In dedication to
Miemiebee 👄
******
Ji yayi an rik'e hannu tareda buga masa naushi a baki sanda yayi baya ta shiri, dakyar ya iya d'ago kai ya kalli murad dake tsaye gaban miemie yana masa wani mugun kallo har idanunsa sun sauya kala...sa hannu yayi tareda shafo bakinsa yaga jini, a zuciya ya d'ago ya hayayyak'o masa.
"How dare you!"
"That's what you get when you tried to misbehave with what isn't yours"
"How could you murad?"ya d'aga hannu zai naushesa yayi saurin rik'ewa.
"Don't you even dare make the mistake of hiting me cause billahil azeem you'll pay hundred times worse than this..."ya sakar masa hannu a hankali.
"So you wanna fight me huh?"ya fad'a angrily.
Murad ya d'anyi murmushi ya girgiza kai.
"Not at all Ni ba wawa bane irinka dazan tsaya ina 6ata lokacina wajen fad'a dakai,nayi k'ok'arin baka girmanka a matsayin babba amma inaga yanzu lokaci yayi dan zan gwada maka iyakarka cause ka shigo gonar da ba taka ba."
Kasa magana yayi idanunsa sun koma kamar garwashi sai huci yake kamar zakanya kuma baiyi garajen kai hannunba dan da alama murad zai iya aekata abunda yace daga yanayinsa.
"Aren't you ashame of yourself?"
Sauk'ar da kansa k'asa yayi cikeda 6acin rai.
"Trust me jalal if you come anywhere near her I swear your sister will pay for everything..."
Jalal ya dubi murad yayi murmushin takaici yace.
"You've made a very big mistake murad, I swear you'd regret what you just did to me trust me mu zuba ni da kai..."
Murad yayi smirking yace
"If you try to act anything stupid ba Abu bane mai wuya na iya sauya ra'ayina akan 'yar uwarka and you know she'd be to suffer..."
"And who're you to decide that?"
"this is my life and no one is gonna force me akan abunda banyi niyaba but zaka iyayin duk abunda kaga dama bazan hanaka ba,abun da zan gargad'e ka akai shine stay away from her."
"You'd regret this murad..."yana kaiwa nan ya juya a zuciye ya tafi.
Murad ya bisa da kallo baice komaiba kana yamaida kallonsa ga miemie dake tsaye a tsorace har hawaye yafara cika idonta.a masifance yace
"And you... See what you've got yourself into, I severally warned you it's insecure for you to be walking around everywhere..."
"Would you just stop shouting at me Mr. Emperor..."itama ta fad'a exasperatedly
"Thank goodness I came here on time to stop this...what if that asshole did something bad to you..."ya mayar mata irritatedly
"Why'd you have a problem with that..."
"You must be stupid... Did you think I can ever forgive myself?"
Shiru tayi tana kallonsa da idanunta narai narai da hawaye ya cikasu, juyawa tayi zata wuce yayi sauri rik'o hannunta.
matsowa yayi kusa da ita.
"Are you okay?"ya tambaya concernedly.
"How would I be okay bacin you add to the headache I already have..."hawaye ya zubo mata.
"Atleast Let me go to someone who can comfort me bakai da zakamun masifa ba..."tafad'a tana k'ok'arin kwace hannunta.
Batasan ya akayi ba itadai kawai jinta tayi a cikin kirjinsa ya d'aura hannunsa kanta alamar rarrashi.
Dad'a kwantar da kanta tayi tayi lamo cikin embrace dinta tanajin wani yanayi mai wuyar fassaruwa, a hankali taji duk wani 6acin ran da takeji yafara tafiya hawayen ya tsaya, lumshe Ido tama manta a inda take, sunkai kusan 5mnts a haka a hankali daidai kunnenta yace.
"Am sorry..."kafun ya zameta daga jikinsa.
Kallonta yayi ta sadda kanta k'asa, sa hannu yayi ya d'ago ha6arsa
"Are you alright?"
D'aga kai kurum tayi tareda cewa
"You've to be very careful duckie cause that asshole is up to no good..."
"Thanks..."ta juya abunta tabar gun.
Kallo yabita dashi harta 6acewa ganinsa, shafa kansa yayi ahankali ya lumshe idanunsa yace
" _*Kia*_"
*******
A zuciye ya shiga falon mahaifinsa inda wazeeri da hakimi ke zaune suna tattauna wasu Batu, from no where ya fad'o batareda yayi sallama ba.
