In dedication to
Miemiebee 👄******
Bud'e k'ofar tayi a lek'a hallway, babu alamar mutum,downstairs tanufa ko zata samu abunda zai d'ebe mata kewa,rik'e take da goran farm fresh da da popcorn a hannunta,da mamaki take kallon wani k'ofa dake gefen kusa da stairs d'in,dan a yadda mermu tace mata mutanen gidan basu cika zuwa gun ba kullum k'ofar a kulle take, haske tagani alamar akwai mutum a ciki sakamakon ganin k'ofar a bud'e.
K'arisawa tayi tareda lek'awa kamar 6arauniya tabi gurin da kallon, makeken bookshelf ne daga sama har k'asa yakewaye d'akin sai gurin zama dake a tsakiya dogo Wanda a k'alla zai d'auki mutane goma,gefe guda kuma desktop computer ne, bataga alamar rai a cikiba sai Macbook data gani a kunne alamar aeki ake a kai, gefensa kuma drawings sheets ne da drawing materials a gefe.
K'arisawa ciki tana kalle kalle tana kai popcorn nata baki
Drawing sheet d'in ta d'aga tare da k'are masa kallo,zane tagani Wanda bata gane na menene ba amma alama ya Nuna na building ne. Kallon Macbook din tayi taga same abunda ke jikin drawing sheet d'in shine a jikin screen na laptop d'in.
Ta6e baki tayi tare da ajiyewa tana mamakin na waye architect a gidan nan,footsteps dataji alamar shigowan mutum yasa tayi saurin 6uya a k'ark'ashin desk.
"Am almost done with the contract,I just need a day to clarify some minor errors."Ta tsinkayi muryar mutumin yana shigowa.
Dad'a cusa kanta tayi tareda rik'e numfashinta sakamakon ganin kyakkyawar farin k'afar mutumi cikin slippers sanye da cikin sweatpants.
"Okay...schedule my meeting with the client to determine the objectives and the requirements for the structure of the project."
Gani tayi k'afar tazo dab da ita da sauri taja baya sakamakon haka tabuga kanta batasan sanda ta Saki k'ara auuch ba.
"No need, I'll prepare the contract documents for the contractors to en..."
Ya tsaya sakamakon jin k'ara dayayi k'asa desk d'in dake gabansa.
"excuse me please." Ya tsaya tare da bin study room d'in da kallo da tabbatar da abunda kunnuwansa sukaji, miemie dake la6e ta rik'e numfashinta tareda toshe bakinta da hannu tana muzurai.
"Ehm...what were you saying?"yafad'a bayan yamaida wayar kunne.
Wani tari ne yazo wa miemie sakamakon toshe hancinta a da tayi.
"Haccccchi!"tayi da Sauri ta toshe bakinta tana zare idanu cikeda tsoro.
"Excuse me! I'll call you back later."yayi saurin kashe wayar tareda tsugunawa k'asa inda yaji k'aran don ganin Wanda yashigo inda babu mahaluk'in dake shigowa bayan shi da 'yan uwansa.
Daidai lokacin miemie ta saici hanya dan guduwa, sai gijibb goshinsu ya had'u, da Sauri duka suka dafe goshin cikeda azabar zafi.
"Emperor."
"You." Suka fad'a a tare
Cizan yatsa tayi tsoro fal a ranta sakamakon had'a Idanu tasukayi, harga allah tana mugun tsoron PMB.
Lumshe idanu yayi ya bud'e zaiyi magana tayi saurin cewa.
"Please before you start yelling what the...what the...at least let me get out of here tukunna."ta fad'a muryarta sark'e da shakkar sa.
Wani mugun kallo ya watsa mata, batare da yayi magana ba ya mik'e tsaye tareda ja baya ya tsaya tareda nad'e hannunsa a k'irji yana kallonta fuskarsa a tamke.
A garin fitowa ta sake gwara kanta tasa d'an k'ara tana mulmulawa, kallonta kurum yake baice komaiba.
Bayan ta mik'e tahau kakkad'e pajamas d'inta.
Ganin alamar zaiyi magana yasa tayi saurin k'ak'alo murmushi tareda cewa
"Excuse me."ta tsugunna tareda d'auko popcorn d'inta da farm fresh dake k'asan desk d'in tareda ajiyewa akai tana kallonshi murmushi d'auke a fuskarta.
"What the heck are you doing here?"ya fad'a fuska a tamke.
Ganin yadda ya had'e rai miemie ta tsorita batasan sadda ta d'auki goran farm fresh d'in ta mik'a daidai saitin fuskarsa tareda cewa.
"Have this please...it might cool your temper."
"What are you doing here?"ya fad'a muryarsa tafi ta d'azu idanunsa suka k'ank'ance alamun babu wasa tattare dashi.
"I... I...I yes yes am here to grab some books, gaba d'aya na gaji da zama haka shiyasa."tayi k'arya tana wak'e hak'ora.
Kallonta ya tsayayi na seconds yana nazarinta.
Itakuwa sai kyaf kyata Ido take cike da shiririta.
"And what were you doing under here."yafad'a yana nuna inda tafito.
Hannunshi tabi da kallo har zuwa inda ya nuna, ta had'iye yawu tana tunanin abun cewa.
"LOL... of course naji tsoro ne saboda footsteps danaji, yadda kake jan slippers nasha monster ne zai shigo that was why I hid under..."tafad'a tana dariya tareda nunagun kamar yadda ya nuna.
Kallonta yake bazaka gane expression na fuskarsa ba Amma yad'an sake fuska.
"Weren't you told that babu Wanda ke shigoa nan bayan members d'in gidan nan?"ya tambaya yana kallonta.
"No yeah no....o ooo bansani ba."tafad'a cikeda I.. Ina
Nufan inda Macbook nasa yayi yaja kujera ya zauna batare da ya dubi inda takeba yace.
"Grab all that you need and get out of here ASAP."yafad'a bayan ya focusing kan abunda yakeyi.
A hankali bayan ta juya tafara kukuni.
"You don't have to chase me out saboda babu mai k'aunar ya zauna kusa da masifaffe irinka..."
"And I also don't need a fool like you here."ya bata amsa.
"Huh?"ta juyo tana kallonsa tana mamakin yadda akayi ya jita.
Batareda yad'ago ba yace.
"Stop gazing at me kiyi abunda zakiyi before I throw you out myself."
Murgud'a baki tayi tareda harararsa a ranta tana mamakin yadda akayi yake mata abunda yaga dama tana kyaleshi.
Juyawa tayi tahau dube duben banza da hofi dan ita bataga abun d'auka agun ba,jawo kujera tayi tareda hawa tana cire littatafai tana mayarwa don bataga abunda yayi kama da itaba, pretending tacigaba dayi batare ta noticing takusa fad'uwa ba.
Duk abunda take yana kallonta ta gefen Ido, Sarai ya gane pretending takeyi gulma kurum ya shigo da ita, da gayya yayi haka don k'ure k'aryarta, lura yayi da yadda takusa fad'uwa, ganin kan aekinsa zata rikito idan har ta fad'o,idanunsa naga system yace.
"Careful Dr"
Daga sama ta dubi inda yake.
"Are you an architect?..."bata Idasa tasa ihu sakamakon loosing balance nata datayi zata fad'i tareda runtsa idanu tana jira ta jita a k'asa.
Bud'e idanunta tayi a hankali sakamakon jin datayi an rik'e waist nata kuma k'afafuwanta basubar kan kujeran ba sannan hannayenta kan kafad'ar mutum,idanunta ne suka sark'e cikin grey eyes nasa dake matuk'ar mata kwarjini da bata tsoro.
Shima kallon charcoal black eye nata yakeyi hannunsa rik'e da d'an k'aramin kunkuminta fuskarsu baifi inchi biyu da juna ba, numfashinsu ya had'e guri d'aya.
Sunkai minti biyu a haka yak'i sakinta itama tak'i gyara tsayuwarta idanunsu na cikin na juna, miemie bata ta6a tsintar kanta a cikin yanayin nan ba, gaba d'aya she's lost a cikin sabuwar duniyan data tsinci kanta.
Kamar Wanda aka tsikara yayi sauri maidata former state nata tareda juyawa yakoma Inda ya tashi fuskarsa nanan yadda yake expressionless kamar bashiba ya cigaba da abunda ke gabansa, miemie tabishi da kallo gaba d'aya jikinta a mace, da Sauri tasa hannu ta zunguri kanta tareda runtsa Ido ta bud'e, a daburce ta sauk'o daga kan kujeran.
