In dedication to
Miemiebee 👄Abeg don't chop me off lovelies,am so sorry for abandoning you guys for so many days,but you know am a good girl right? Yeah I really am coz am gonna make up everything, here's an update stay tuned for more I LOVE Y'ALL
******
Wani rafkeken maciji tagani yana k'ok'arin kai mata Sara, da sauri ta sake pillown tareda zunduma uban ihu tana baya, tunda take a rayuwarta bata ta6a ganin maciji a zahiri ba sai yau a d'akinta kuma kan makwancinta, ta ina ya shigo? Allahu aalamu, gaba d'aya ta gama gigicewa takasa motsi idanunta nakan macijin dake shawaginsa kan gadon,ihu take ba gaggautawa sannan ta kasa ta6uka komai.
Alamun bud'e k'ofa taji allah ya taimaka batasa lock ba, sai a sannan wani k'arfi yazo mata, batare da ta dubi Wanda ya shigoba da mugun gudu taje ta k'ank'ameshi gaba d'aya a firgice take sannan takasa daina ihun.
Jitayi ansa hannu an zagaye bayanta tareda mannata sosae an d'aura hannu a kanta.
"Wayyo Allah na maciji...wallahi maciji please take me out."ta fad'a frighteningly jikinta na rawa ta fad'a kank'ameshi.
Shiru bataji mutum yayi motsiba sannan bata fasa ihu ba, da k'arfi tana jijjiga mutumin a rud'e tace
"Take me out of here please... Ma..ci..."
"Calm down Dr...babu abunda zai miki"ta tsinkayi muryar murad daidai saitin kunnenta.
D'ago kai tayi ta kallo cikin sauri idanunsu ya had'u, gaba d'aya tagama firgicewa sai kakkarwa jikinta keyi juyawa tayi takalli inda macijin yake inda ya sauk'o yana a k'asan tiles kusa da inda take kasancewar bai iya tafiya a kan tiles ba sai sulb'ewa yake yana wutsil wutsil sai a sannan taga girmansa yafi yadda take zato, shi kansa murad saida gabansa ya fad'i amma dake,hakan ya dad'a firgitar da ita tajuya tasa kanta cikin k'irjinshi tareda sanya ihu,k'ok'arin janyeta yake su fita amma ta kame jikinta tareda k'ank'ameshi ya kasa motsi, lokaci d'aya muryarta ta d'auke ta sulale zata fad'i sumammiya da sauri murad ya tarota ya mannota da jikinshi, hakan yasa ya sauke ajiyar zuciya dan ihunta ya cika masa kunne yanzu zai iyayin wani abu.
Da hannu yayiwa securities alamar su d'auke macijin, suran miemie yayi kana yayi waje da ita, a bakin k'ofa yatarda zarah da amatullah a duk hankalinsu a tashe, wani kallo ya watsa musu da sauri suka bashi hanya ya wuce.
D'akinsa yanufa da ita idanunsa akan innocent face nata inda gashin kanta ya rufe rabin fuskar,d'an murmushi kadan ya sake yana ayyana abubuwa dayawa aranshi game da ita, akan gadonsa ya ajiyeta tareda tsugunawa gaban gadon yana kallon fuskarta yayi na seconds tareda sa hannu ya gyara mata gashin zuwa bayan kunnenta ya lumshe idanu.
Ganin cup din ruwa yayi gaban idanunshi, ahankali yabi hannu da kallo har ya isa fuskar zarah Wanda hankalinta a tashi ganin halin da miemie ta shiga, nazarinta yayi na d'an dakiku kana ya amsa tareda maida kallonsa ga miemie.
Firgit ta tashi a zabure zata gudu da sauri ya rik'o hannunta hakan ya hanata tashi, k'ok'arin fisgewa take idanunta rufe tana salati, jin an rike mata hannu gagam yasa a hankali tabud'e idanunta ta sauk'e kan murad dake kallonta, har a lokacin jikinta bai bar kakkarwa ba.
Kallonsa take ahankali la66an bakinta ya furta.
"Ma...ci... Ji..."tana nuna k'asa a tsorace.
"Shh... Calm down babu maciji anan, you're safe okay."tafad'a idanunsa a kanta hannunta cikin nasa.
Ahankali ta d'aga kai a tsorace tana waige.
Kallon amatullah yayi dake tsaye gefen zarah, kallon daya mata ta gane abunda yake nufi, da sauri tanufi fridge ta d'auko ruwan sanye tareda zubawa a cup ta mik'a masa ya amsa tareda mik'awa miemie idanunsa akanta har a lokacin yana rik'e da hannunta ganin yadda hannunta ke rawa yasa a hankali yazauna bakin gadon tareda saita bakinta yakai cup d'in, kallonsa take ko kyaftawa babu, lumshe mata idanu yayi kamar maibin umarni takai bakinta bata cireba harsaida ta shanye tanaji wani sanyi na ratsata.
A hankali numfashinta ya fara dawowa dai dai har saida ya dawo normal, kallo tabisu dashi d'aya bayan d'aya tana tuna abunda ya faru, can bakin k'ofa ta hangi jaleelah Wanda babu Wanda yasan da tsuyuwarta a gun sai cika take ta batsewa idanunta kan wani abu, ahankali miemie tabi inda take kallo har idanunta ya sauk'a kan hannunta yadda murad ya rik'e gagam, idanunta tad'ago a kasalance suka had'a Ido saida gabanta ya fad'i.
"Are you okay?"ya tambaya iya yadda data jishi.
D'aga kai kurum tayi a kasalance tafara k'ok'arin zare hannunta daga rik'on daya mata da sauri kamar Wanda aka tsikara ya sakar mata hannunta tareda mik'ewa ya tamke fuska.
Kallon su zarah yayi da sukayi cirko cirko suna kallon ikon allah ya zura hannu a aljihu tareda dubansu.
"She's still frightened ku kula da ita, you shouldn't let her go anywhere I'll be right back."ya fad'a batareda ya jira amsarsu ba ya nufi k'ofa, ko kallon jaleelah baiyiba ya ra6a ta gefenta ya wuce.
ManSadi da sauri yabi bayan PMB.
"Yalla6ai fitarda macijin dakamar wuya."
"Kamar ya?"ya tambaya batareda ya tsayaba balle kalleshi.
"Tunda nake banta6a ganin maciji kalar wannan ba,ga girma ga abun tsoro, duk iya sul6in tiles dinnan dakuma yawan mu saida ya samu damar 6oyewa, munkasa kasheshi balle mu fitar."ya fad'a da d'an fargaba.
"Yanzu da dabara mun bud'e windows ko allah zaisa yafita ta inda ya shigo kan gobe zamu duba dan tabbatar daya fita ko yananan,gadai phone dinta."cewar ManSadi tareda mik'a masa.
Da mamakinsa murad yayi d'an murmushi tareda tsayawa ya dubeshi kana yasa hannu ya amsa.
"Bazai fitaba sai anfitar dashi kamar yadda aka kawoshi."cewar murad
Da mamaki ManSadi ke kallonsa.
"Kamar ya yalla6ai."
Murad ya dubeshi.
"A times I used to wonder wani irin kwakwalwa gareka sadisu,so you easily believe that abunda ya faru was real?"ya bashi questionable look.
Shiru sadi yayi yana nazari kafun muryar murad ya katsesa.
"Sadisu kata6a ganin inda maciji yayi tafiya comfortably kasan tiles?"
Yayi saurin girgiza kai cikeda mamaki.
"A'ah yalla6ai."
"Good. Sannan duk girman gidannan ya baro down floor ya hauro staircase sannan yarasa d'akin dazai shiga saina visitor kuma kan gadon ta, did that make sense to you?"
Shiru sadi yayi cikeda mamaki daga k'arshe yadubi murad yace.
"A'ah yalla6ai... Amma..."
"It's obvious duk abunda yafaru was all a set up, shiryayye ne."finally murad ya katsesa.
Sadi na tsaye cikeda mamaki, murmushin takaici murad ya sake kana yace.
"You shouldn't be surprise sadisu, wannan ba bak'on al'amari bane a gidan nan."yafad'a cikin sanyin murya idanunsa a lumshe.