"Jalaluddeen da lafiyarka kuwa? Ina ka baro manners dinka"hakimi ya tambaya rai a 6ace.
Jalal yayiwa hakimi wani kallo kana yamaida kallonsa kan mahaifinsa wazeeri yace.
"Baba akwai matsala?"
"Wai yaushe zakayi hankali jalal kafad'o mana babu sallama sannan babu Wanda yasamu darajar gaisuwarka..."cewar wazeeri
"Baba ya kamata ka gane akwai matsala, kaima kasan bazan fad'o maka haka kai tsaye ba."yafad'a cikeda rashin kunya.
"Kai gidanku... Gidanku nace mutumin banza kawai, kai jalal ka kiyaye ni... Ahakan kake tunanin zaka gaji sarauta kana irin wannan halin banzan, shin murad yana abun da kakeyi, meyasa bazaki yi koyi da halayen dan uwanka murad ba, shine k'arami amma yafika hankali da komai..."
Wazeeri ya had'e rai jin hakimi ya yaba murad yadubi d'ansa yace.
"Ayi hakuri hakimi bazai kumaba, kai jalal ka sauya halayenka."
Hakimi ya girgiza kai kurum baice komaiba dan sam wazeeri baya amsar gaskiya indai ta fannin 'ya'yansa ne.
"Meke tafe dakai?"cewar wazeeri
"Baba ya kamata kadau mataki akan murad dan rashin kunyar tasa tafara wuce Gona da iri...wai ni har murad zai d'aga hannu ya nausa bai bacin zagina da yayi ya k'irani wawa,akan wata karuwar banza har yana cewa bazai aura jaleelah ba kuma babu Wanda ya isa yasashi dole ko uban Waye shi."ya k'are yana huci.
A fusace wazeeri ya mik'e.
"Ni murad zai tozarta, har ya isa ya kaucewa umurnina, me akayi akayi ubansa bareni, banda cewa da yayi bazaka auri fateemah ba har abun ya koma kan jaleelah, lokaci yayi dan zan kawo k'arshen tsegaranci da fitsarar sa,nunawa yake yana dadai da kowa babu Wanda ya isa ya bashi Abu yabi, wannan da ni yake bada kai ba jalal kabarni dashi...inadai duk akan wannar yarinyar ce? Komai ya kusa zuwa k'arshi saina nuna masa sahun giwa ya take na rak'umi..."
Duk abunda da suke hakimi baice komaiba har saida wazeeri ya gama banbaminsa kana yace.
"Wazeeri ka tabbata abunda jalal yake fad'a gaskiyane dakake wannan banbamin? Sanin kanka ne ba'a yanke hukunci cikin fushi, na tabbata jalaluddeen shike da laifi dan murad ba dan neman rigima bane, yaron da ko magana bayayi ne zaiyi wannan maganan, kowa zaiyi shaidar murad da rashin maida martani balle har yayi zagi...maganar Mariam kuwa yarinya ce hankali da baseera kuma akan gaskiyar ta take gudanar da aeyukanta,kadai bincika dakyau AbdulMaleek kadaina amfani da zancen yaro wannan bayi bane..."cewar hakimi.
"Baffa zaifi kyau kafita daga cikin maganan nan, tun farko kai kafara had'in nan tun da yace jalal bazai auri fateema ba baka d'auki mataki ba sannan ga batun da jalal yazo dashi yanzu kasan bazai fad'i karyaba, yanzu dai ka nuna kafison 'ya'yan abdulazeez akan 'ya'yana, tunda a matsayinka na babba bazakadau mataki ba ni zan d'auka a hannuna..."
Hakimi yadanyi murmushin kasaita kana yace
"Kayi duk abunda kaga ya dace abdulMaleek bazan hanaka ba amma kasani na zame hannuna acikin maganan nan babu Wanda zan tilastawa abunda baiyi niyaba, kuma duk abunda yaje ya dawo ka kuka da kanka..."yana kaiwa nan ya buga garensa ya fita jalal yabi bayansa da harara.
"Baba na lura da hakimi yanaso ya 6ata mana aeki..."
Wazeeri yayi murmushi
"Kwantar da hankalinka d'ana, ina murad ne matsalar ka, barni dashi kurum ka mance da baffa hakimi."
Jalal yayi murmushi yanaiwa mahaifinsa godiya.
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romance"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...