"Your time is off kinemi hanyar fitq before I drag you out myself."yafad'a batare da ya dubeta ba.
Kallonsa tayi tareda cewa.
"Ae kamata yayi ka tambaya ko na gama abunda ya kawoni."ta kama konkosonta.
D'ago Ido d'aya yayi ya kalleta cikeda mamaki itama kallonsa takeyi.
"Waya baka damar ta6ani iye..."tafad'a tana kwaikwayon muryarsa hannunta d'aya ya k'ugunta d'aya tana nunasa da yatsa.
Rik'e ha6a yayi yana kallonta bazaka gane yanayin daya shigaba, zuba mata idanu yayi yana kallon bakinta.
"What the...what the heck is wrong with you?"tafad'a still tana kallonsa.
Zata sake magana cikin husky voice nasa yace
"Get out."ya fad'a fuskar babu alamun wasa.
Ganin yanayin daya shiga yana iya bugunta batare da ta dubi abunda takeba idanunta a kansa cikeda tsoro.
"Out."yasake fad'a
Sakamakon haka farm fresh dake a bud'e ta buge batareda ta saniba ya zube kan drawing sheet d'in dake ajiye kan desk d'in.
Da idanu sukabi abunda ya faru, miemie gaba d'aya ta gama tsorita ta toshe bakinta da hannunta idanunta sun firfito, 6acin rai k'arara a fuskar PMB bak'in ciki da takaici duk ya gama lullu6eshi, mik'ewa yayi ya dubeta tamkar zai rufata da duka.
"What the..."
"I'm..."bakinta ne ya tsaya a bud'e sakamakon ture Macbook d'in datayi garin matsowa.
Fad'uwa yayi a k'asa take screen d'in ya dagargaje baka iya ganin kamai sai farin haske da gefe guda, komai ya d'auke.
Idanunta ta maida kan PMB dake kallon system nasa a k'asan tiles.
Yadda ya d'ago ya dubeta ta mugun tsorita saboda idanunsa sun d'anyi ja saboda 6acin rai.
"What the...
"I'm so sorry."tafad'a bakinta na rawa.
Matsota yayi sosae cikin 6acin rai harsaida ta takore da jikin shelf d'in, guduwa zatayi da Sauri shima ya matso tareda sa hannunsa d'aya ya tare gefenta.
Iya tsoro miemie tagama tsorita shikenan yau ta banunta.
"Kinkuwa San abunda kikayi?"yafad'a angrily
Da Sauri ta girgiza kai takuma d'aga kai sama.
Ahankali kamar mai rad'a muryarsa cikeda rauni yana kallon cikin Idonta itama shi take kallo. "You ruin everything Dr, everything."yafad'a a hankali muryarsa na rawa.
"I... I am very sorry I'll fix everything..."
"Just shut your filthy mouth up..."ya daka mata tsawa.
Idanunta sukayi narai narai, a hankali yace
"How? I worked very hard on this project, I didn't get the chance to submit kin lalata komai."
Kallonsa take ya mugun bata tausayi, haushin kanta ya gama lullu6eta.
Tana kallonshi ya d'aga jik'akken drawing sheet d'in sakamakon haka ya yage.
Juyowa yayi ya dubeta cikeda takaici yace.
"Banga amfanin ki a nan gidan nan ba,zaifi kyau ki koma gida kifara consoling psychiatrist coz you're mentally unstable,you're a lunatic."yana kaiwa nan ya d'auki drawing materials nashi tareda iPhone7 nashi yabar gurin bayan ya watsa mata wani mugun kallo.
_A lunatic_ ta maimaita kalmar a hankali,Sam bataji haushinsa ba coz abunda ta mishi a yau ko zagin dayafi haka zaimata,haushin kanta taji sosae, tsuguwa tayi a gurin hawaye d'aya nabin d'aya,itace mahaukaciya.
A hankali ta k'arisa gaban laptop d'in ta d'auka tareda ficewa ta nufi d'aki.*****
Tunani tafara yadda zatayi apple laptop ne gareshi mai mugun tsada tasan bazata iya affording ba dan kwata kwata abunda ke cikin account nata 600,000k ne, konga tashiga tahau dubbubawa yawanci hawa hawane, na 465000k tagani Wanda zata iya siya same color da nashi.
