In dedication to
Miemiebee 👄
*******
"Aunt mareeya is still alive believe me..."
"What the hell are you talking about duckie..."
"Listen to me emperor... I heard that bayan ankamata da laifi tunkafun a tambayeta dalilin dayasa ta aekata hakimi yanke mata hukuncin kisa right?"
D'aga mata kai yayi alamar eh.
"Ka ta6a ganin inda uba ya kashe 'yarsa komai rashin sonta da yake?"
Ya girgiza kai yana kallonta.
"Uhm... How would a father kill his own daughter,komai abunda d'iyarsa ta aekata bazai ta6a bari a kasheta ba shiyasa yayi saurin yanke wannan hukuncin akanta,ko kunga gawarta lokacin da aka kasheta?"
"Nop...yace babu Wanda zaije jana'izar ta..."
"Exactly...Bazai bari ajeba cause yasan aunt mareeya ba mutua tayi ba, he took her somewhere far from here inda baza'a ta6a saniba..."
Shiru yayi yana kallonta expressionless shi kadai yasan abunda ke ranshi.
"Nayi bancike kuma an tabbatar mun da hakimi babu inda hake yawan zuwa irin adamawa, na tabbatar da hakan ne gurin CS, But ya bani tabbacin cewa tana nan cikin jimeta but baisan tak'amammen inda takeba he would help us find her..."
"And you believed him?"
"Yes I do...he won't do anything to harm me ya riga yabada kai sai yadda mukayi dashi..."
Kallon bakinta da idanunta yake karum.
"We really have to find her saboda ganinta kadai za tabbatar da gaskiya balle idan akaji confession nata..."
"How sure are you zata confessing gaskiya?"finally yayi magana
Shiru tayi dan ita kanta batada tabbaci.
"Ehm?"
"samunta ne abu mai wuya but am sure komai zaizomun da sauki insha allah..."ta bashi amsa.
Sauk'e numfashi yayi kana yace
"Am coming with you..."
"What? But you're...
"No argument... Am coming with you and that's final..."
"Har yanzu baka samu lafiya ba..."
"Whatever..."
Shiru tayi tareda tura baki.
Ya matso kusa da ita yana kallon face nata kana a hankali yace.
"You've done so much for us already, if not because of you I wouldn't be standing here...you risked your life multiple times to save this family Wanda yakamata ace ninayi but bansamu damaba...am ashamed of myself da banyi abunda yakamata ba lokacin daya dace I really am,as you said earlier I wouldn't be able to stop you from whatever you're doing...but atleast let me do this once,don't stop me please..."ya k'arishe pleadingly Wanda hakan ya matukar baiwa miemie mamaki.
"Stop blaming yourself for nothing emperor...allah yagani you've really tried your best but..."
"Please..."
"Okay fine..."ta yarda finally
Harga allah taso tayi itakadai batareda ta involving emperor ba, a halin yanzu it's risky for him to do this but he insisted.
Zatayi magana ya katseta tareda nad'e hannu a kirji.
"From now on I'd be the boss,and you'll only do exactly what I ask you to got it?"
"Yes emperor..."ta fad'a blushigly
"Plan A; we've to disguise ourselves cause babu Wanda zaisan da tafiyarmu."cewar murad
"What?"
"Yes and you'd do exactly what I said."yafad'a autocratically
Girgiza kai miemie tayi tana mamakinsa kamar ba yanzu ya gama sauk'ar mata da muryaba ji yanzu yadda yake nuna mata isa...murmushi kurum tayi tana sauronsa.
******
_*The next day*_
_4:30am_
Goge idanu nayi sosae dan ganin miemie cikin kayan Fulani taci kwalliya d'ige d'ige wane d'aga ruga ta fito ko ina yaji kwalli a fuskarta,kanta kuwa yasha kalaban data tukwuikuya wa kanta ta d'aura mayafi sama d'aya rufe mata fuska, hannunta d'auke da k'ullin kaya alamar matafiyace,k'afarta sanye cikin kwada roba wane mai raka shank,kallon kanta tayi a mirror Karo na uku ta kwashe da dariya sosae tana mamakin sauyawarta lokaci d'aya, maimaita words (fillanci) da murad ya koya mata jiya da daddare dakyar ta iya rik'e wasu nan ma saida sukayi fad'a sannan.
Wayartace ta fara ringing dasauri ta d'ago kamar yadda take tsammani sadi ne.
