chapter 51

1.6K 155 12
                                    

In dedication to
Miemiebee 👄

******
  Tafiya take zuwa d'akinta bata ko kallon gabanta, tunani ne fal a zuciyarta tana tuna matakin farko dazatabi dan cimma burinta, dab zata shiga d'akinta mermu na shirin fitowa sukaci gware, kallon mamaki suka shiga yiwa juna, mermu na mamakin dawowar miemie while itakuwa tana mamakin meyakawota d'akin bacin tasan ba kowa.
A tare sukayiwa juna murmushi cikeda mamaki mermu tace.
"Doctor why are you back?"
Kallon yanayinta miemie tayi.
"Why?"
"No I was surprised to see you,I mean ba kintafi ba what made you change your mind?"ta tambaya tanad'an murmushi.
Miemie ta kare mata kana tace.
"Isn't it what you wanted mermu? Naji kurum bazan iya tafiya na barku a yanzuba saina gama abunda ya kawoni."tabata amsa.
"Ohhh... Good to have you back am really happy."ta hugging d'inta.
Bayan sun breaking hug d'in miemie tace.
"I need to rest may I?"
"Oh yes you may..."tafad'a tana dariya.
Duka suka tsaya miemie na kallonta.
"'Wuce mana doctor."cewar mermu.
"I can only pass idan kin bani hanya."tafad'a tana nuna hanyar.
"Ohh am sorry..."tayi saurin matsawa
"Is there anything wrong?"miemie ta tambaya.
"No... Why?"tayi saurin tambaya tana sosa kai.
"Why are you nervous all of a sudden?"ta tambaya tana kallonta.
"Not at all... Am so so happy doctor zamanki cikin gidan nan alkhairi ne, nayi k'ok'arin fahimtar dake d'azu kink'i saurarata Ashe allah ya Riga ya tsara zaki dawo..."tafad'a cikeda farin ciki tayi saurin wucewa.
Miemie tayi murmushi tabita da kallo kana ta shige d'akin.
  Tana shiga d'akin taga komai a kimtse bakamar yadda ta birkita kafun ta tafiba, toilet tafad'a tayi wanka tareda d'auro alwala ta gabatar da sallar magrib bata tashiba har saida tayi isha tareda nafila ta rok'o allah ya shige mata gaba aduk abunda take shirin yi tareda neman kariyarsa, tana ninke darduman sallan ne mermu ta shigo jaye da akwatin ta.
Gaisuwa kamar ko yaushe sukayi kafun ta haye kan gado tareda jawo MacBook dinta tahau danne danne, mermu kuwa mayar mata da kaya closet suna d'an ta6a hira, dab ta gama zata fita Miemie tayi saurin cewa.
"Amm dan allah mermu kinada charger na Nokia nawa ya 6ace kuma inada buk'atar yin Abu da wayan yanzu."
"Inada barina na d'auko miki."
"No bari na biki na amsa karna wahalar dake dan jeka ka dawo ba sauk'i."
Dan Jim mermu tayi kana tace.
"Ba komai zan iya kawo miki besides duk wasu al'muranki hannunta suke..."
"Karki damu ae ni nace muje ko..."tafad'a smilingly tareda sauk'owa ta zura slippers.
Jinjina kai mermu tayi kana tafara gaba, da sauri miemie ta d'aga k'asan pillow ta d'ago wani abu kamar biro (pen) ta cusa aljihun wandonta tabi bayanta da sauri.
A hanya suna d'an hira jifa jifa har suka Ido wani k'ofa da mermu tanuna mata tun zuwanta gidan.
"Kikace wannan k'ofar babu Wanda yasan da zamansa banda PMB da sisters nasa saikuma ke da ManSadi?"
"Kwarai kuwa mu kad'ai mukasan dashi saikuma ke a yanzu, kinga idan ba lura kikayi ba bazaki ta6a sanin akwai k'ofa agun ba. "Tafad'a hankalinta naga hanya.
Babu Wanda ya sake magana har suka isa d'akin mermu.
Kallo miemie tabi d'akin dashi sosae yayi kyau babu abunda babu aciki amma saidai akwai banbanci sosae dana sauran yaran gidan.
"D'akin yayi kyau..."cewar miemie bayan tayi gurin mirror.
"Oh thanks."cewar mermu data juya baya zata zare chargern daga cikin socket.
Bayan ta juya ta mik'awa miemie sukayi sallama tafice zuwa d'akinta.
  Dab tazo shiga murad na shirin fitowa, ko kallon inda yake batayiba while shikuma binta yayi da idanu har tashige d'aki tarufe k'ofan.
Zama tayi tareda jawo system dinta dan k'arisa abunda take.
  Tanacikin hakane taji anyi knocking, fuskarta d'aure tace.
"Come in."batareda ta kalli k'ofarba har aka shigo.
Kusan minti daya mutumin dake k'ofar bai motsaba hakan yasa ta d'aga kai ta kalli k'ofar,zarah ta gani tsaye gaba d'aya jikinta a sanyaye.
Ganin haka yasa miemie mata dan guntun murmushi tace.
"K'ariso mana zarah."
Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta k'ariso kusa da ita tazauna tana kallonta.
"What's wrong?"miemie ta tambaya concernedly.
Kamar marar gaskiya zarah tahau murda yatsu.
"I don't know where to start miemie..."
Kallon rashin fahimta miemie tai mata.
"Wallahi duk abunda na miki bada son raina bane I was forced by yah murad am really sorry."finally ta fad'a tana kallonta.
"He refused to tell us why amma dan allah karkiga bakinshi kila yanada dalili..."
"Shhh... Ya isa zarah."miemie ta katseta.
"Let bygone be bygone ni nariga na manta da komai kema kicire a ranki kamar bai faruba tunda na dawo..."tafad'a tana murmushi.
"Am sorry miemie..."tasake fad'a.
  "I'll smash this mouth of yours idan ya sake ban hak'uri."duka suka sa dariya.
"Worry no more, am back everything would be alright as I promised earlier..."tafad'a smilingly.
  Ahankali ta hugging dinta kana taja baya tace.
"Bansan kindawo ba saida yah murad yace na k'iraki bai ganki a dinning ba."
Shiru miemie tayi tana nazari can tace.
"Eyya... Banajin yunwa you go and have your dinner."tafad'a tareda jawo macbook dinta.
"Why? But..."
"I insist..."
"Kinsan bazan fitaba sai kin taso idan ba hakaba nima bazani."tafada tana tura baki
Hakan yasa miemie dariya.
"Okay you go first I'll join you in a jiffy..."
"You sure?"
"101% sure."sukayi dariya a tare kana zarah tafice.
Miemie tasauk'e ajiyar zuciya tareda gyara kwanciyarta tacigaba da abunda takeyi.