Bayan tagama ta k'ira yah faruk dan shi kadai zai iya taimakonta.
"Hello yah faruk."
"Anty mumu."ya fad'a teasingly.
Dan murmushi tayi kana tace.
"Mama tace zaka koma Turkey Monday."
Mamakinta yaji yadda gaba d'aya yajita wani iri, tsokanarta yayi amma bata tamkaba, wannan any a miemie ce.
"Yup insha allah Istanbul na k'ira... wannan karon mezan kawo miki daga can?"yafad'a yana dariya.
"Noo... Bana buk'atan komai yah faruk,allah dai yakaika ya dawo mana dakai lafiya."
"Ameen ameen... Lafiya kuwa you sound disturbed,akwai abunda ke damunki ne?"tafad'a worriedly
Miemie tad'an goge hawayenta tareda dariyan yak'e.
"Am absolutely fine yah faruk kodai kaji banyi tsokana ba... Ina bitazaizai d'inka Juliet da Mary..."
"Kinci gudanku..."duka suka kwashe da dariya.
"Ina surutun naki ya tafi mumu."
"Bacci nakeji shiyasa..."
Cikeda mamaki zaiyi magana tayi saurin katseta.
"Ina ammah na,d'azu damukayi waya da maa tana bacci."
"Silly girl, ance mini kowa irinki ne dayake yaro yanzu kinsan kuwa k'arfe nawa."tafad'a teasingly
D'aga kai tayi ta kalli agogo goma ta wuce.
"Ohhh... Tana bacci."
"Ohooo Ashe kin sani."duka sukayi dariya
"Yauwa yah faruk I need your help engineer."
Shiru yayi yana jinta.
"MacBook d'ina ya samu matsala, ya fad'i d'azu and the screen got damage kuma akwai important files nawa a ciki,so i bought new one how will I transfer everything to the new laptop."
"Oo miemie careless, yaushe baba yasai mini sabo harkin sake fasawa."
"Haka allah ya tsara yah faruk babu yadda na iya."
"Okay to... Cigaba da carelessness wani irin brand kika siya."
"Apple."tabashi amsa.
"Zaki iya using external hard drive that can backup your data idan kin plugging cikin USB port d'in ammafa sai if you had auto run enabled on your laptop, plug the monitor a jikin old macbook d'in saiki transferring data's naki zuwa Sabon by external storage idan kuma kinada SATA a cikin sabon Macbook d'in saikicire hard drive from the laptop and connect the drive using an external drive connector to the new one and copy everything kingane?"
"Nagane."
"Idan bazaki iyaba you can take the old one to a repair shop."
"Nagane.thanks"
Bayan sungama hira ne ta kwanta bacci cikeda tunani dakuma kunyar abunda tayi, gobe insha allah za'a mata delivering laptop d'in, insha allah she'll make up everything for him._The next day_
Da k'arfe _4:45_ alarm d'in miemie ya fara d'ire, mirginawa tareda sa hannu ta kashe, ahankali ta bud'e idonta bayan ta karanto addu'a,dakyar ta samu ta d'aga kanta tareda Shiga toilet ta d'auro alwala, wani annashuwa takeji saboda tashinta a wannan lokacin.
Nafila ta tayi kana ta gabatar da sallan subh,al-qur'an data gani a d'akin ta d'auka tafara kira'a cikin suratul nisa'i, karatun al-qur'an take fluently tana baiwa kowani harafi hakkinsa, wani farin ciki da annashuwa taji yana shigarta a wannan lokacin,bakin ciki rayuwarta na bawa tayi inda tafi maida hankalinta ga karatun boko batacika karatun littafi mai tsarkiba, ashe dama annashuwa da farinciki na tattare a cikin qur'ani, bata idar ba saida gari yafara haske kana tacire hijabin tareda kwanciya.
K'arfe 8:30am ta farka sakamakon jin knocking datayi, mik'ewa tayi tareda Sanya hularta tanufi k'ofa.ta spyhole ta lek'a tareda bud'ewa.******
Vote, comment. And share
OneLove ❤❤❤

YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romance"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...