"Hello..."
"Time to go doctor, you've to be quick and careful cause as for now nayi disconnecting CCTV camera nakuma distracting securities dan kar aga fitarku..."
"Okay I'll be right there..."kana ta kashe ta tura wayar cikin saman zanin data d'aura da kyar kana ta kalli kanta taga komai yayi dariya she can't wait taga yadda emperor zai zama.
Saida ta lelleka hallway taga ba kowa ko ina shiru kana tafita tareda sawa k'ofar key kamar yadda murad yace kafun tasauk'a down floor a hankali kamar 6arauniya, ta back door tabi kamar yadda suka tsara.
D'an nesa ta hango Sadi na d'aga mata hannu tanufi gun.
Tana isa gurin sukayi Ido hud'u da emperor atare sadi da miemie suka kwashe da dariya inda sadi ke dariyarta itakuwa wa murad harda rik'e ciki, shikuwa kunu yasha yana watsa mata sarcastic look.
LOL zanso kuga emperor'n ku cikin kayan bororo harda wannan rawanin nasu dasukeyi rabin fuskarsa a rufe ya rataya sanda kamar meh raka
"At least look at yourself before laughing at others..."ya fad'a annoyingly ganin miemie bata daina daruyarsaba.
Dakyar tadaidata nutsuwarta tana murmushi tace.
"Sorry Mr. Emperor..."
Dan guntun tsaki yaja kana ya dubi sadi yace.
"You shouldn't let anyone know bama gida koda kuwa abba."
"Don't worry nasan abunyi no one will find out..."
"Good shall we?"
Waje sukafita Inda sadi ya ajiye mota batareda an gansu ba.
Motace k'irar Prado bak'a wuluk me tinted glass inda baza'a iya ganin mutanen cikiba.Sadisu ya shiga gidan gaba murad ya zauna ana me zaman banza miemie tashiga baya suka fice daga masarautar gabad'aya...sai alokacin akafara k'iran assalatu saida suka tsaya sukayi sallah wani masallaci sukabi jam'i batareda kowa ya shaidasu ba, allah sarki murad yaji dadin kasancewar cikin talakawansa bayan an idar akayi musabaha da juna,miemie kuwa a gefen motar tayi nata cikin duhuwa.
Bayan sun idar sadisu bai zarce dasu ko inaba sai tashar mota har alokacin gari bai wayeba.
Bayan sun sauk'a murad ya kalli gun dakyau tareda yamutsa fuska tamkar zaiyi amai, itama kanta miemie bata ta6a shiga Tasha ba sai a yau.
Ahankali murad yasa hannu a aljihu yaciro handkerchief tareda rufe hancinsa yana wani yatsina.
Miemie ta dubeshi ta ta6e baki tana kokarin maida dariyarta tace
"Dama tun wuri kaba dan kadan ma ka gani."
Sadisu yadanyi dariya shanu harda sa beard saboda 6adda kama.
"Yalla6ai idan kana haka za'a iya ganoku,gaskiyar doctor ne gara ka saba."
Bai kulasu ba illa cire hanky din dayayi fuskarnan a yatsine yadubi sadi yace.
"You've to leave gari ya kusa fara haske ga mutane na fitowa,we'll communicate later Insha Allah."
"Okay sir... Safe trip Allah ya taimaka."
"Ameen..."suka amsa kafun sadi ya yanufi inda ya parking mota yaja ya tafi.
Tohfa kallon kallon aka fara tsakanin murad da miemie dan babu Wanda yasan ya za'ayi, tsaye suke babu wanda yayi magana har matafiya masu sammako sun fara isowa, nan ne murad ya dubi miemie data sake baki tana kallon halayen yan Tasha.
kauda kai yayi murmushi dauke a fuskarsa ganin kwalbanen da miemie tayi a fuskarta dan bai gani dakyau ba sai yanzu.
"Let's go...remember no more English,speak either Hausa or Fulani and mind you hausar ma ba sosae ba"yace da ita.
"But ban iya sosaeba..."tura baki
"Then you mustn't talk..."
"Huh? Nayita shiru kenan..." "Whatever..."baikuma sauraranta ba yayi gaba.
Kullin kayanta ta gyara rik'ewa tabi bayanshi dasauri.
Bai nufi ko ina ba sai wajen lodin 'yan Adamawa.