*******
  Zarah ta shigo tareda Jan kujera tazauna murmushi d'auke a fuskarta tace
"Tana zuwa yanzu."
Abba ya jinjina kai murad ko kallonta baiyiba balle ya tamka,hajjo kuwa ko daga kai batayi ba, amatullah da zarah suna magana k'asa k'asa suna murmushi har kusan minti biyar.
"Haven't you told her that jiranta ake?"murad ya tambaya alamun ransa ya soma sosuwa.
"Sosae kuwa yah murad she said she's coming."ta bashi amsa.
"How much longer are we gonna wait for her, amatullah jeki dubota."
Harta tashi hajjo ta kallota.
"Zauna."ba musu ta koma tazauna.
Hajjo tadube murad tace.
"She's not a kid anymore so banga dalilin kiranta Karo na biyu ba."tana kaiwa nan tace zarah ta serving.
Murad ya kalli inda miemie ke zama tareda lumshe idanu.
Bayan angama serving suka faraci banda murad da hankalinsa ke ga wayan hannunsa.
Zarah ta dubeshi.
"Yah murad why are you not eating?."
Duka hankalinsu yadawo kansa, d'ago kansa yayi yadubesu tareda kauda kai yamik'e.
"Bring it to my room."yana kaiwa nan yamik'e tareda ficewa duka suka bishi da kallo.
  ******