"Somebody. Someone is after Dr's life, someone is stalking her saboda abunda ya kawota nan gidan, _duk saboda ni._"yafad'a still idanunsa a rufe.
"And its my duty to protect her."yafad'a bayan ya bud'e idanunsa dasuka sauya launi zuwa ja.
Sadisu ya dubeshi cikeda tausayi, tabbas duk abunda PMB ya fad'a gaskiya ne.
Tafiya yafara sadi nabinsa a baya har zuwa inda computers na CCTV yake.
Ma'aikatan gun suna ganinshi suka mik'e tareda sauk'ar dakai k'asa, hakan yana daya daga cikin abubuwan daya tsana shiyasa suna gaishesa bai tamkaba.
Dakansa ya fara operating har yakai kan hallway na gidan inda zaiga shiga da fitan kowa aganun, maidawa baya yayi zuwa shida na yamma yana ganin shiga da fitan mutane, su da ma'aikata.
Exactly 8:30pm sauk'ar miemie zuwa dinner sanye cikin wando baki da Riga fari a ciki mai dogon hannu sai ta d'aura sleeveless jacket dayakai mata gwuiwa red ta d'aure igiyan tsakiya da bakin gyale a kanta ta sauk'a staircase.
Ko minti biyu batayi da sauk'aba saigashi ta hauro with same outfit rik'eda babban basket mai murfi a hannunta, cikeda mamaki murad ke kallo, he was there lokacin da miemie tashigo dining room sanye da kayan nan ta zauna opposite him his gaze on her, he sat there with her for almost half an hour,tayita surutu da mai marbata tana sashi fara'a, kafun tagama dinner kuma ya rigata haurowa followed by zarah da amatullah.
Then how comes akwaita anan tana haurowa while yasan tana taredasu a dining.
"Damnit!"ya murmuring a hankali babu yadda za'ayi ya zooming.
Gyalen kanta ya kalla Wanda tajanyo yarufe fuska hakan ya k'ara tabbatar masa it wasn't her, replica nata ne, itace Wanda tasa maciji a d'akin Doctor saboda basket din hannunta.
"Who's she?"ya furta a hankali fuskarsa d'auke da mamaki.
Juyawa yayi yadubi sadi da ke tsaye yana kallonsa.
"Ina buk'atar list din Wanda suka shigo gidannan yau ASAP."
"I'll be right back."cewar sadi tareda nufan hanyar fita.
Ko minti biyar baicika ba sai gashi ya dawo d'auke da list d'in.
Dubawa yashiga yi baiga bak'on sunaba, gaba d'aya kansa ya d'aure.
"Summon duk wani security on duty yau a second floor."yafad'a bayan ya ajiye da script na hannunsa.
Bayan sun shigo kusan su goma yadube fuskarsu d'aya bayan d'aynaza ri.
Tambayansu questions yayitayi suna bashi amsa, na k'arshen ne ya dubi wani siririn Security Wanda ya lura tunda ya fara bai tamkaba sai muzurai yake.
Murad ya matso kusa da shi yana kallon shi can yace.
"What's your name?"
"Jameelu sir."yabashi amsa yana zare idanu.
Kallonsa murad yayi na d'an lokaci kana ya dubi sadisu.
"Inason sanin duk wasu details nashi da yadda akayi yazo nan."batareda ya jira amsarsa ba yasakai ya fice zuciyarsa na tafar fasa.
Wayar miemie ya d'ago zai duba Abu sai kuma yafasa, bincike baya cikin tsarin rayuwanshi, yaune Karo na farko a rayuwarshi daya tsawwala bincike,shi mutum ne Wanda rayuwa Sam bata dameshi,yaga bakin ciki kala kala a rayuwarshi amma komai ya dangana a allah yad'auka a matsayin k'addararshi, duk abubuwan dayagani Wanda akayi dan a cutar dashi bai ta6a koda magana balle har yayi bincike amma ayau saboda abunda akayiwa miemie yaji k'arfin gwiwa yak'an mak'iyansa.