Tana kallonsa yadda yake magana da fulatanci ana mayar masa.. Saika rantse da allah bai iya wani baroron jejin ne dagaske dabadan ya rufe fuskarsa sannan ya toshe da wata shegiyar gilashi ba babu abunda zaisa baza'a ganesa ba dan kallo d'aya za'aiwa fatarsa asan yaji Hutu ga haske kamar me,ita kanta miemie babban mayafin dake jikintane ya taimaka ta rufe rabin fuskarta.
Yadda yake fillanci saika rantse bai ta6a sanin kalma d'aya na Hausa ba bare larabci da turanci...sosae miemie ta shagala kallonsa tana mamakin yadda ya iya komai kamar dagaske dan kauyen ne shi, sosae take dariya ciki ciki.
K'arisowa yayi gabanta miemie giggly miemie tace.
"Wow mind blowing...I must say you're a fantastic actor emperor..."
Dan karamin tsaki yaja yace.
"For the first time I feel like slapping the hell out of you...I said you mustn't speak with either language rather than Fulani..."yafad'a irritatedly
"Ohh... Kai me kakeyi yanzu, dan nayi praising naka shine nayi laifi... Besides nifa ban iya wani fulatanciba dan wanda ka koyamun jiyama na manta..."tafad'a tana tura baki tana kankance Ido.
Duk abunda take yana kallon fuskarta yadda take magana,sosae fusar keson sashi dariya amma ya dake sai cewa yayi sarcastically
"Ae in baki manta ba allah saiya tambayeki..."
"Mekake nufi? You wan say my brain no dey function again or what?..."tafad'a exasperatedly
"Whatever...let's go."
"Bazani ba..."ta fad'a kai tsaye tana kauda kai gefe alamar fushi.
"Okay fine! Ke kika sani."yana kaiwa nan yayi gaba ko waiwayowa baiyiba.
Da Ido tabishi _kefa wannan ba yah maheer bane dazai tsaya lalla6aki_ ta raya a ranta ganinfa da gaske yake tafiyar sa zaiyi ya barta.
Da sauri tabi bayanshi, jin takun mutun bayanshi yasa ya juyo saura k'iris suci Karo, ganinta yasashi smirking tareda amsar kayan hannunta.
Bayan sunzo gaban wani mutumi yana kirga kudi(conductor) kamar yadda mutumin dazu yai masa kwatance, d'ago kai yayi yadubesu daga expression na fuskarsa zaka gane yaji mamakin ganinsu komeye dalili oho,murad ne ya k'ak'alo murmushi cikin gurancen hausa with Fulani tone yace
"Cannu da aeki yalla6ai..."
"D'an fillo ina zuwa?"cewar mutumin.
"Yola..."ya bashi amsa
Nuni ya masa da wata Sharon yace
"Ga motar adamawa saura mutane uku dama ta cika saiku zauna a kujerar baya..."
Murad ya kalli kana yad'aga kai sama conductor yace
"Saura kudi..."
"Nawane?"ya tambaya cikin gaurancen Hausa alamar bai iyata sosae ba.
"Dubu d'aya da dari biyu ne kaga ku biyu saika bada dubu biyu da dari hudu..."
Jin haka murad yasa hannu a aljihu sabbin mint na 1k ne ciki,tunani yafara anya bazai fahimci wani Abu ba dan daga yanayin dayake kallonsa kamar bai yarda dashi ba.
Kafun yayi wani tunani sai kallon hannun miemie yayi tana mik'awa conductor'n wasu kud'add'un dubu biyu da dari biyar.
Kallon mamaki yai mata ta lumshe masa Ido tareda girgiza kai alamar kar yace komai.
Daidai lokacin da mutumin ya mik'o mata canji tareda mik'a ma murad wani littafi yace.
"Details dinka zaka rubuta..."
"Meye kenan shi?"murad ya fad'a alamar baisan meyake nufi da details ba.
"Sunanka da sunan matarka sai inda kuka fito da inda yakuje, sai lambar wayarka dan dan uwanka nakusa inkana da..."
Murad da miemie suka kalli juna, wati an dauka su ma'aurata ne,ga wata sabuwa wai subada details nasu.
"Mallam kana 6atamun lokaci..."cewar conductor din yana mika hannu.
Miemie takalli murad ganin yayi shiru
"Ban iya rubutu ba ko zaki taimaka ki rubutamun..."ya fad'a finally yanad'an murmushi.
Tsaki mutumin yaja kana ya wafca a hannunsa.
"Meye sunanka dana matarka..."
Shiru murad yayi yarasa abun cewa miemie tayi wuf tace.
"Sunanta audu nikuma larai..."
Kallota yayi da sauri takashe masa Ido tana murmushi a 6oye.
"Wani unguwa kuke?"
"Daga wuro biriji"cewar miemie allah yataimaka sun ta6a hirar da zarah tana fad'a mata rugar Fulani.
Daganan kuma aka carke dan cewa sukayi basuda waya haka mutumin ya kyalesu dab zasu juya mutumin yace.
"Turaren nan naka da kamshe sosae dagaji da tsada..."yafad'a yana kallonshi
Rasa abun fad'a yayi miemie tayi caraf tace
"Yo idan mutum na ruga ba hali Isiye abu mai shada kenan iyee"tafad'a a rai a 6ace
"Larai..."murad ya kirata tareda Jan hannunta.
"Dalla malama laifin me nayi dan na yaba turaren mijinki, ae bacewa nayi sata yayi ba...karkisa yanzu na miki shegen duka dama irinku ko ina kukaje sai kun nuna halinku"
Miemie ta warce hannunta tace gabansa ta rik'e k'ugu.
"Kutumar uban Wanda yace haka saidai uwarkine 6arauniya badai mujina audu ba k..."da sauri murad ya toshe mata baki da karfi yana janta tana k'ok'arin kwacewa
Ashar musa ta fara rugawa abarshi ya daki larai mutane kowa yafara kallosu
Wani dan tsoho dake zaune gefe kan benci yace.
"Musa raba kanka da shiga sabgar mutanen man basuda dadi fa..."
"Tsoho babu ruwanka... Ko ruguntsumin tsafine kansu ina daidai da shegiyar matar nan..."
Murad yayi saurin cewa
"Do allah kiyi hak'uri ba lafiya yake dashi ba,kinsan masu juna biyu sai a hankalo..."
"Ciki... Wa..."da sauri murad ya tura miemie cikin motar yayi saurin shiga ya zauna gefenta.
"What's your problem duckie, are you out of your mind?"cewar murad dai yadda miemie zataji.
"Bakaga yaso fara ganomu bane, dabanyi hakaba allah za'a zargemu gwara Dana nuna masa halin 'yan kauye."tafad'a tana dan dariya
Girgiza kai kurum yayi tareda d'an Jan k'aramar tsuka dan miemie tafara sa masa ciwon kai.
"Tsayama yaushe na zama matarka harda ciki..."
Bai kulata ba yakauda kai gefe.
"Kuma kana karya rules, ba kace ba turanci ba ku...
"For goodness sake keep shut duckie..."yayi saurin katseta irritatedly
Tsit tayi tana muzurai.
d'aga idon dazaiyi ya hangi mutumin gabansu na kallonau suspiciously kamar yaji abunda sukace.
Murad yayi saurin kallon miemie yace
"Haka kurum zaka tayar da hankali dan baki siyama go (so yake yace goruba but ya manta sunan LOL) so kake hakorinka yayi ciwo..."
Da mamaki miemie ta dubeshi.
"Go..."da sauri ya rik'o hannunta cikin nasa ya matse,hakan yasa tagane tayi shiru tanajin wani Abu na yawo mata a jiki, yana kallon sanda mutumin yajuya.
Maimakon ya sakar mata hannu saima sake rik'ewa da yayi cikin nasa hakan yasa ta dago ta kallesa shima ita yake kallo yadan sakar mata murmushin da ke kashe mata jiki dasauri ta d'auke kanta.
A hankali murad yabi ko ina da kallo dan ba karamin daurewa yake yiba dan ma allah ya taimaka Sharon din da d'an kyau sannan mutane bakwai kurum take d'auka.
"Disgusting..."yace can kasan mok'oshinsa tareda lumshe idanu shi har yanzu yana rik'e da hannun miemie shi kad'ai yasan abunda yakeji.
Ana haka mutumin karshe ya iso yana biyan kudi gun musa conductor.
Murad ya d'aga kai kenan ya kallesa, ganin expression na fuskarsa concernedly miemie tace ahankali daidai jinsa
"What's wrong emperor?"
"That man looks familiar..."yabata amsa tareda damke hannunta cikin nasa.
******
Vote, comment. And share
ESTÁS LEYENDO
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romance"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...