  Dariya take sosae rik'eda waya a kunne da alamar waya take.
"Am serious paladin, kasan I won't do anything without telling you."
  "Frankly I didn't believe you wannan lokacin kina k'ok'arin 6oyemun wani Abu..."
"OmiGod... Yah maheer believe am not hiding anything."
"Okay..."
"Don't you trust me anymore?"
"I do..."
"Then believe me babu abunda ke damuna, am perfectly fine."
"I won't believe sai randa nazo na ganki da idona zan tabbatar."
"Okay... Wait kana nufin zakazo?"ta tambaya astonishingly
"Bakyaso nazone?"ya tambaya da zolaya.
"Of course I do..."tafad'a cikeda murna tana dariya.
"When?"
"Don't know but very soon kinsan irin aekin namu..."
"Can't wait really am terribly missing you pladin..."
"I missed you as much princess, akwai wata muhimmiyar magana danake so muyi."
"Really... Am all ears."
"Nope sai randa nazo kinga saina kaiki gidan mummy kathum (sistern ummi) Ki gaisheta kullum saita tambayeki."
Zatayi magana taji ana knocking, sharewa tayi takuma jin wani wani atunaninta zarah ce ta dawo batareda ta nemi d'an kwalinta ba tabada izinin shigowa.
Idanunta nakan screen na system hankalinta naga wayan da take batareda ta dubi Wanda ya shigoba tacigaba da hirarta da maheer tana dariya,ganin bata k'ariso ba tadubi gun.
"Zarah..."bakintane ya tsaya ganin murad rik'e da abinci a hannunsa fuskarnan a tamke.
"Okay pladin... Take Care ILoveYou agaidamun ummina."kana ta kashe tareda jawo hulanta ta Sanya tareda duban inda yake.
Ajiye mata abincin yayi kan side drawer  yajuya ya nufi k'ofa har ya bud'e zai fita yajuyo ya dubeta.
"You shouldn't starve yourself for no reason...eat something maybe yabaki k'arfin  gayamun magana gobe..."yanakaiwa nan ya fice.
Miemie tabi k'ofar da kallo kana tayi murmushi dan maganar dariya yabata, wato baison tazauna da yunwa kuma yanaganin kamar zubar da girmane in yanuna damuwarsa shiyasa yagaya mata bak'ar magana.
Tsintar kanta tayi da jawo abincin tahauci tana murmushi ita kad'ai,bayan tagama tad'auka plates din zuwa kitchen.
Bayan ta ajiye tana dawowa taga kamar shadow na mutum ta wajen glass wall harzata share ta wuce tayi saurin dawowa ganin garden din murad suka nufa, dawowa tayi da baya dan tunawa datayi babu mai zuwa gun saishi.
  Haka kawai taji bata yarda da wadannan mutanen nan ba, rasa abunyi tayi can shawara ta fad'o mata,back door tanufa inda zai sasaka da gun shuke shuken fruits, tsayawa tayi ganin securities biyu tsaye, runtsa Ido tayi ta bud'e tareda nufan gun.
"Excuse me."
Duka suka juya suna kallonta saida ta dan tsorita.
"Mekike buk'ata?"dayan mai katon murya yatambaya.
"Inason guava ne please."
Yadubi na gefensa yai masa alama dakai, har yajuya sai fita tayi saurin cewa.
"Noo... Inaso naje da kaina."
"Why?"
"Ba guava kad'ai nakeso ba harda wani ganye zanyi magani dashi."
"Wani ganye kenan?"
Sun fara bata haushi.
"Why are you treating me like am a prisoner...ni nasan abunda make so kubani hanya."tafad'a cikeda isa.
"No one is allowed to go out from this door da daddare shiyasa muka hanaki."
"But nafadi muku uzurina ko... I won't take long yanzu zan dawo."
"PMB will..."
"Na tambayeshi karku damu."
Daga jin haka suka bata hanya tawuce ta sauk'e ajiyar zuciya tace.
"Yan iska masu kama da zomo."
Suna daina hangota ta sauya hanya zuwa inda taga wadannan mutanen.
Bin gun tayi tana sand'a hartafara jin muryoyin amma bata samu ganin fuskaba ta buya bayan flowers.
"Yarinyarnan tana mugun 6ata mana aeki, we need to get rid of her tun kafun yalla6ai yagano tana cikin gidannan."cewar d'ayan.
"Mugun taurin kai takeda shi tanada kafiya, kawar da ita zai bamu wahala kamar PMB."
"A yanzu anbamu damar kawarda shi kamar yadda mukaiwa sauran 'yan uwansa dan shima ya sauya zai iya jawo mana matsala maimakon ya kawo mana sauki."
That means munafukan a cikin gidan suke kenan.
Jin takun alamun suna yowa ta inda take tayi saurin matsawa baya ta mik'e tareda la6ewa cikin duhuwan ganyayyaki ji tayi taci karo da mutum Wanda ya mugun tsoritata, ta bud'e baki zatayi ihu akayi saurin to she mata baki tareda sake jawota ciki.

*****
Vote, comment. And share

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang