa, ko abincinta basaci.
Sun gama registration nasu alhamdulillahi kowa yafara attending lectures, randa miemie tafara zuwa tayi fad'a da mutane sunfi a k'irga takusayin danbe dawani yaro, saida Sarah dasu ammar sukasa baki kan abun yalafa.
Ganin gumurzun da miemie tahad'a yasa mutane da dama suka fara shakkarta,sosae bata tolerating iskanci kamata yanzu zata tsigaleka.
Rayuwa tacigaba da tafiya, miemie batakula kuwa, irin D'an banzan dressing datakeyi babu namijin dake kulata, batak'i tasa kaya daga sama har k'asa gambal habaru ba,bata shiri da hijabi sai sallah, k'ananun gyale take ratayawa, yanzu tafara sa brazier ganin sarah na sawa, wataran da bathroom sleepers take zuwa lectures gatada kyawun fuska da jiki amma babu matayi, dama abunda takeson kenan, tana jira wani mai k'aran kwana ya tinkareta da zancen soyayya dan saiya kwana a asibiti, idan taga masoya suna hiransu tadinga Jan tsaki tana zaginsu, sanin halinta yasa ba'a kulata dan ayanzu Rabin makarantar ansan da zamanta, yanzu ka zageta ta zage kuci dambe tamaka dukan tsiya dan wani irin mugun k'arfi allah ya bata, bata iyajin gulma idan tazaun taji Ana gulman wani to zataje ta k'ira Wanda ake gulmanshi takawo gaban magulmatan ta maimaita kuma babu halin musu, munafukai tsoronta sukeji dan tona musu asiri take, ammar da muneer sune abokan yawonta kullum suna tare sai Sarah sa'i da lokaci dan batafiye son hayaniya ba,tafiyar miemie kad'ai abun kallonne.

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now