Alamar shigowan sak'o ne ya dawo dashi daga tunanin daya fad'a, hotonta da maheer ne fara masa sallama, k'urawa hoton Ido yayi nad'an wani lokaci zuciyarsa na ayyana masa abubuwa, runtsa Ido yayi yana tunani yayine ko ya bari, baita6a bincika abun waniba amma yau zuciyarsa na ayyana masa yayi bincikin daya kamata, komai saboda ita zaiyi.
Bud'e idonsa yayi ya kalli screen din wayar,sabuwar number ce ta turo batareda tunanin komaiba ya bud'e, abunda ya yagani ne ya matuk'ar bashi mamaki dakuma tsoro.
_Hahaha...are you scared already PMB? Nasan a yanzu kana k'ok'arin bincike akan abunda bai gameka ba, karkayi mamaki danasan haka,well kanason cusa kanka cikin matsala,wannan tsakanin mu ne da Doctor mariam,bincike bashine abunda ya dace ba saboda kanaso kadad'a jefa rayuwarta cikin hatsari, amma zan gargad'eka,muddin kanason Doctor ta kasance da rayuwarta saika kasance tare damu, ba shawara ba it's more like threatening, stay tuned dan ko da yaushe zaka iya jin abunda mukeso ka mana#giggles._******
Binsu yayi da kallo suna tsaye cirko cirko amma baiga alamun miemie ba,shigewa yayi cikin d'akin idanunsa yasauk'a kan gado amma bai ganta ba, da sauri ya fito kafun yayi magana zarah tayi saurin cewa.
"Yah murad Allah wallahi I told her not to go."
Take gabansa ya fad'i rai a 6ace Zarah.
"Ina taje?"
Da sauri amatullah ta nuna masa k'ofan d'akin miemie.
D'afe kai yayi da mugun sauri ya nufi d'akin.
Daidai lokacin dana k'ok'arin fitowa cikin fargaba sai d'ari d'ari takeyi.
"What the hell did you think you're doing?"ya tambaya a tsawace bayan ya janyota.
Muzurai miemie tafara bakinta narawa takasa magana.
"I.. I...
"Shut up! So kike ki halaka kanki huh? The snake is no where to be found but still kina risking life naki,your damn phone is with me mekuma kike buk'ata?"yafad'a ransa na tafarfasa.
Zatayi magan ya katseta.
"There's no way da zaki koma d'akin nan so karki ma sake tunanin shiga dan na gama magana."
Kasa magana miemie tayi tsoronsa na dad'a shiga ranta, wani mugun kwarjini yake mata datake kasa mayar masa da magana koda kua tsawa ya mata,to ina zata kwana? D'akinshi? Da sauri ta girgiza kai tareda kawar da tunanin,ba ita kad'ai ba hatta ga su Zarah sun tsorata don ganin mode d'in yayansu basu ta6a ganinsa a wannan halinba.
K'aramar tsuka tareda sakar mata damtse ya ra6a gefen Zarah ya wuce duka suka bishi da kallo.
Runtsa Ido miemie tayi k'irjinta na bugawa, ahankali ta d'ago laptop d'in dake d'ayan hannunta ta kalla kan tabi bayanshi dasauri, batareda ya luraba ya banging k'ofar ya buge mata goshi, da sauri ta dafe gurin dan ba k'aramin buguwa tayiba duk irin daurewa na miemie saida hawayen azaba ya cika mata Ido.
Knocking tafara a k'ofar dukda batada tabbacin zai bud'e,duk abunda suke Zarah da Amatu na tsaye.
Takai minti biyu harta hak'ura tajuya tareda jingina bayanta jikin k'ofar ta lumshe idanu zuciyarta na zafi tana mamkin kanta, ina miemie mai rashin kunya? Ina miemie mai cika baki da masifa? Ina miemie mai saurin hannu da rashin hak'uri? Ina miemie wacce bata barin talk kwana? Duk wannan ta nema ta rasa indai tana tareda PMB, Meyake farua da ita? Ta nemi amsa ta rasa, ta zurfafa cikin tunanin sauyin rayuwar dayazo mataVOTE, SHARE AND COMMENT
ESTÁS LEYENDO
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romance"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...